Chapter 4
Chapter 4
Bayan mahaifin Usman ya zo mahaifiyar shi ta fad'a mi shi komai, kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Masha Allah, wannan ai abun farin ciki ne, dan girma ne zai k'aru, fatan alkairi kawai za mu ma sa, zuwa safe kuma idan ya zo sai muji yanda za ayi." *Allah ka bani lafiya mai anfani.* 27/12/2019 Γ 20:31 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *3* Kasancewar maza ne su ka shiga al'amarin, sai akayi komai cikin sauk'i da sauri aka gama, kuma cikin k'ank'anin lokaci aka saka *wata biyu* mai zuwa, dan haka kowane b'angare ya fara shirye shiryen da su ka dace da shi a bikin, amma b'angaren Khadija hankalin ta kwance ya ke, dan dama tun farko mace ce mai kama jikin ta da tsare gida, hakan ne ya sa ba ta buk'atar d'aga hankalin ta wajen gyaran jikin ta ko wata kwaskwarima, kayan d'aki ne kawai ta ke buk'atar canzawa, shi ma kuma a nutse ta ke so ta yi komai, tunda kud'i ba su ne matsalar ba. Wajen amarya ma yan uwan ta ne ke tsaye kan kula da gyaran jikin ta, dan mahaifiyar ta dattijuwa ce kuma babu ruwan ta, ita ma kuma ba zaune ta ke ba ta na d'an k'ok'arin ta wajen ganin ta gyara kan ta da kan ta. *Duk* abin da aka sa ka ma rana to k'ararre ne, sai gashi kamar k'yabtawar ido har an ciye *wata d'aya* da sati d'aya, hakan ne ya sa biki ya rage saura sati uku, kuma har yanzu uwar gida ba ta tab'a ganin amarya ba, amarya kuma ta ga uwar gida amma a hoto ba'a zahiri ba, shirye shirye ya kankama sosai, sai dai kuma Khadija ta d'an fuskanci wani k'alubale a wajen dangin mijin ta, kasantuwar ta mace mai fara'a da kyauta da kirki ya sa yan uwan ta da yan uwan Usman su ke son yawan kawo mata ziyara, amma tun da aka saka ranar auren shi har yanzu ba ta ga k'eyar kowa ba, ba ma kamar k'anwar shi *Aziza* wacce har kwana ta ke a gidan. Yau dai sunyi sallama da Usman za ta je wajen bikin k'awar ta *Halisa* da ta haihu, kuma tace za ta fara biyawa ta gidan su ta gaishe da mama, tsaf ta shirya cikin kayan da ta fi son sakawa, leshi (less) ne aka gwangwaza mata d'inki mai kyau riga da siket, sai takalmanta ma su tsini da mayafin da ya dace da kayan, ta na shigar motar ta ba ta zame ko ina ba sai gidan su Usman, cikin sa'a sai ta samu k'anwar Usman d'in da ke bi mi shi wacce da Usman ya had'awa Khadija kayan fad'ar kishiyar ta ya kai mata yace ta kai wa Khadija, ba dan ba zai iya ba sai dan ya na so ya bata mamaki, ita kuma ganin kayan sunyi yawa ya sa ta taho da su nan d'in dan ta nunawa mahaifiyar su. Da isar Khadija a soro taja birki ta tsaya saboda jin muryar aunty *Hassana* na fad'in "To domin Allah Hajia yanzu wannan kayan da mata ne za ki ce ba su yi yawa ba? Ko fa lefen amarya da aka kai wallahi bai kai wannan kayan ba, haba dai, kayan fad'ar kishiya har akwati goma, kuma kowace cike da kaya, gaskiya ni ba zan kai su haka ba." Tshohuwar ce tace "To ya za ki yi da su? Ragewa za ki yi? Ko kuma me za ki yi?" Ai kuwa sai muryar Aziza a kunnen Khadija ta na fad'in "To dama ina zai had'a lefen ta dana amarya, kin manta ta gabar goshin ce? Ai ina tabbatar mi ki a yanda na san yah Usee (sunan da su ke kiran shi da shi kenan) ya na tsoron matar nan, wallahi da za ta ce ya fasa auren nan, to ko musu babu zai fasa shi." Tsaki tsohuwar ta yi tace "Kullum ina fad'a mu ku ku dinga kyautatawa mutum zato, abin da ba ku da hujja da yak'ini a kan shi, amma ku na hukunta yarinya da shi, wannan fa bai dace ba." Hassana ce tace "Hajia ba kya son laifin Khadija ne kawai, amma duk wanda ya san rayuwar su wallahi ya san da magana a k'asa." Aziza ce tace "Ku ai duk labari ne ku ke ji, ni da na mayar da gidan fa kamar gidan mu, kar ki so ki ga wani abun haushin idan ya na yi wallahi, su kad'ai a cikin gida sai shegen yaron nan da ba komai ya ke ci ba sai abin da ya ga d..." Ba ta k'arasa ba tsohuwar nan ta kwashe ta da mari, hararan ta ta yi tace "Dan rashin mutumci d'an yayan na ki za ki sheganta? Kuma a gaba na, dama gulma da d'aukar rahoto ne ke kai ki gidan na su? To kinyi na k'arshe, mutuniyar banza kawai." Tashi tsaye ta kalli Hassana tace "Ke kuma ki tabbatar kin kai wannan kayan in da aka aike ki da su." shigewa ta yi d'aki ta barsu nan, Khadija kam k'walla ne su ka cika idon ta, juyawa kawai ta yi ta fita ta d'auki hanyar ta zuwa in da za ta je, Hassana kuma tattara kayan ta yi ta rufe akwatinan kafin ta samu yaro aka mayar da su a motar da ta kawo su, Aziza kuma ta ci gaba da kumburar baki. Ko da Hassana ta je gidan babu kowa, dan haka ma ta kira Usman d'in dan ta fad'a mi shi, a cewar zai aiko da yaro da makullin falon Khadija ta bud'e ta saka kayan, bayan nan kuma sai da ya mata fad'a wai ba ta kawo a kan lokaci ba har ta fita, hakan ya sake tunzurata ita ma, dan ganin ta ke kawai ba ya k'aunar b'acin ran matar shi bai kuma damu da b'acin ran su ba, haka ta jira yaron shi ya zo ya kawo mata aka bud'e aka jera akwati nan kafin ta bar gidan. β©β©β©β©β©β© *Yamma* ta yi sosai *Hassenah* ta kammala girkin ta ta na jiran isowar yayar ta, kallon maman ta ta yi cikin b'acin rai tace "Wallahi aunty *Mariya* ta cika b'ata lokaci, sai da na fad'a mata akwai in da zanje ta yi sauri fa." Dattijuwar da ke cike da kamala da sanyin jiki wanda da alama hallitar ta ce haka tace "Watak'ila wani abun ne mai mahimmanci ya tsayar da ita, amma ki k'ara hak'uri." Tsaki Haseenah taja cikin b'acin rai, amma ba ta dire tsakin har k'arshe ba Mariya ta shigo a hargitse da sallama, mahaifiyar kad'ai ta amsa sai kafeta da ido da Haseenah ta yi, ita kam goyon da ke bayan ta ta kwance ta aje kan tabarmar da ke shinfid'e ta na gaishe da maman na su, cikin rashin kunya Haseenah tace "Dan Allah aunty
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117