Chapter 88
Chapter 88
fuska sosai fiye da ma farko su na gaisawa, mik'ewa ya yi cike da kunya ya na fad'in "To Hajia ni zan koma, dama ina sauri ne nace dai bara na biyo." Gyara zama ta yi tace "Maman shi ai ta na ciki, ka wuce ku gaisa sai ka wuce ko." Da wutsiyar ido ya d'an saci kallon ta ya na sosa kai, kama hannun shi Bilal ya yi sai cukuikuyeshi ya ke, kallon shi Mama ta yi ta harare shi tace "Kai dallah miye haka malam sai wani cakumar shi ka ke kamar wani wutsiyar shi, dawo nan ka zauna har ya fito." Ta nuna mi shi kusa da ita, mak'ale kafad'a ya yi yace "Wai ke ina ruwan ki, ba Abba na bane, karfa ki ga idon Abba na ki b'ata min rai, sai na ce na fasa dawo da ke d'akin ki." Rufe baki Mama ta yi tace "Ka ji masharranci kuma, to yaushe ka kore ni da har yanzu ba ka dawo dani ba?" Dariya Bilal ya yi yace "Ka ji ko tsohuwar nan, wato so ki ke Abba ya bani hak'uri na dawo da ke, to na k'i d'in sai kinyi sati d'aya babu kud'in cefanai." Usman da ke dariya shi dai cewa ya yi "Ka na manta wani abu yarima, na fad'a ma ka kafin ma Mama ta san da kai mu ta fara haihuwa, shin ka na ganin duk yawan mu za mu iya barin ta da yunwa? Abu ne da ba zai yiwu ba ai." "Ah to fad'a mi shi dai, kuma da ka gan shi nan cika bakin ne kawai, gishiri wannan na dala biyar bai tab'a bayarwa aka siya ba, watak'ila ma ko sabon bebe da zai zo yanzu na yi miji idan na ga ya fika k'ok'arin cefanai." Dariya Bilal ya yi yace "To ai dai sai na sake ki sannan za ki koma gare shi, kuma idan fa aka haifo min mace ya za ki yi?" Shiru kawai Mama ta yi sai murmushi da take ta na kallon shi, gwalo ya mata yace "Yeeeehooo, na rufe mata baki, ai ba'a aure akan aure, kuma nasan ke kishi ya mi ki yawa." Sai lokacin Usman ya juya ya nufi d'akin Khadija, Bilal kuma zaune ya yi kusan Mama ya d'ora kan shi akan k'irjin ta, ture shi ta yi tace "Kai d'aga min nono malam, k'walelen kare da hantar kura fa, tom." Saida ya sa hannu ya tab'a nonon yace "To me zanyi da wannan tsohon nono, abin duk ya yamutse, ga na Mummy ta nan sabo dal a leda." Bushewa su ka yi da dariya dukansu ta janyo shi jikin shi su ka rumgume juna, tabbas kamar yanda ta ke matuk'ar k'aunar Khadija matsayin ta na mace, haka a cikin jikokin ta ma take matuk'ar k'aunar Bilal saboda wayon shi, yaro ne mai shiga rai dan shi ko irin mahaukaciyar k'uruciyar nan baiyi ba, hasalima cikin yara za ka ga shi wasan shi ta dabance, sannan bai cika son hayaniya ba kuma baida yawon surutu, idan kaji bakinshi cacaca to sun had'u ita da shi ne. Tun kafin Usman ya shiga ya ke tunanin abin da suka fad'a na maganar bébé da haihuwa, me su ke nufi? Khadija ciki gare ta kenan? Dama k'ofar a bud'e ta ke dan haka k'arasa tura ta kawai ya yi ya shiga, zaune take akan gado da littafin *hisnul muslum* ta na karantawa, ta na kallon shi ta d'auke kai ta mayar kan littafin tace "Me ya sa ba za ka nemi izini ba kafin ka shigo?" Saida ya k'arasa shigowa har ya zo daf da gadon yace "Saboda da kai da kaya duk mallakar wuya ne." Kallon shi ta yi fuska ba annuri tace "Kan na iya zama na ka amma banda kayan saman shi." Murmushi kawai ya yi yace "Haka ake tarban bak'o a garin ku?" "Duk bak'on zai iya shiga kowane lungu da sak'o na gida ba bak'o bane, musamman ma irin ka da ba sa neman izini kafin su shiga, kuma ina da tabbaci ba waje na ka zo ba, dan haka me zai sa na damu kai na?" Kafe ta ya yo da ido ya na kallo kamar ya na karatun wani abu, jin shirun ya yi yawa ne ya sa tace "Bilal fa ya na farfajiyar gida." "Na gan shi ai." Kallon shi ta yi tace "Hajia kuma ai ta na falo." Saida ya zura hannayen shi aljihu yace "Ita ma mun gaisa." Mayar da hankalin ta tayi kan littafin ta tace "Da kyau." Ci gaba ta yi da karatun ta shi kuma yace "Ya beby ya ke?" Cak ta tsaya amma ba ta kalle shi ba sai rarraba ido da ta fara yi, tambayar da take wa kan ta ita ce ya aka yi ya sani? Dan ba ta san Mama ta je ta fad'awa su Hajia ba, rasa abin fad'a ya sa Usman zaune kusan ta ya na k'are mata kallo yace "Kenan da gaske ne? To amma me ya sa ba'a fad'a min ba?" Kallon shi ta yi cikin dagiya tace "Waya fad'a ma ka ina da ciki? Ko kuma ka na so ka b'ata min rai ne?" "Ban gane ba? Bayan da kunnuwa na naji Mama ta na fad'a, gashi kuma na tambaye ki amma duk alamu sun nuna gaskiya ne." Murmushi ta yi tace "Ka taya ni addu'a Allah ya bani nawa nima, amma yanzu ai amaryar ka ce ke da shi, duk da ka ce ina mata bak'in ciki." Kafe ta ya yi da ido yace "Ki rantse da Allah ba kya da ciki." Cikin mamaki tace "Rantsuwa kuma? To miye na rantsuwar? Abin da na ke nema ido bud'e zan samu kuma na kasa fad'a ma ka." "Ba ki ke nema ba dai, mu ke nema, kar ki manta da haka, har yanzu ina son sake ganin abin da zai fito daga tsatsonki." Kallon shi kawai ta yi shi kuma ya mik'e yace "Kin dai tabbatar ba ki da komai?" "Eh." Ta fad'a, sake jajjadawa ya yi "Kin tabbatar babu?" Cikin k'osawa tace "To! Na ce babu, babu, idan ba ka yarda ba ka je ka tambayi su Maman ka ji, su a zatonsu ne ciki gare ni saboda rashin lafiyar da na yi, ni kuma wahala ce ta sani wannan rashin lafiyar na dukan da ka min." Murmushin gefen labb'a kawai ya yi ya sunkuyo da kan shi kusan fuskar ta yace "Kin tabbatar dai ba kya tare da ciki na ko?" K'asa ta sauke idon ta hakan ya sa yace "Sai kin kalli ido na." Kallon shi kam ta yi tace "Eh, babu komai." Tsaye ya mik'e yace "Shikenan, amma ki tabbatar duk ranar da na ji labari yasha bambam wallahi sai kin gane kurenki." Saida ta sake kallon idon shi tace "Na yarda." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan, saida safe." Juyawa ya yi ya fice daga d'akin ta bishi da kallo, saida ta tabbatar ya bar gidan ta fito ta samu Mama ta tambaye ta, ba ta b'oye mata komai ba hakan ya sa tace dan Allah kar su sake ya san ta na da ciki, dalili Mama ta tambaya saita nuna mata kawai ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117