Chapter 73
Chapter 73
d'aukowa ta yi ta mik'a mata ta fizga ta juya za ta fita tace "Lokaci zai zo da za ki gane mahimmancin d'a da kuma zafin haihuwa." Ta na fitowa k'ofar d'akin ta yi karo da Aziza da ta k'i shiga saboda tsoro, saida ta kwance d'an kwalin ta ta d'aura akai ta kalli Aziza da kyau tace "Aziza ba ni ki ka cutar ba, kan ki kika cutar, ba ni ki ka azabtar ba, d'an ki kika azabtar, hak'ik'a na ji ba dad'i a zuciya ta, amma ki sani bai kai wanda d'an d'an uwan ki ya ji ba, wannan yaron ko d'an mak'wabta ne ina tunanin zai iya samun tausayin ku a matsayin ku na 'yan adam kuma mata masu d'aukar ciki da haihuwa, amma kash an rasa wannan tausayin daga gare ku ba dan komai ba sai dan kawai ku na so wai ala dole sai kun cuzguna min, to bari na tuna mi ki wani abu, Bilal d'an ki ne domin kuwa ciki d'aya ku ka fito ke da mahaifin shi, Aziza rayuwa ba ta da tabbas, watak'ila wannan yaron da ki ke nunawa k'iyayya yanzun sai kin fini cin moriyar shi ni da na haife shi, idan ki na ganin kamar zanji zafi saboda kun cuta mi shi, to ki sani fa ku sai kun fini cutuwa, domin wannan yaron d'an uwanku ya na son shi fiye da komai a rayuwar shi, sannan abu d'aya da ku ka manta shine, ko a makaranta ana kiran shine da sunan *Bilal Usman Ali* ba wai *Bilal Khadija*, da yau mahaifin shi zai fad'i ya mutu, to ko shakka babu ke d'in nan Aziza zaki fini iko da shi ta wani b'angaren, da ace yau zanje nemawa Bilal aure a wani gidan, daga cikin tambayar da za'a mana ita ce *ina dangin mahaifin shi*? Domin kuwa kune shak'ik'an shi, kuma wallahi ina tabbatar mi ki ke d'in nan kawai idan na nuna a matsayin k'anwar mahaifin shi zai iya sawa a bamu aure, dan haka ku farka daga baccin da ku ke, duk abin da kukawa Bilal zai koma kan ku ne da d'an uwanku, ke ma kuma mace ce, nan da wani lokaci za ki yi aure kije gidan miji, ba zan mi ki fatan samun matsala a gidan auren ki ba, amma zan so ko na wuni d'aya ne ki fuskanci irin rayuwar da na fuskanta a dalilin ku, kinsan me Aziza? Na fi jin zafin juyawar bayan ki a kai na fiye da sauren 'yan uwan ki, kinsan me ya sa? Saboda ke ba baya kad'ai ki ka juya min ba, har da cin amana da yaudara, Allah ya ganar da ku gaskiya, za ku gane waye ya mallake d'an uwan ku." Da sauri ta juya ta koma kan Bilal da ke kwance k'asa har yanzu, da gudu ta d'auko mayafin ta ta d'auke shi tasa mota suka bar gidan, asibitin da aka kai Haseenah ta kai shi, saida suka ciri tikitin ganin likita kafin suka samu aiki, bawan Allah saida aka saka mi shi k'arin ruwa sannan ya sabu bacci, kan shi na kan k'afafun Khadija ta na shafa kan shi, hawaye ta ke saboda tunanin irin halin da d'an ta ya shiga saboda wata tsinanniya a cewar ta, Habeeb dake ta faman kiran wayar Bilal dan su gaisa ne amma ba'a d'agawa, hakan ya sa ya kira Khadija sai lokacin suka san abin da ke faruwa, kafin ki ce kwabo asibitin ta samu hallarar 'yan biyar da mahaifiyar su, iya abin da ta sani kawai ta fad'a mu su, saida Bilal ya farka a bacci ne ya kora mu su jawabin duk abin da ya faru tun daga zuwan shi gidan har wannan lokacin, kuka Khadija ta yi sai Mama ke bata hak'uri, haka dai dare ya yi ko da ruwan suka k'are aka sallame su suka koma gida. *Bayan fitar* Khadija sosai Aziza taji ba dad'i tare da jin nadama, amma bata gama gane halin da take ciki ba taji ihun Haseenah daga d'aki, sosai Haseenah ke murk'ususu tana kiran cikin da marar ta, waya Aziza ta d'auka ta kira Hajia ta fad'a mata, ana sallah isha'i Hajia ta zo gidan dan ganin lafiya, amma ganin irin azabar da take sha ya sa ta tambayi dalilin abun, Aziza ba ta yi magana ba sai Haseenah ce tace Khadija ce ta yi niyyar kashe ta yau a gidan, saboda kawai tace ta bata makullin mota tace Usman bai yarda ba haka kawai, ran Hajia ne ya b'ace saida Aziza tace " Amma fa likita tace za ta kai Bilal da ba shi da lafiya." Cikin b'acin rai Hajia tace "Daga haka kuma sai tace saita nemi kashe ta, yanzu dubi ta'asar da take shirin yi." Kama Haseenah ta yi suka tashi aka tafi asibiti, adaidaita na aje su suka shiga ciki, Aziza kad'ai ta lura da motar Khadija a k'ofar shiga amma banda su da basa hankalin su, saida akawa Haseenah éco aka duba cikin na ta, a cewar likitan "Cikin ta lafiyar shi k'alau, amma fa a kiyaye dan yanzu haka jijjiga ce ta sa take jin wannan ciwon, ayi hankali sosai in ba haka ba cikin biyu za ayi d'aya, ko dai cikin ya zube ko kuma ya bar mahaifarta ya koma bayan mahaifa, dan haka a kiyaye sosai." Nan aka rubuta mu su magani za su koma gida Aziza tace "Hajia kinga motar aunty Khadija har yanzu su na nan, mu shiga mu ga jikin Bilal mana." A tak'aice Hajia tace "In ke za ki shiga ban hana ki ba, ni ma ai marar lafiyar na kawo." Ba dan ta ji dad'i ba suka wuce gida bayan sun siye maganin a pharmacie, Hajia da kan ta ta fad'awa Usman halin da ake ciki, kuma yanda take magana zai nuna ma ka cikin hushi take, shi ma dai tunzura ya yi har yace "Zan shigo garin gobe, ba zan yarda da wannan iskancin ba dan naga abun nata rashin mutumci ne." "Ai kam dai gwara ka yi ka dawo, dan nima na fara gajiya da wannan al'amarin." Aziza da jikin ta ya yi laushi ce ta kalli Hajia tace "Amma Hajia fa makullin mota kawai ta amsa ta kai yaro asibiti, me ye laifi a ciki?" "Yarinya ce ke Aziza, ba wai makullin kawai ta amsa ba, ta so ace tsotsayi ya gifta cikin jikin ta ya zube, dan haka gwara ya zo ya wa tubkar hanci." Saida su Ashir suka rankosu har gida, canzawa Bilal kaya ta yi sannan ta kwantar da shi akan gadon ta, ita ma shirin baccin ta yi su ka kwanta bayan ta jima tana tofesu da addu'a. *Washe gari da safe* Gidan kamar ana wani sabga, dangin Khadija sun hallara dan ganin jikin Bilal, dangin Haseenah ma da dangin Usman sun hallara dan ganin jikin ta, duk da kowa na b'angaren da ya kawo shi amma ka kan iya jiyo hayaniya ta ko ina, a lokacin ne kuma Usman ya diro garin ba dan ya shirya zuwa ba sai dan amaryar shi na wani hali. *Allah kare k'aramin yak'i.* 17/02/2020 à 21:31 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar*
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117