Chapter 18
Chapter 18
boko da yamma ta kawo Barira gida akan moton ta, layinda ta shiga dan ya sadata da titi ne ya kawota k'ofar gidan, har zata wuce sai kuma tace bara ta tsaya ta shiga, har ta shiga soron sai kuma ta ji ba ta so ta samu wannan mai d'aure fuskar, da k'arfi ta juya dan ta koma wajen moton ta sai kawai wata yarinya k'arama data shigo da gudu su ka ci karo, fad'uwa yarinyar ta yi ta fashe da kuka saboda buguwa da kanta ya yi da bango, yanda ta tsala kukan ne ya sa Khadija yin saurin durk'usawa ta rumgumo yarinyar ta na lallab'a ta, gidan kuma akwai mutane har da Hassana ma ta zo, kuma d'iyar tace aka bige, da sauri su ka fito soron dan gani me ke faruwa, har da Usman wanda zuwan shi kenan daga *zinder* ko d'aki bai shiga ba, lafiya lafiya? Kowa ke tambaya, Khadija kam tsaresu ta yi da ido sai da Usman ya daka mata tsawa yace "Wai ba tambayar ki ake ba? Me ki ka mata?" Tsaye ta mik'e lokacin da Hassana ta d'auke yarinyar daga jikin Khadija, kallon tsohuwar ta yi tace "Dan Allah ku yi hak'uri, wallahi ban lura da ita bane, kuma ta shigo ta na gudu." Hassana ce tace "Ba komai haba, ai yaran kenan, bare ma *Fadila* da bata tafiya sai gudu." Usman ne yace "Baiwar Allah, in dai har za ki ci gaba da saka wannan gilashin, to fa ki sani wallahi kullum ki na cikin karo da mutane ki na ji musu ciwo, me zai hana ki cire shi ki aje ko kuma ki dinga hutawa? Shi fa gilashi ba dan sakawa kullum bane, yawan anfani da shi ya na b'ata ido, wanda su ka san abun ma za ki ga akwai lokacin da kad'ai suke anfani da shi, amma ba kamar ke ba sai kace makauniya kina ta fama da abu kullum a ido, wallahi za ki ragewa kanki kud'i ne idan idonki su ka samu matsala." Khadija da tunda ya fara magana ta kafe shi da ido, sai da ya gama tasa hannu ta cire gilashin tasa hijabinta ta share k'wallan da suka taru a idonta, kallonshi ta yi amma sam ba ta iya ganinshi da kyau, wasu hawayen ne suka sake taho mata, kallonshi tayi tace "Ni ma ba haka kawai na ke sakawa ba, larurar ido gare ni, sai da shi ne na ke iya gani, ku yi hak'uri dan Allah idan na b'ata ran ku, zan wuce ne dama nace bara na biyo mu gaisa, da nasan haka za ta faru da ban biyo ba." Ta na fad'a ta juya ta na ci gaba da share k'walla, ta na sauke hannunta k'asa ashe har ta kai wajen moton ba ta sani ba, sai kuwa ta kai mi shi karo motonta fad'i ita ma ta fad'a mi shi, duk da taji zafi haka ta tashi, da saurin mutanen cikin soron su ka fito dan taimaka mata, banda Usman da ya kasa motsawa sai kallonta ya ke, Mannir zai taimaka ya d'aga mata moton tace mi shi "Ka bar shi kawai nagode." Gilashin ta saka ta d'aga moton ta tayar ta wuce, daga wannan ranar ta yanke ba zata sake zuwa gidan ba ko da hanya ta d'auko ta, yayin da Usman kuma ya sha fad'a sosai wajen malam Ali ya kuma ce sai ya je har gidansu ya bata hak'uri, baiyi musu ba yace zaije, dan ya faranta mu su kamar yanda ya saba, a daren ranar yaje gidan ya kuma aika aka mi shi sallama da ita, da farko kamar ba zata fito ba saboda ba ta yanayin dad'i, sai kuma mama tace taje ta gani watak'ila bak'o ne, fitowa ta yi da doguwar rigar shadda da mayafi, ta na ganinshi ta daskare wuri d'aya har saida ya sauko daga kan moton ya same ta, ita dai kallon shi take yayin da yace "Sannu ko?" Da kai kawai ta amsa tana ci gaba da kallonshi, gyara tsayuwa ya yi yace "Kin yi mamakin gani na ko? Ba abun mamaki bane, na zo ne na baki hak'uri akan abin da ya faru d'azu, bayan dogon tunani da nazari na gane ban kyauta ba, ina afuwar ki dan Allah ki gafarce ni, rashin sani ne da kuma rashin fahimta." Ko ba komai ta ji dad'i da ya bata hak'uri, cikin taushin murya tace "Ba komai wallahi ya wuce ai." D'an sunkuyowa ya yi yace "Kin tabbatar ya wuce?" Kallonshi ta yi da murmushi tace "Na tabbatar." Saida ya sake nuna ta da hannu yace "Kin tabbata ba za ki sake kallo na a matsayin marar kirki ba?" Da murmushin da ya fito da hak'oran ta tace "Na yi alk'awari." "To shikenan nagode sosai da ki ka yafe min." "Ni ma nagode." Kallonshi ta yi tace "Sai anjima." Ba ta jira ta ji me zaice ba ta juya za ta shiga kuma sai ta ji oda a bayan ta, ta na juyowa ta ga yayan ta ne Ashir, kashe motar ya yi ya fito daga cikin, "inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Cewar Usman, dan har zuciyar shi bai so Ashir ya gan shi k'ofar gidan nan ba kuma tare da k'anwar shi, sai ya d'auka akwai wani tsakaninsu ne, matsawa Khadija ta yi kusan shi ta rik'o hannun shi tace "K'afafu na sannu da zuwa." Dariya ya yi yace "Yau ko k'afafun nan na ki sun gashi sosai dan sun sha yawo." "Sai muje nasa aunty *Rahama* ta gasa maka su ai." Ta fad'a ta na jawo shi, zaro ido ya yi yace "Kai, ka kai, ka kai, wa na ke gani kamar Usman." Murmushi kaxai Usman ya yi kafin Ashir ya ba shi hannu su ka yi musabaha da gaisuwar anjima ba'a had'u ba, saida suka gama ya saki hannun Khadija yace "Auta zan shiga ciki, idan kin gama sai ki zo kiga tsarabar ki." Turo baki ta yi ta juya masa baya, dariya ya yi ya aza duka a kafad'ar ta yace "Ayi hak'uri, Nana Khadija baiwar Allah." Juyowa ta yi ta na fara'a tace "Wannan sunan ya fi dad'i, amma wani auta auta kamar k'aramar yarinya." Kallonta ya yi yace "Um! Wato ke kin girma ko? To ya ki ke dani tsoho." Tura shi ta yi ya nufi cikin gidan tace "Dallah ni dai ka shiga ciki." Dariya ya yi ya wuce ya na ma Usman sallama, sai da ya shige ta kalli Usman tace "Ni zan shiga ciki, sai anjima." Shigewa kawai ta yi ta bar shi nan, saida ya ga shigar ta ya hau moton shi ya wuce shi ma, daga shi har ita babu mai jin wani bak'on alamari a game da d'an uwan na shi, tana shiga ciki ta samu yan uwanta su ka baje suna hirarsu kamar yanda su ka saba kullum, Khadija ce ta fara tashi ta je ta kwanta, har za su tashi sauran Ashir ya dakatar da su, bayan ya mu su bayani akan abin da ya gani ne ya d'ora da "Nasan Usman sosai, dan mun yi aji d'aya da shi, har yanzu baiyi aure ba saboda abin da ya sa a gaban shi, ganin shi tare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117