Chapter 8
Chapter 8
"Ba na da wani zab'i da ya wuce na ka, duk abin da ran ka ya ke so shine nawa ya ke so." "To in hakane sai ki tambayi yarima dan ya raba mana wannan gardamar kamar yanda ya saba." Cikin shagwab'a tace "Shi ma kan shi yarima zab'in mu shine na shi, dan haka a matsayin ka na shugaba kuma ja gaba dan Allah ka taimaka ka zab'a mana abin da za mu ci." Hannu ya kai ya ja dogon hancin ta ya na fad'in "Kin ganki ko mai wayo, to shikenan yanzu ki je ki samar mana ko da irin wannan wainar da ki ke had'a ta da miyar kayan ciki." Dariya ta yi tace "Kwad'ai ko? Wato ka ji dad'in ta?" Kamo hannun ta ya yi ya sumbata yace "Duk abin da hannun nan zai tab'a to ya kan zama mafi soyuwa a gare ni." "Shikenan to bara na je na fara aikin, tunda har yanzu *Uwani* ba ta dawo ba bare na tsaya jan jiki." Rik'o ta ya yi yace "Amma dai ban takura ki ba ko?" Sai da ta waina idon ta tace "Gaskiya na d'an takura da ka k'i fad'a min abin da ka ke so tun da wuri." Dariya ya yi ita kuma ta mik'e ta juya, tafin hannun shi ya sa ya daki mazaunan ta, da sauri ta dafe ta juyo ta na kallon shi, far-far ta masa da ido ta juya ta sake juya masa mazaunan da kyau kafin ta fice, tashi ya yi ya haura kan gado ya yi ruf cikin bargo, ita kuma aiki ta fara gadan-gadan. *A GURGUJE* Lokaci ya zo na biki, ta kowane b'angare shiri ake yi, yayyun Khadija da mahaifiyar ta sun sake mata kayan d'aki na gani na fad'a, kaya ne yan uban-ubansu, hatta teburin cin abinci sai da Khadija ta cika kud'i aka bata sabo da ya dace da kayan ta, daga falon ta zuwa uwar d'akin ta idan ka shiga sai ka ji kamar ka fito da mai d'akin kai ka zauna, Usman ma kai da kawowa kawai ya ke, tun yanzu Khadija da Bilal su na ganin sauyi a tare da shi na rashin cikakken lokacin shi, amma ta had'e dan ta san na d'an lokaci insha Allah, amarya ma an shafa an goge anyi jawur, ga bala'in magunguna da take ta kaurawa kan ta, Mariya ma taje wajen malam an basu taimako wanda zai sa Usman ya so ta fiye da kowa, hakan yasa dole ta had'a garin maganin da aka bata ta kwab'a lalle da shi ta shafa a k'afar ta kamar yanda aka ce, sai kuma wanda za ta dinga zuba mi shi a abinci ya na ci, sau d'aya ta yi nasarar saka mi shi kuma ya ci lokacin da ya zo gidan su, shi ma sai da ta fara kukan kissa kad'ai ya ci, dan ya fad'a mata shi wallahi bai saba cin abinci a waje ba ko da kuwa gidan su ya je, da k'yar dai ya ci shi ya sa ma ta aje da tunani har ta shiga gidan, da haka har aka fara da shagalin kamu, washe gari kuma d'aurin aure, a ranar in banda dakan uku-uku babu abin da k'irjin Khadija ke yi, amma cikin k'arfin hali haka ta had'e kishin ta ta taimaka mi shi ya shirya cikin manyan kayan shi irin na Bilal komai da komai har takalma da hula iri d'aya suka saka, ta na kallo ya kama hannun Bilal suka fice sai k'amshi suke, su na fita ta zube kan kujera ta fashe da kuka da iya k'arfin ta dan ta rage rad'ad'i, cikin sa'a sai ga Kaltume ta zo tun da wuri, nan fa ta shiga aikin rarrashi da ba ta hak'uri tare da fad'a mata ta taushi zuciyar ta sannan ta dinga anbaton sunan ubangiji, da haka ta samu ta saisaita nutsuwar ta su ka fara hira, angama d'aurin aure kuma wasu k'awayen nata suka dinga zuwa wanda tafi kusa da su, tare suka shigo da Bilal su ka canza kaya wata shaddar iri d'aya, k'awayen Khadija kam bayan gaisuwa murna su ka taya shi tare da mi shi addu'a ta alkairi, rana ta farko a *tarihin* rayuwar su da Usman ya shiga d'aki Khadija ta kasa bin bayan shi, bayan rasa kuzari da ya yi sai ya kasa shirya kansa, domin kuwa Khadija ta saba mishi da shirya shi ko ta taimaka masa, hakan ne yasa ko mab'allin riga bai b'alla ba ya fito, kasancewar Kaltume su na wasa ta dinga masa dariya wai zumud'i yasa ya kasa b'alla mab'alli, Khadija kam da ta san komai tashi ta yi ba tare da ta yarda sun had'a ido ba ta b'alla mi shi, juyawa ta yi za ta wuce ya rik'e hannun ta sam ya manta da mutanen da ke wajen, juyowa ta yi amma ba ta kalle shi ba, dan haka yace "Sai yanzu ne na fahimci k'arfin wuta da tartsatsin da ke cikin idon ki, ki kalle ni ko sau d'aya mana, hakan ne zai sa na kasance cikin karsashi da kuzari." Kasa tausar zuciyar ta tayi har sai da tace "... *Allah ka nufe mu da sassauk'an kishi mai tsafta da kyawu, Allah kasa mufi k'arfin zuk'atan mu.* 01/01/2020 Γ 12:14 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *6* "Hum! Ai yanzu ba ni kad'ai ba ce hakk'in saka ka farin ciki ke kai na, ka je ka samo farin cikin ka a wani wurin, ni ina da abin yi a gaba na da yafi wannan mahimmanci." Ta na fad'a ta juya ta koma in da ta ke, sam bai ji dad'i har zuciyar shi,sai dai baiga laifin ta ba in ya yi la'akari da yanda kishi ya ke, fita ya yi shi ma zuciya ba dad'i, rana ta yi k'awayen Khadija sun zage sai girki ake ana hira, sam abin da Khadija ba ta yi tsammanin shi bane ya faru, ganin ba kowa ta gayyata ba amma sai ga mutane na ta b'ullowa daga wurare daban-daban, sai dai da gani kasan wani ya zo ya ga me zai faru ne, daga ciki kuma har da dangin Usman wanda sun san ba biki take ba, amma sai ga shi suna zuwa su na yak'e mata bakuna, ita kam da ta fisu sai ta nuna farin ciki take sosai da hakan, musamman da Aziza ta zo tare da Hassana da yan biyun ta Husseina su ma sun zo gidan, kowa da abin da ke ran shi, haka dai aka yage hak'ora kowa ya bar wajen. A k'alla k'awayen ta kusan goma sha biyar ne su ka jira har a kawo amarya, masha Allah, ba k'aramin shiri Khadija ta yi ba, shaddar da ke jikin ta da aikin da aka ma shaddar kad'ai zai nuna maka an kashe dala sosai, dogayen takalma da kwalliyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117