Skip to content

Chapter 94

Chapter 94

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

tuna komai ne ke damunshi, da haka ya isa gidan ya paka mota a k'ofar gidan, zai sallama sai ga Bashir zai fito daga ciki, gaisawa su ka yi cikin mutumta juna kafin yace ya wuce ciki Hajia na nan shi zai fita ne, ba musu ya wuce dan dama ba tsayawa zaiyi ba, Hajia na zaune tsakiyar less da atampopi ya sallama tace ya shigo, zaune ya yi k'asa kamar yanda ya same ta a k'asa ita ma, gaisawa su ka yi kamar kullum kafin ya d'anyi shiru ya na tunanin ta'inda zai fara, shiru ne ya ratsa d'akin kamar ba kowa a ciki, a hankali Hajia ta kalle shi da murmushi tace "Komai lafiya dai ko?" Saida ya rarraba ido kafin yace "Mama, wani abu ne ya ke faruwa da ni da na ke so na samu amsar tambayoyi na anan, dan Hajia ta ma k'i saurara ta bare ta fad'a min me ke faruwa, dan Allah Mama ki taimaka ki fad'a min ina Khadija take? Sannan meya faru tsakani na da ita da har ya sa take zaune gida?" Jim Mama ta yi ta na tunanin to in har iyayen shi ba su fad'a mi shi ba me zaisa ita ta fad'a, murmushi kawai ta yi ta kalle shi tace "Ba komai Usman, ka wuce ta na ciki yanzu mu ke zaune tare da ita ta shiga ta yi sallah." Damuwar kan fuskar shi ce ta k'aru yace "Mama, dan girman Allah ki fad'a min meya faru tsakanin mu, Mama idan ma sakin ta na yi wallahi tallahi bansan na yi ba, shi ya sa na ce mu ku wani abu ne ke faruwa, gaba d'aya na kasa tuna komai ji na ke kamar daga dogon bacci na tashi." Ganin kamar zai mata kuka ya sa ta saki fuska tace "Kar ka damu Usman, ba wata babbar matsala ba ce, ka shiga ka same ta a ciki ku yi magana, idan har ka na so ma za ka iya tafiya da matar ka gida yanzun." Sai lokacin murmushi ya bayyana a fuskar shi yace "Mama da gaske zan iya tafiya da ita? Kai Alhamdulillah Allah na gode ma ka." Dariya Mama ta yi ta na kallo ya shiga ciki, dama k'ofar ba rufe ta ke ba kamar yanda tafi barinta mafi yawan lokuta, ya na tura k'ofar ya shiga ya yi daidai da Khadija ta idar da sallah ta mik'e tare da cire hijabin ta, riga ce jikinta ruwan madara mai k'ananan hannuwa wacce ta kama ta, sai bak'in siket da ya bud'e sosai bai kama jikin ta ba, saida gabanta ya fad'i ganin mutum kawai a d'akin, amma kuma saita kasa motsawa saboda tasan yau ta ta kam ta k'are dan idon shi na kan cikin ta, Usman da tunda ya d'ora idon shi akan cikin ta yaji k'wak'walwar shi ta fara tuna ma sa da wasu abubuwan, mamaki ne fal a fuskar shi har ya fara matsowa kusan ta, ta na ganin haka ta fara ja da baya a hankali shi ma ya na bin ta, daf da ban d'aki ta juya da sauri za ta shige ciki da azama ya rik'o hannun ta. Janyo hannun ta ya yi har saida ya zaunar da ita bakin gadon ya tsaya gabanta sank'am kamar zai fad'a mata ya na kallo, kan ta k'asa ta kasa had'a ido da shi kafin yace "Ya mu ka yi da ke?" D'agowa ta yi tace "Akan me fa?" Had'e rai ya yi yace "Kar ki raina min wayo mana, Khadija me ye hujjar ki na b'oye min ki na da ciki? Akan me za ki min haka?" Mik'ewa ta yi tace "Kaga malam dan Allah kar ka d'aga min hankali, ni babu wani ciki da na ke da, ko kai ka ga na yi ma ka kama da masu ciki ne?" Wani bala'in haushi ne ya taso mi shi amma sai ya share yace "Tashi wuce muje gida sai mu yi maganar acan." "Wane gidan kuma?" Ta fad'a ta na kallon shi, kai tsaye yace "Gidan ki mana." Wani murmushi ta yi tace "Ni ai duk filaye ne gare ni har yanzu ban gina gida ko d'aya ba." Cile da k'aguwa yace "Haba uwar yarima, gidan mu fa na ke nufi, ki tashi mu tafi mana." Cikin nuna rashin damuwa tace "Au! Ai wannan gidan ka ne ba nawa ba, idan da nawa ne ma ai da ba ka yi abin da ka yi ba har na baro ma ka gidan." A hankali ya durk'usa kan gwiwoyinshi ya rik'o hannayen ta yana murzawa yace "Khadija fad'a min me na mi ki in ba ki hak'uri? Ke kinsan ba zan iya cutar da ke ba, tunda mu ke da ke ba mu tab'a samun sab'anin da yasa mu ka raba shinfid'a ba bare gida, dan Allah ki fad'a min sai na baki hak'uri yanzu kuma mu koma gida tare, sanin kan ki ne ba zan iya bacci ba alhalin ke ki na nan." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ka na nufin ka ce ba ka san ma me ka min ba?" Kamar zaiyi kuka yace "Wallahi na manta Khadija, komai ya dawo min kamar sabo a rayuwa ta." Tab'e baki ta yi tace "To kaga ka tashi dai yanzu ka koma gidan ka kafin amaryar ka ta fara neman ka." Tsaki yaja yace "Ina mi ki magana mai mahimmanci ke ki na magana akan wata, dallah malama ki tashi ki wuce mu tafi gida." Waro ido ta yi irin mamakin nan tace "Eyee! Lallai ma mutumin nan, to ba zan je ba ina nan gidan mu." Ba alamar wasa yace "Haka ki ka ce?" Ita ma ba tsoro tace "Eh, haka na fad'a." Yatsunshi ya sa biyu ya kama agarar (jijiyar da ke bayan k'afa kusa da diga-digi) ya dinga murzawa da zafi, da sauri ta janye k'afar ta sai kuwa ya rik'e k'afar ya na fad'in "Ba dai kinfi son na mi ki hukunci a gidan ba? To ai sai mu zuba ni da ke, na ga wanda ya isa ya k'wace a hannu na yau." K'ok'arin k'watar k'afar ta ta shiga yi amma ya hanata dama, idon ta ne suka cika fal da ruwa ta na so ta bashi hak'uri amma ta k'i magana, shi kam ko a jikin shi har cije leb'e yake ya na fad'in "Uhum! Da dad'i ko? To yaya yanzu za ki fad'a min dalilin ki na k'in fad'a min ki na da ciki?" Jin zafi ya kai mata ya sa ta bud'a baki da k'arfi tace "Mamaaaaa, ki zo ki taimake ni." Bushewa ya yi da dariya yace "Kuma a zaton ki za ta zo? Kar ki wahalar dani a banza ki fad'a min abin da na ke son sani." Jin bala'in na k'aruwa ya sa Khadija fashewa da kuka irin na sangartattun yaran nan ta na fad'in "Dan Allah ka yi hak'uri zan fad'a ma ka, wallahi zafi ke akwai, dan Allah ka daina zan fad'a." D'an tsagaitawa ya yi yace "To ina jinki." Saida ta fara goge hawaye tace "To d'anyi baya mana ka matse ni sosai." Kallon da ya mata ya sa ta d'an matsa baya amma sai ya sake binta ba

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117