Chapter 50
Chapter 50
manta gidan nan ba bak'o na bane." Cikin dariya Haseenah tace "Na sani kam, ai yanzu ma ina jiran ranar da za ki sake kawo mana ziyara ne." "Zan zo, amma sai an koma makaranta (school) dan yafi dad'i, saboda yafi kusa kuma nafi jin dad'in zama a lokacin." K'awar ta ta kalla tace "Ina zuwa *ma chérie.*" Wucewa ta yi Haseenah ma ta shiga ciki dan ganin mijin ta, Aziza na shiga kai tsaye wata yar drower ta bud'a, cikin sa'a kam ta lalabo abin da ta ke nema, murmushi ta yi tace "Yawwa, na samo shi." Ta na fad'a ta saka a k'asan siket d'in ta kafin ta fara had'a indomie, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta fito da ita a cikin faranti, su Haseenah na zaune ta aje tace "To to bismillah, ba zan jira kowa ba fa." Haseenah kallon indomien ta yi sosai yawunta ya tsinke, sai dai kuma a k'oshe take bare ta ci, sai dai ta na mamakin yanda suke dafa indomie haka gwanin kyau da dad'i, ga dukkan alama ma Azizar ta koya ne a wajen Khadija tunda kamar babbar yar ta ce a yanda ta samu labari, ba ta ci ba sai kallon su da take su na hira har su ka kammala, sun tashi tafiya ta shiga ciki ta d'auko kud'i sosai ta basu su hau adaidaita, haka su ka fita cikin jin dad'i da kuma samun nasara wajen Aziza, ko takan Khadija ba su bi ba bare su mata sallama, su na shiga adaidaita aka fara aje k'awar Aziza, daga nan ita kuma gidan Hassana ta wuce, ta na zuwa ba ta yi k'asa a gwiwa ba wajen bata wannan abun, saida ta k'are ma sa kallo sosai ta kalli Aziza jiki a sanyaye tace "Aziza kinsan me ye wannan?" Kai ta girgiza tace "A'a, amma dai shine ta ke zubawa a shayi, wani lokacin ta daka wani lokacin kuma ta saka a haka." Tsakin jin haushi Hassana ta yi tace "Wannan fa minana ce, k'wallon ta ne wannan kafin a daka ta zama gari." "To miye shi d'in?" Cewar Aziza, cikin jin haushi tace "Ana had'a maganin mata da shi, watak'ila akwai wani anfani da ya ke da a jikin namiji ne da ya sa take sakawa." *Hotiho, ki koma makarantar mata* Dafe kai ta yi tace "Me ya sa ma banyi tunanin haka ba? Tun farko ya kamata musan ba za ta tab'a aje wani abu muhimmi a madafa ba, bugi da k'ari ita fa k'awar Kaltume ce." Cikin rashin jin dad'i Aziza ta baro gidan ta koma gida, ta na zuwa gida ta samu malam ba ya jin dad'i zazzab'i mai tsanani, ya sha magani amma har yanzu rawar d'ari ya ke, hakan ya sa aka kira Usman da a lokacin ya ke gida tare da amarsu, cikin gaggawa ya canza kaya ya fita zuwa gidan, ya na zuwa kuma asibiti su ka nufa da shi aka ba shi agajin gaggawa, an bashi taimakon amma kuma ya na buk'atar jini, nan fa yaran su ka shiga layi dan a gwada nasu a k'ara ma sa, gwajin farko aka gane na Usman ya dace da na shi, ba'a b'ata lokaci ba aka kwasa aka k'arawa malam, sun jima a asibitin su na kai da kawowa har dare ya yi sosai. Ya na zuwa kai tsaye d'akin shi ya wuce, a can Haseenah ta same shi har ya shiga wanka, shiga ta yi su ka yi wankan har su ka fita, cikin shagwab'a ta kalle shi tace "Ni fa yunwa na ke ji." Kallon ta ya yi sosai, ya na ji kamar ya tuhume ta akan rashin tambayar shi lafiyar mahaifin shi, amma kuma sai ya share yace "Ki yi hak'uri, me ki ke so ki ci yanzu?" Cikin tiro baki tace "Abu mai dad'i na ke so." "Kamar me?" Ya sake fad'a ya na d'aukar wayar shi a gaban madubi, "Koma meye." A cewar ta ita ma. Waya ya yi Bilyamin ya sa ya kawo mi shi duk abun buk'ata, har ya gama shiryawa ita ma haka, suna zaune ya ji ya gagara samun nutsuwa saida yace "Ba ki tambayi jikin Baba ba, kamar abun bai dame ki ba, har da jini fa aka k'ara ma sa, kuma nawa aka d'iba." Ya k'arasa da nuna mata hannun shi da aka d'ibi jinin. Kallon shi ta yi cikin rashin jin dad'i take ta k'ak'aro hawayen k'arya tace "A ganin ka ban damu da ku bane ko me? Kasan halin da na shiga saboda rashin dawowar ka da wuri? Duk da ana fad'a min wayata babu kud'i amma bai hana ni kiran lambar ka ba saboda tunanin ko za su duba girma da soyayyar da na ke ma ka su aika kira na a wayar ka, amma a haka ka ke cewa ban damu ba? Lallai ma." Mik'ewa ta yi irin ta yi hushin nan za ta fice, Usman kam sai ya ji kamar ta na zuba ma sa ruwan zafi wannan kukan da take, da sauri ya rik'o ta ta fad'o kan sa ya shiga rarrashi, da k'yar ta yi shiru tace ya wuce, lokacin kuma Bilyamin ya kawo mu su abinci, da kan shi ya fita ya amso tare da bashi kud'i yace ya rik'e canjin, dawowa ya yi ya kawo mata amma kafin ta zuba yace "Bara na shiga na ga yarima, nasan yanzu dai ya yi bacci." "Amma fa idan ka jima ba zan jira ka ba." Ta fad'a ta na nufa kan teburi ta d'auko faranti, baice komai ba ya fice, ai kuwa a falo ya samu Khadija ita kad'ai zaune, idon ta akan telebijin amma da gani kasan hankalin ta ba nan ya ke ba, da sauri ta zabura ta sauke idon ta akan shi, shi ma ita ya ke kallo amma da wani irin yanayi na tsana da haushi, mik'ewa ta yi ta nufe shi da k'arfi ta fad'a kan jikin shi ta sauke ajiyar zuciya ta na sake rumgume shi sosai, cikin muryar kuka ta furta "Na yi kewar ka Abban Bilal." A hankali cikin dubara ya raba ta da jikin shi ya na d'an k'aramin tsaki ya kalne ta yace "Me ye na kuka kuma?" Kamar wacce ya mara sai ta sake fashewa da kuka saboda bak'in cikin da ke zuciyar ta, sunkuyar da kai ta yi k'asa ta na jiran ta ji ya janyo ta jikin shi ya gara rarrashi kamar yanda ya ke, amma sab'anin haka sai cewa ya yi "Wai me ye na kukan dan Allah yanzu cikin daren nan? Wani abu aka mi ki?" Girgiza kai ta yi cike da mamaki ta na kallon shi, cikin jin haushi ya d'ora da "Shine kuma za ki tasani gaba ki na kuka, ba na son koke-koken nan ni wallahi, haka kawai da girman ki da komai ki tsaya ki na kuka, ke ba duka ba, ba zagi ba, salon jawa mutane magana." Wani tsaki ya kuma yi kafin yace "Ina Bilal ya ke?" Khadija da bakin ta ke bud'e kamar k'adangare zai shiga ciki ta nuna mi shi k'ofar d'akin Bilal, cikin hararen ta yace "Ya yi bacci ne?" Saida ta zura hannu ta cikin gilashin ta ta share
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117