Skip to content

Chapter 98

Chapter 98

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

sosai akan lamarin na shi, dan har yanzu ba su kwana d'aki d'aya ba, gari na wayewa kuma zai buga sammako yaje gida ya na lallab'ar malam ya je ya dawo da Khadija, sam ba ya da lokacin wata Haseenah yanzun, abinci ma idan ta dafa sai dai ta ci ita kad'ai amma ban da shi, ba ya son zuwa gidan saboda ba ya son ganin Haseenah da idon shi, ya na iya k'ok'arin shi sosai wajen b'oye k'iyayyar da yake mata, ya rasa dalilin da ya sa ya ke sake jin tsanar ta a kullum idan ya ganta, ba ya son jin muryar ta ko ganin giftawarta a gidan, duk da ba ya da kokwanto akan cikin da ke jikin ta cewa na shi ne amma dai ba ya jin ya na k'aunar abin da ke cikin ta kamar yanda ya ke k'aunar wanda ke cikin Khadija, a haka har aka kwashe *sati biyu* babu abin da ya sauya. A sati biyun nan ne Usman ya yi tattaki har k'auyen su Baba Garba mai gadi ya je ya bashi hak'uri akan abin da ya farusannan ya nemi da ya dawo bakin aikin shi, ya hak'ura ya kuma nuna masa komai ya wuce shi dama bai rik'e ba saboda ya san ba laifin shi bane, amma dai ba zai iya komawa aiki ba saboda jiki da jini, amma idan ya amince akwai d'an shi da ke neman kangarewa zai iya had'a shi da shi saiya zauna a mazaunin shi, ya amince ya taho da yaron mai sunan *Rabe*, tabbas ya fara aiki yanda ya kamata sai dai burin Usman akan yaron ba wai ya zama mai kula da pliwoyin (flawers) gidan shi bane da k'ofa, ya na so a gama wannan zagon na karatu sannan ya d'ora shi ya ci gaba da karatun shi tunda ya na yi ya dakatar saboda shirme, duk da haka kuma Usman bai daina bibiyar Khadija ba, yanzu haka har ya gaji da sawa Bilal na rok'on ta akan ta dawo, Hajia da malam dama sun ce ba ruwan su, a k'arshe ya samu da k'yar ya lallab'a Murtala ya je ya mata magana, nuna masa ta yi ba komai za ta koma, amma ya na barin gidan tace ba yanzu sai ya sake shiga hankalin sa, jin shiru shiru ya sa saida ta kai ga Usman ya turo Nura da Kabir da kuma Mannir su ka je bata hak'uri, sai lokacin Mama tasan da irin tsiyar da Khadija ke tsulawa, dan sam babu wanda ya tab'a ce mata ya zo bata hak'uri dan ta koma, Usman kuma idan ya zo ta kan basu wuri ne dan su tattauna, kuma ba ta nuna mata wasu alamu na rashin jituwa, hakan ya sa ba ta san me ke faruwa ba, shi ma Usman ya so ya b'oye mata ne dan yasan za ta iya tirsasata akan ta dawo, duk da ya na matuk'ar so ta koma amma ya fi so ta koma dan ganin damar ta, kuma har yau ba ya ganin laifin ta akan hukuncin da take masa, dan kuwa babu abin da ta rage shi da shi a rayuwa amma ya mata kishiya, sannan ya rasa meya shiga kan shi da ya dinga cin mutuncin ta, dan wasu abubuwan sai yanzu ne idan ya na rarrashin ta take iya fad'a mi shi irin abin da ya mata, bugu da k'ari kuma bata gama hucewa ba ya zo ya bugar mata baki har saida ya kumbura, wanda kullum mitar hakan take masa, nan Mama tace su koma Khadija za ta dawo gidan ta ba jimawa, sun tafi da farin cikin samun nasara amma sam Khadija tace ba yanzu zata koma ba, da Mama ta fara fad'a kuma sai 'yan biyar suka tausheta suka ce tunda ba yarinya ba ce kawai a rabu da ita, hakan ya sa a ranar Usman ke ta zuba idon ganin Dije amma shiru, ko bacci baiyi ba a ranar ya na sak'awa ya na warwarewa, washe gari da dare ya je gidan da kan sa, a falo ya samu duk 'yan biyar d'in da wasu daga cikin yaransu, Mama na d'aki hakan ne ya sa ya zauna suka gaisa sosai, Naseer ne yace "Auta kam ta na ciki, amma kafin ka shiga ciki ka kawo kud'in ganin ta." "To in dai hakane me zai hana ka fad'a min gaba d'aya farashin da zan biya, kaga sai ka d'auke ta da kan ka ka kai min ita gida na." Cewar Usman cikin raha, dariya su ka yi sai Habeeb ne yace "K'anwa ta fa tsada ne da ita, farashin ta baya fad'uwa." Cikin zolaya yace "To kunga, duk cikin kun nan naga babu wanda zai iya taimaka min, dan haka ni zanje na yi yak'i na ni kad'ai, in har k'anwar ku bata koma gida na zuwa gobe ba to ku canza min suna." Cike da cika baki ya mik'e zai nufi d'akin Khadija Naseer ya bushe da dariya yace "Wane sunan za mu saka ma ka to?" Juyowa ya yi ya harare shi yace "Ka zab'a da kan ka mana." Bashir ne ya yi saurin cewa " sai mu saka mi shi *Mani*." Komai baice ba ya wuce d'akin, ko sallama baiyi ba yau dan al'amarin ba sauk'i, kuma cikin sa'a saiya samu Khadija tana ban d'aki, murmushi ya yi kafin ya cire hular kan shi ya aje gefe ya kwanta kan gadon ya yi d'a-id'ai, kusan minti biyu ya d'auka kafin Khadija ta fito daga ciki d'aure da k'irji, kasancewar cikin ta ya sa ya d'age sosai daga sama har ya kan iya hango cinyoyinta, ita kam gilashin ta ne take gogewa ta na k'ok'arin sakawa, ta na sawa ta ja ta tsaya da tsoro fal a idon ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim, innahu min Suleimana wa innahu bismillahir-rahamanir-rahim." Ba tare da damuwa ba Usman yace "A kan ki, wato na ma zama shaid'an ko?" Wata ajiyar zuciya ta sauke ta matso kusan shi tace "... *Ina k'aunar ku.* 06/03/2020 Γ  12:54 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *36* "Malam lafiyar shigo min d'aki haka kawai, wa ma ya baka izinin shigowa nan?" Kamar ba dashi take magana ba ma saiya share ta, ta jima tsaye ta na kallon shi ganin bai damu da tsiyar da take ba ya sa ta juya ta isa gaban madubi ta fara shafe shafe kamar yanda ta saba, lokaci lokaci takan juyo ta kalle shi amma abun mamaki shi kuma hankalin na ga waya ya na dannawa, saida ta gama ta nufi wajen kaya ta d'auko riga, ba tare da ta cire d'aurin k'irjin ba ta saka wando da rigar nono kafin ta saka doguwar rigar, juyowa ta yi ta kalle shi tace "To malam, idan ka gama da d'akin sai ka rufe min

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117