Chapter 65
Chapter 65
*SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€ ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *25* Saida ya gama fad'in abin da ya faru kafin ya d'ora da "Wallahi Mama Khadija ta bani mamaki, wai ni Khadija zata kalla ta dinga fad'awa duk abin da ya zo bakin ta, saboda kawai na mata kishiya saita raina ni, ko kuma dan na mata magana akan abin da tayi bata kyauta bane, wannan abu ya b'ata min rai sosai, shine dalilin da ya sa nacr ta zo gida saina neme ta, banyi haka dan cin mutumcin ta ko cin zarafinku ba, sai dai nasan dole anan akwai wanda za su fad'a mata kuma ta saurare su, dan naga yanzu kishi ya rufe mata ido gaba d'aya." Malam ne yace "Kai dallah rufewa mutane baki, koma menene ai sai kayi hak'uri, duniyar nan uban waye baisan halin mace ba akan kishi, ko kai kana ganin kamar uwarka ba ta da kishin ne, ita kan ta mahaifiyar ta ta da ka ke magana akai ai tasan zafin shi, kenan sai ka yi hak'uri ka d'auke kan ka dukansu na d'an lokaci ne za su yi, in banda rashin hankali irin na ka da can farko ta ma ka haka kafin zuwan amaryar?" Murmushi Mama ta yi tace "Alhaji ka k'yale shi haka, to idan yace ya saka mu su ido suyi yanda su ka dama suna fakewa bayan kishi, ai kuwa kullum da tsiyar da za su b'ullu da ita a gidan, hakan zaisa ba za'a zauna lafiya ba, ni banga laifin shi ba dan hakan shine daidai, ka na ji ko." Mama ta fad'a ta na kallon shi cike da kulawa, kallonta ya yi take kuma ya sunkuyar da kan shi k'asa, d'orawa ta yi da "Ka yi hak'uri dan Allah akan abin da ya faru, insha Allahu zan ja mata kunne hakan ba zai sake faruwa ba, abinka ne da d'an yau ka haife shi baka haifi halinshi ba, babu irin tausar zuciyar da ban mata ba, amma ba ta ji ba ko kad'an, amma ka yi hak'uri kaji, insha Allah za ta kiyaye a gaba." Kallon malam ta yi tace "Bara na kira mu ku ita sai ku tafi ko." Cike da dattako malam yace "Shikenan Hajia mun gode sosai da karamci, Allah ya bar zumunci." Mama na wucewa d'akin Khadija dake ta cika ta na batsewa Usman ya d'ago kai a hankali ya kalli su Ashir da duk su ka hakimce su na kallon shi, d'auke kan shi ya yi dan gani yake kamar za su rufe shi da duka, dan ko basu fad'a ba kasan ba haka su ka so ba, musamman Naseer da Habeeb da bakin su ke ta motsiπ, a d'aki kam tuburewa Khadija ta yi wai babu in da za ta je, saida Mama ta fara nuna b'acin ran ta kad'ai ta fito ta na kumburo baki, wajen yan uwan ta ta tsaya ta ja birki ta na kallon su, Naseer ne yace "Ki yi hak'uri kinji auta, Hajia tace ba ta yarda mu ce komai ba." Kallon Usman ta yi da shima yake kallon ta, har ga Allah kafin ta fito ya ji ya na son ya koma tare da matar shi, amma ya na ganin ta yanzu sai ya ji kamar yace ta yi zamanta ko kuma ya rufe ta da duka, haka kawai ya ji ranshi ya b'ace ko da ya ganta, amma sai ya dake ya mayar da hankalin shi kan Mama da tace "Maza ki bawa mijin ki hak'uri yanzun nan, sannan ki mi shi alk'awarin hakan ba za ta sake faruwa ba, in kuma ki ka sake to fad'an ni da ke ne ba da shi ba." Kamar za ta yi kuka ta kalli Mama tace "Mama, wai ni ce ma zan ba shi hak'uri? Har fa mari na ya yi mama, kuma dama duk na ji abin da ka fad'a ina d'aki." Ta fad'a ta na mayar da hankalinta kanshi, ci gaba ta yi da cewa "Bansan me ya sa za ku yi tunanin na lalata abincin yarinyar nan ba, domin Allah ku dube ni da kyau ku dubi Haseenah, ace na rasa ta yanda zanyi na yi maganinta akan kishi saita hanyar zuba gishiri a abincin ta, haba dai kuma, wannan ai abune da hankali ba zai d'auka ba, kenan ma ta gagare ni?" "Khadija." Mama ta fad'a cikin tsawa, shiru ta yi ta kalli Mama, cikin b'acin rai tace "Rashin kunyar da ya fad'a mana ki na masa ita ce za ki nuna mana sanfurin da ki ke ma sa?" A hankali ta durk'usa duka gwiwoyinta biyu tace "Ki yi hak'uri Mama." "Ba ni za ki bawa hak'uri ba, mijin ki ne gashi nan." Saida ta had'e hawayen ta kad'ai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri." Yanda ta turo baki ne ya sa Mama cewa "Anya kuwa Khadija ke ce? Ke ce Khadija auta ta da na sani." Kallon maman ta tayi ta sake kallon Usman ta saisaita murya tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, insha Allah ba zan sake ba." Da k'yar ya iya k'arfin halin k'ak'aro mata murmushi yace "Ba komai ai ya wuce, ni ma ki yi hak'uri abisa marin ki da na yi, kuskure ne da b'acin rai." 'Anzo wajen." Cewar Naseer, d'agowa ya yi daga jinginar da ya yi a bayan kujera yace "D'an uwa Usman dan Allah a dinga kiyayewa, shi duka a fuska ya na da had'ari sosai, mari kan iya jayo makanta, mari ya kan iya sanadin rasa ji, mari zai iya sakawa haure ya fita, mari kan saka kai ya yi ciwo, dama wasu matsaloli da dama, ka ga sai a dinga sanin me za ayi idan rai ya b'ace." Yasan ba lallai Mama ta yi shiru ba, dan haka ya na fad'a ya tashi ya bar falon ya nufi b'angaren shi, da murmushi Usman ya bishi ya kalli sauran yace "In Allah ya yarda ma ba za ta sake faruwa ba, wannan ma tsautsayi ne." "Allah ya kiyaye gaba." Cewar Ashir, haka suka tashi su ka koma gida, saida ya ajeta gida kafin ya wuce ya kai malam, Bilal ya yi farin cikin ganin mahaifiyar shi, Haseenah kam ba ta ji dad'i ba ko kad'an, sai dai tasan nan ba da jimawa ba za ta koma tunda yanzu sai yanda ta yi da Usman. A matsayin kwanan Khadija ne yau ta shirya ta kuma je har d'akin shi kamar yanda ta saba, tabbas ya kwana d'akin, amma da kwanan shi da rashin kwanan duk d'aya, dan kuwa baya ya juya mata ko uhum ba ta ji daga bakin shi ba har ya yi bacci, amma ita ba ta yi baccin ba sai nafila da ta kwana ta na yi ta na kaiwa Allah kukanta, har asuba tana nan kafin ya tafi masallaci ita kuma tayi sallah, bayan ta kammala ta shiga madafa ta d'ora girki. Usman kuma na dawowa daga masallaci d'akin Haseenah ya nufa su ka gaisa, daga nan ya fad'a mata gobe fa zai yi tafiyar nan ta shirya in tana zuwa, amma bayan tunani da tayi sai taga za'a zargeta idan suka tafi tare,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117