Chapter 92
Chapter 92
tambaye shi ina malam? A cewar shi ya na k'ofar gida tare suke da shi ma, aika shi ta yi ya yo ma sa magana, a soron gidan su ka had'u da malam in da ta bashi magungunan ta fad'a mi shi duk yanda akayi, murmushi malam ya yi ya mata godiya tare da fatan alkairi, ciki ta koma ta yi zaune su na b'are tafarnuwa, malam kuma na fita ya kira Usman a waya ya na d'auka yace "Duk abin da ka ke ka zo gida yanzu ka same ni." Usman da ke tsaye gaban gado ya na kallon Haseenah ta na shiri zai kai ta can ne yace "To malam, dama yanzu za mu taho gidan." Datse kiran kawai malam ya yi yayin da ya bi wayar da kallo, kallon Haseenah ya yi da ta mik'e ta saka hijabin da ya dace da kayan ta haka ma jaka da takalmi, a gaskiya ta yi kyau sosai cikin wani bak'in leshi mai ji da kud'i da kyau, kwalliyar da ta yi kai kace yau ne bikin kuma ba aiki ne za ta tafi kamawa ba, wayoyinta biyu ta d'auka duka a hannu ta rik'e suka fito, da kan shi ya bud'e mata k'ofa ta shiga kafin ya ja suka bar gidan yamma ta k'ara yi sosai. Daga nesa ne aka fara kiran sallah hakan ya sa Khadija tashi ta yi alwala ta shiga d'aki dan yin sallah, ta na shiga d'aki ta kabbara sallah ta ji sallamar Usman, saida gaban ta ya fad'i kafin ta saita nutsuwar ta ta ci gaba da sallar ta, gaisawa ya yi sosai da mutanen da ke wajen in da Haseenah ke gaishe da mutane ciki-ciki, fita ya yi tare da malam ysu ka yi alwala in da malam ya tara ruwan shi ya aje suka nufi masallaci, mata ma alwala suke su na sallah, Khadija na fitowa daga d'aki Haseenah za ta shiga, dukansu gadara su ka nuna in da Haseenah ta had'a da girman kai da raini, babu wacce ta matsawa wata dan ta wuce hakanne ya sa su ka bangaji kafad'un juna su ka wuce, tsaki Haseenah ta k'ara da shi wanda ya sa Khadija jawo hijabin ta ta kalli fuskarta tace "Kamar tsaki na ji kinyi ko? Da ni ki ke?" Cikin nuna isa tace "Sake min hijabi malama." Dawowa Khadija ta yi cikin d'akin yanda ta ke fuskantar ta da kyau, k'ara shak'o hijabinta ta yi za ta yi magana Hassana ce ta shiga tsakani tace ma Khadija "Dan Allah yi harkar gaban ki, kinsan sai ka kula kashi ka ke jin warin shi, kare kuma ai ba ya haushi shi kad'ai." Kallon ta Khadija ta yi tace "Ta ci albarkacin ma su albarkaci." Ta na fad'a ta fito daga d'akin ta na mu su sallama, Haseenah kam kallon Hassana ta yi wato ma ita ce karyar? K'wafa ta yi a ran ta ta zauna ko sallah ba ta yi ba, ta na kaiwa k'ofar fita malam ya tiso k'eyar Usman zuwa d'akin shi, tsaye ta yi su ka yi sallama da malam Usman kuma idon shi na kan cikin ta dake cikin hijabi ya ke ganin kamar gizo, shigewa malam ya yi Usman kuma ya tsaya bakin k'ofar k'ik'am, rab'awa Khadija ta yi za ta wuce sai kawai ya had'a ta da bango ya rufe kamar zai rumgume ta, kallon fuskar ta ya ke cikin wata irin murya yace "Me na ke gani a jikin ki ne haka?" Fuska a had'e ta kalle shi ta na sake gyara hijabinta tace "Me ka gani?" Hannu ya zuro zai tab'a cikin ta yi saurin bige hannun shi ta ture shi ta kalle shi tace "Ka zama mai d'a'a mana, haka kawai sai ka tab'a jiki na." Za ta fita ya rik'o hijabin ta yace "D'a'a? Ni ne marar d'a'ar?" Kafin ta yi magana ya fizgo ta ya had'a da bango, saida ta rintse ido tace "Ashhhhh." Saboda zafin da taji, hannu ya sa cikin hijabin ta ya na fad'in "Bara kiga rashin d'a'a, ke da kinsan ba na da d'a'ar kuma ki ka aure ni? Yanzun ma fitsara za ki min kenan." Da sauri ta rik'e hannun shi da ke shirin shafa cikin ta, kallon idon ta ya yi yace "Ban sani ba ko gizo ne ido na ke yi min, amma sai na ke gani kamar ciki ne a jikin ki." Shiru ta yi ta kasa d'ago kai ta kalle shi, hannunta da ta rik'e na shi hannun ya kama yatsunta sosai ya na murzawa tare da juyasu son ran shi, tun ta na jurewa har ta fara matse ido saboda mugunta ce yake mata, jin idon ta na neman kawo ruwa ne ya sa ta kalli cikin gidan tace mi shi "Malam fa na jiran ka." Da sauri ya saki yatsunta ya d'an ja baya ya juya ya kalli cikin gidan shi ma, ta na ganin haka ba ta b'ata lokaci ba wajen takawa da sauri ta bar soron gidan, juyowa ya yi dan ya kalle ta sai ya ga wayam, cije leb'e ya yi tare da k'wafa yace "Wato ni za ki rainawa hankali ko, ki na d'auke da ciki na amma ki na b'oye min, wallahi na tabbatar da gaskiya sai ran ki ya yi mugun b'aci, sai kin gane ba'a min haka a zauna lafiya." Ciki ya shiga ya samu malam a d'akin shi, abun mamaki shine izini da malam ya masa ya shiga ban d'akin shi ya yi wanka da ruwan da ke cikin bokiti, idan ya gama sai ya d'auki wanda ke cikin buta suma ya yi wankan da su, yanda fuskar malam ke had'e ya sa dole bai iya tambayar komai ba face shiga ya yi abin da aka ce, tunda ya yi wanka da ruwan cikin bokitin nan ya ji kan shi ya masa bala'in nauyi, jiri ne ya dinga d'ibar sa har saida ya rik'e kan panpo kafin ya ji ya fara masa sauk'i, butar ya d'auka ita ma ya kwararo ruwan daga sama har k'asa, rawa ya ji jikin shi ya d'auka kamar mazari, bala'in da yake ciki ne ya sa ya kasa sako kayan shi sai towel d'in malam da ke rataye ya d'auro ya fito, malam na zaune ya na jiran shi da kaskon garwashin wuta, har zaiyi zaune saboda abin da yake ji sai malam yace "Dakata." Tsaye ya yi malam yasa maganin nan ya na kewara shi da shi, Usman da hatta numfashin shi ya fara canzawa kasa tsayuwa ya yi sai kawai ya fad'i k'asa kwance ya na rawar d'ari, k'amk'amewa ya yi sosai ya na rawar d'ari, sunkuyawa malam ya yi yace "Fodio lafiya ko? Me ka ke ji?" Cikin hard'ewa da hak'oran sa keyi ya iya had'a kalmar "S...ss..an..yi...na..ke.ji." Aje kaskon malam ya yi ya shiga uwar d'aki ya d'auko mi shi bargo ya na zuwa ya rufa ma sa, d'auko wannan garin maganin ya yi ya zauna k'asa kusa da shi ya bud'e ledar ya dangwalo da yatsunshi biyu ya kara masa a hanci yace "Shak'a, shak'a Fodio kaji." Shak'awa ya yi duka hudar hancin shi kafin yaja zanin rufar ya sake rufe kan shi, mik'ewa malam ya yi amma shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117