Skip to content

Chapter 77

Chapter 77

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Zan kira Baba na fad'a mi shi ya yi hak'uri zan je anjima, shikenan kinji dad'i?" Dariya ta yi ganin ya cire hular shi da takalma ya fasa tafiyar, ko farfajiyar gida babu wanda ya lek'a a cikin su suna d'aki suna soyayyar su, hatta abinci sai dai ya kira Bilyamin ya siyo ya kawo mu su, haka dare ya yi amma Haseenah na jikin Usman, da ya yi maganar tafiya wajen Baba za ta fara shagwab'a wai zai barta ita kad'ai, haka ya k'arar da wunin na shi bai je kiran Baba ba kuma bai kira shi a waya ba. Tunda malam ya ga shiru ya tabbatar da zargin shi na cewa akwai abin da ke damun Fodio, ganin har dare ya yi anyi shirin bacci ya sa malam samun Hajia a d'aki har ta fara bacci ya tashe ta, saida ta wartsake yace "Bacci fa bai kama ki ba, tashi ya kamata ki yi mu duk'ufa da addu'a, dan shakka babu Fodio ba kan shi d'aya ba." Saida ta k'ara murza ido tace "Malam, ban gane ba, me ya ke faruwa da Fodio kuma?" "Shiga gaba." Ya bata amsa kai tsaye kafin ya d'ora da "Na yi mamakin da ku ka kasa fad'a min gaskiyar abin da ya faru a gidan shi, kun fad'a min ta karb'i makulli da k'arfi, amma ba ku fad'a min ta karb'a bane saboda za ta kai Bilal asibiti, yaron da aka barwa Haseenah ya wahala saboda babu mahaifiyar shi nan, sannan shi kuma Fodio bai fad'a min ya daki Khadija ba, ke ma kuma ba ki fad'a min ba." "Duka malam?" Ta fad'a da dafe k'irji, d'orawa ta yi da "Wallahi ban sani ba ni ma, bai fad'a min ba ko alama." Gyara tsayuwa ya yi yace "Har da duka, kinga yanda ya kumburawa yarinyar nan fuska da kin tausaya mata, tun jiya ta na kwance babu lafiya har zuwa safiyar nan da na je gidan ana k'ara mata ruwa, wannan abun kunya da me ya yi kama? Kinga yanda ran 'yan uwanta ya b'ace su na cewa ba za ta koma ba si in ya zo ya nemi ta koma tare da alk'awarin ba zai sake tab'a lafiyar jikin ta ba, kuma ni banga laifin su ba ko kad'an dan su na da gaskiya." Shiru Hajia ta kasa magana saida malam ya sake cewa "Na fahimci yarinyar nan ta na biyar shi da sharri, ba kuma alkairi bane ya kawota gidan nan, dan haka k'arya take tace za ta cutar da ahalina wallahi, ko da boka take yawo ni nan zanyi maganin ta, Allah ya fi k'arfin ta wallahi." Kallon Hajia ya yi da zufa ta rufe ta yace "Ke ma ki taya d'an ki da addu'a." Fita ya yi daga d'akin ita kuma ta k'ara gudun masuburbud'ar sanyin dake d'akin, ta jima bacci bai sake d'aukar ta ba ta na tunani akan abin da malam d'in ya fad'a, anya kuwa Haseenah za ta iya yin haka? Yarinyar da a zahirance ita ake cutawa, taya za ace kuma ta cutar da wani? Kai da kamar wuya gaskiya. *Da kamar wuyar zata kassara ku.* 21/02/2020 Γ  19:15 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *29* Sai k'arfe *10:25* suka tashi daga bacci, Usman ne ya fara shiga wanka da tunanin ya gaggauta shiryawa dan ya fiya kiran malam, ya sakarwa kan sa ruwa kenan Haseenah ta shigo ban d'akin, bahon wanka ta cika da ruwa ta had'a sabulu a ciki ta cire d'aurin k'irjin ta, da k'arfi ta jashi su ka famtsama cikin bahon su biyu, dama abin da take so kenan, shi ya sa ma ta yi anfani da damar wajen b'ata lokaci suna wanka da 'yar shiriritarsu irin ta amare, sun d'auki lokaci kafin su ka fito haka nan ma wajen shiryawa saida su ka jima, suna fitowa falo cikin shiri ya kalle ta yace "Mummyn beby yau ma ba ki dafa mana komai ba fa, ya za mu yi kenan?" Zaune ta yi akan kujera tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki masarrafar telebijin (remonte) ta kunna tace "To ai ina ganin ba sai na yi girki ba, tunda kaga amarci mu ke ci, ko ba haka ba?" Zaune ya yi kusan ta ya na fad'in "Kuma fa da gaskiyar ki, dan mafiya yawancin lokuta idan na dawo daga tafiya sai dai muje cin abinci kawai." Cike da izza ta na karkad'a k'afa ta kalle shi tace "Oho, kenan aka ake yi, amma shine ni ba za ka iya d'auka ta ba muje?" Waya ya ciro daga aljihu yace "Yanzu dai bara na fara kiran Bilayamin ya kawo mana na karin kumallo, anjima da dare sai muje mu ci ko, hakan ya mi ki?" "Ba damuwa." Ta fad'a cike da k'asaita, ta na ji ya bawa Bilyamin sallahun abin da suke buk'ata su ci, bayan d'an lokaci Bilyamin ya iso da abincin, ya na karb'owa kai tsaye kan teburi ya nufa da shi ya d'auki faranti ya zuba ya kalle ta daga in da ta ke zaune yace "Madame ki taso abinci na jiran ki." Tashi ta yi cikin tako d'aya bayan d'aya ta isa, zaune ta yi akan cinyar shi ya dinga saka mata abincin a baki, saida su ka gama ya tashi zai fita tace "Babban mutum ni fa gida na ke so ka aje ni, idan za ka shigo da dare sai ka biya mu taho tare." "Gida kuma?" Ya tambaya da mamaki, "Eh, gida." Jim ya d'anyi dan gaskiya a tsarin shi ba'a mi shi haka ko kad'an, ace sai yanzu ne kawai za ta fad'a masa ta na so ta fita kuma yanzu yanzu saboda raini, had'e fuska ya d'anyi yace "Ki yi hak'uri mana Mummyn beby, ki bari har gobe sai kije." Yamutsa fuska ta yi tace "Gaskiya yanzu na shirya tafiya, in kuma ka hana ni wallahi kuka zan kwana ina yi a gidan nan." Ta na gama fad'a ta mik'e ta nufi hanyar falon ta, ganin fa da gaske ranta zai b'ace ya sa ya yi saurin rik'o ta ya had'a da jikin shi yace "Shikenan to naji, ran gimbiya ya huce, je ki d'auko hijabin ki sai mu tafi." Cikin farin ciki tace "Da gaske kake?" Cike da tabbatarwa yace "Sosai ma, ai ba na da wani abu da ya fi min ke mahimmanci, zanyi hidimar ki kafin na yi tawa, ki yi sauri ki je." Cikin d'an lokaci ta d'auko hijabi da jaka da takalma duk kala d'aya suka tafi, ba jimawa ya sauke ta gida tare da bata kud'i kafin su ka yi sallama, mahaifiyar ta kad'ai ce a gidan a farfajiyar gida zaune, bayan sun gaisa sosai suka fara tab'a hira, anan ne mahaifiyar ta tambaye ta ko ta na anfani da magungunan ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh, ina sha

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117