Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

kalle shi tace "Au! Wai dama duk soyayyar da ku ka yi ba ka tab'a fad'a mata abin da ka ke so ba da wanda ba ka so? Dole sai ni ce zan dinga fad'a mata?" Matsowa ya yi kusanta yace "A gani na ya zama dole tunda ke ce gaba da ita, me ya sa ba za ki d'ora ta a hanya ba a matsayinki na babba?" Da k'arfi ta zaburo daga kan gadon ta sauko ta na fad'in "Oho, wato babba juji ko? Komai tunda ke ce babba ke ce babba, to daga yau na bar mata girman ta d'auka, kuma ka je ka tambaya ta idan ban fad'a mata ba ka cin tuwo ba, amma sai tace a dole ita ma sai ta d'ora ka a tsarin da ya mata, saboda ita ma matarka ce, haka kawai za ka zo ka d'ora min laifi ka cika ni da surutu." Komawa ta yi kan gadon ta kwanta ta ja zani ta rufa, shi kam baki bud'e ya ke kallonta har ta kwanta, sunkuyawa ya yi ya sumbaci kumatun ta ya d'ago yace "Saida safe masifata." Zunbur ta tashi tace "Masifar ka kuma? Abban Bilal ni ce ma masifar yanzu? Lallai ka kyauta." Gimtse dariyar shi ya yi yace "To in ba tawa ba ta wacece? Ai Khadija sai Usman, Usman kuma sai Khadija, kinga dole na kiraki da masifa ta tunda na ga kin fara koyon masifar." Cinno baki ta yi gaba ta bishi da kallo har ya kai k'ofa, sai da ya bud'e ya fita ya juyo yace "Allahya huci zuciyar Umman Bilal, ta Usman bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad'i, na Khadija ba ni shan furataba nono, hakan ya yi ko? Saida safe, ina son ki." Dariya ce ta kubce mata, sumba ta aika masa tare da fad'in "Ina son ka ni ma, saida safe." _Ni ma dai saida safen nan gaskiya._πŸ˜‰ *Washe gari* ta kama alhamis, hakan kuma ya sa duk yan islamiyya na hutu ba karatu, k'awayen Haseenah na su ka zo gidan tun misalin *11:00* bayan fitar Usman ba jimawa, in da Bilal ma ke gida ya na wasan shi, dan ya so ya je gidan su maman Khadija amma ta hana, a madafa suka tare su na ta hira abinsu, kasancewar *Zeinab* na da k'ok'arin aiki ya sa yau ita taja ragamar girkin gidan, abinci su ka had'a kala har uku da kuma abin sha, bayan sun gama su ka dawo falon Haseenah dan cin abinci, kiran Usman ta yi ya aiko a d'aukar mi shi abinci ta na da bak'i a gida, ba d'aukar lokaci ya aiko da yaron shi Bilyamin ya d'auka, su na ci su na kwamtsa hirarsu sai ga Mariya, sai da suka gama ta shiga da ita ciki inda ta kwashe komai ta fad'a mata, bud'ar bakin Mariya cewa ta yi "Lallai Haseenah ina tausaya miki, dan wallahi kishiyar nan ta ki ba k'aramar muguwa bace, kawai ki hak'ura ki bita sau da k'afa, domin kuwa ita da d'an ta ne da gidan nan wallahi." Cike da damuwa Hassenah tace "Ni ma na fahimci hakan, kar ki tona raina ki ji me na ji ranar, ita ce da laifi amma ya rufe ido ya d'ora min laifin, wai shi ya san matan shi." "Ai kad'an ma ki ka gani in dai ba ki tashi tsaye ba, yanzu dai ina magani da na baki? Kinyi aiki da shi?" "Duka na yi, kuma ya ci abincin? Amma ni banga wani sabon abu ba." Gyara zama ta d'anyi tace "Kinsan me zai faru, ki sake kawo kud'i a kaiwa malam ya sake mi ki wani maganin, ko da na bakali ne da kuma samun soyayyar shi." "Kamar nawa?" Ta fad'a ta na kallonta, ita ma kallonta ta yi tace "Eh to, iya kud'in ki ai iya shagalinki." Da alamar tambaya Haseenah tace "Ki na nufin idan na bayar da kud'i dayawa zaifi kyau aikin?" "Sosai ma." Mik'ewa ta yi ta bud'a jakarta da take zuba kud'in da yake bata tun da ta zo, yan biyar biyar ko karyawa babu guda hud'u ta bata, aifa baki har waje ta karb'a suka fito daga d'akin, sallama su ka yi ta tafi ta barta da k'awayen ta, yamma ta yi suka sake tashi kama mata aiki, sai dai suna buk'atar bredi dan soya shi da k'wai, babu yaron da za'a bawa ya siyo sai Bilal ta kira dake farfajiyar gida tare da mai gadi, kud'i ta bashi ya siyo mata bredi, cikin sanyin jiki yace "Aunty nan ba'a siyar da bredi sai can nesa tsallaken titi, kuma Abba ya hana ni fita har can wajen." A gadarance tace "Kenan ba ka da wani anfani cikin gidan? Sai dai a dafa a baka ka ci? To k'arya ka ke, maza wuce ka d'auko wannan shegen moton na ka da baida anfani sai dai ka yi yawo da shi cikin gida ko k'ofar gida ka je ka siyo ka kawo min yanzun nan." Cikin sanyi ya juyo ya nufo wajen uwatai, d'akin da ya ke aje moton ya fito da shi, Khadija na gani tace "To, to ina kuma zuwa da wannan tuk'a-tuk'ar?" Sai da ya zo gabanta cikin turo baki yace "Ba aunty amarya ce ta aike ni siyan bredi ba." Da mamaki ta kalle shi tace "Bredi fa? Amma ba ka fad'a mata ba ka tab'a zuwa ko bakin titi kai kad'ai ba bare gaban shi?" "Na fad'a mata, amma tace wai ni ban da anfani a gidan sai dai na ci abinci, kuma wai dole na je na siyo." Wata shegiyar dariya Khadija ta bushe da ita ta kalle shi ta kalli Uwani, mik'ewa ta yi tace "Ku biyo ni har da ke Uwani." Fita su ka yi har madafar ta same su, sai shewa da hira su ke, suna ganin ta kowa ya yi shiru sai wani kallo ake mata, ko ta kan su bata bi ba ta kalli Haseenah tace "... *Ku yi hak'uri da wannan.* 29/01/2020 Γ  13:36 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _INA K'ARA TAYA 'YAR UWARMU KUMA D'AYA DAGA CIKIN 'YAR GIDAN AMANA WATO MEMBER'S D'IN K'UNGIYAR *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA* MAI SUNA *MARYARHMAH UMMISIDDIQUE* MARUBUCIYAR *MINTI KARU'NYI YE* DA KUMA *NAGA TA KAINA* TA'AZIYYAR RASHIN UWA MAHAIFIYA DA TAYI, INA ADDU'A GA UWAR KIRKI HAR KULLUM ALLAH YAKAI RAHMA K'ABARINTA, ALLAH YA K'ARA MANA HAK'URIN RASHINTA, MUNYI RASHIN UWAR K'WARAI😰_ _Bismillahir rahamanir rahim_ *17* "Haseenah, ga Uwani ki bata kud'in ta siyo mi ki bredin, amma Bilal mahaifin shi ya hana a aike shi ko kusa da titi." Sai lokacin ta juyo ta kalle ta tace "Yanzu kamar Bilal ne za ace ba'a aikin shi, shi kad'ai ne yaro cikin gidan nan, kuma ace ba'a aikin shi, to me ya sa? Me ye anfanin haihuwar shi kena..." Ba ta sauka daga abin da za

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117