Chapter 22
Chapter 22
b'arke baki ne ya sa ya tsaya ya na kallon fuskar ta, da sauri ya mayar mata ya fara goge mata hawayen yana fad'in "Dan Allah ki yi hak'uri Khadija, banyi haka da wata manufa ba, ki yi hak'uri ki daina kukan to, na daina, shikenan?" Share hawayen ta yi ta tashi daga jikin shi ta koma d'aya kujerar ta na ci gaba da share hawaye shi kuma yace "Ki rufa min asiri Khadija, yanzu me ki ke tunanin zai faru idan yan biyar d'in ki su ka shigo su ka same ki kina kukan nan? Ina tabbatar mi ki rataye ni za su yi a jikin pankar nan." Ya fad'a ya na nuna pankar sama da ke falon. Kallon shi ta yi tace "Ka yi hak'uri to." Yanda ta yi magana cikin shagwab'a ba k'aramin birge shi ta yi ba, murmushi ya yi yace "Ai ni ne da baki hak'uri, tun da na fahimci ba kya so mu k'ara samun kusanci." Haka dai suka kammala ya mik'e zai fita ya fito da jikka uku ya bata, kallon shi ta yi tace "Na miye wannan?" Murmushi ya yi yace "Da taimakon Ashir ni ma yau gashi ina bayar da kud'in cefane." Dariya ta yi tace "Ai ba sai ka bayar ba, akwai duk abubuwan buk'ata." Sunkuyowa ya yi yace "Sai abin da ba'a rasa ba ko?" Shiru ta yi ya janyo hannun ta ya d'ora mata kud'in yace "Kar ki rage min darajata mana." Murmushi ta yi tace "Angode, Allah ya saka da alkairi." D'agota ya yi tsaye ya rumgume ta, yarrrrr, dukansu suka ji saboda dukansu shine karo na farko, shiru su ka yi kowa da abin da ya ke ji a game da d'an uwan shi, kamar ba za su rabu ba sai kuma suka raba jikin su, ba su yarda sun kalli juna ba sai Usman ne yace "Wannan ranar ita ce iyaye na ke min burin shiga, su na yawan fad'a min idan na yi aure ko kud'in cefanai na bayar idan har na yi sa'ar samu mace ta gari, to tabbas za ta gode min akan hakan tare da min addu'a." Shiru ta yi ita dai har yace "Ni zan tafi, sai na dawo." "Allah ya kiyaye, Allah ya tsare ka ya bada abin da aka je nema." "Ameen ameen, nagode sosai." Har ya juya zai fita ya sake juyowa ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta, ficewa ya yi ya bar ta tsaye ta na tunanin sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a cikin k'ank'anin lokaci, kayan da suka b'ata ta fito da su ta wanke ta gyara wurin sannan ta d'an zauna ta huta, ba jimawa sosai ta d'ora girkin rana, ita kad'ai ta gama aikinta ta yi wanka ta shirya, ta na zaune ita kad'ai yaran mak'otansu suka shigo su ka tayata hira, har la'asar ba Usman ba labarin shi, ta idar da sallah ta d'ora girkin dare kenan Hassana da Husseina su ka zo tare da Aziza lokacin ba ta fi shekara uku ba a duniya, wannan abincin ta juye mu su suka ci suna ta hira, zuwa k'arfe *biyar* na yamma su ka tashi tafiya, turaren wuta da na jiki da kud'i ta basu su shiga taxi, haka suka fita su na fad'an ta da alkairi cike da k'aunar ta dukansu, har suna mamakin yanda ta so su bar Aziza wajen ta, aikinta ta ci gaba da yi har ta na daf da k'arasa miya, kamar jiran fitarsu ya ke sai gashi ya shigo gidan, cike da gajiya da kasala ya zauna akan kujera kusa da ita ya na sauke numfarfashi ya na cire hular kan shi yace "Wallahi na gaji sosai." Cike da kulawa ta kalle shi tace "Sannu, aiki ka yi sosai?" Ido rufe yace "Wallahi ina fita *Murtala* ya fizge ni mu ka tafi wani k'auye, na d'auka zamu dawo da wuri amma Allah bai nufa ba." "Ayyah! Sannu." Kallon ta ya yi yace "Ko zaki had'a min ruwan wanka?" "To, to." Ta fad'a ta na tashi kamar za ta ruga a guje, ta na kai mi shi ruwan ta d'auki kwandon sabulu ta kai mi shi da towel, dawowa ta yi ta d'ibo ruwan sha ma su sanyi ta durk'usa gaban shi tace "Ga ruwa ka fara sha to." Karb'a ya yi yace "To zan sha saboda daga hannunki su ka fito, amma bayan wanka na fi buk'atar abinci gaskiya." Sororo ta kalleshi ta had'e yawu, rarraba ido ta fara yi gabanta na fad'uwa, dan ba ta saune miya ba ma bare ta d'ora macca, ko da yasha ruwan ya mik'e zai wuce tace "Ka fad'a min me za ka iya ci yanzu na dafa maka?" Ta fad'i hakane ko da zai ci wani abu mai sauk'in sarrafawa. Juyowa ya yi da mamaki yace "Ban gane ba, ki na nufin ba ki d'ora komai ba tun da na fita?" Cikin nutsuwa tace "Wallahi na d'ora, na yita jiran shigowar ka amma shiru, sai kuma su aunty Hassana su ka zo kawai sai na juye mu su abincin." Murmushi ya yi yace "Wai su aunty, Hassana fa k'annai na ne su, ba sai kin kira su da aunty ba." Cikin jin kunya tace "Amma ai ni sun girme ni." "Duk da haka, dan na tabbata da zasu fita da ke aka tambaye su wacece ke? Za su ce matar yayan su ce, ke ma kuma dole ki kirasu da hakan." "To na ji, yanzu dai ka shiga ka fito." Dariya ya yi ya wuce, ta na ganin shigarshi ta gaggauta k'arasa miyar ta, da sauri ta d'ora ruwan macca, ya na fitowa ruwan sun taso ta zuba maccar, cikin sauri ya shirya ya fito zai fita, rik'e shi ta yi da hira tace ya koma ya zauna za ta bashi wani abun mamaki, zaune ya yi ya na kallo yana jiranta, baifi minti sha biyar ba ta shigo da kwanuka masu kyau da gani ta aje gaban shi ta d'auko ruwa da lemo da faranti ta aje masa, sai da ta zauna gaban shi zata zuba mi shi yace "Amma ina ki ka samu wannan?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "Abincin dare ne za ka ci tun yanzu." Dariya ya yi yace "To idan daren ya yi kuma ya zanyi?" "Sai na girka maka na safiyar gobe ka ci." Dariya ya yi sosai yace "Da alama zan cinye abinci na kafin kwana na ya k'are." Dariya ta yi sosai har hak'oran ta na fitowa waje sosai, duk da ba ta jin yunwa sai da ya takura ta ta ci abincin tare da shi, daga lokacin kam ta yarda cewa ba zai iya cin abinci ba tare da ita ba, ya na gamawa hira su ka dinga yi kamar dama sun saba har saida magrib ta gabato kad'ai ya fita. *Allah ka mana kyakyawan k'arshe.* 18/01/2020 Γ 17:42 - πππ: ππππππππππ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ ππππππππππ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_π§πΌ *(UWAYEN GIDA)* πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117