Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

hawaye tace "Eh." Juyawa ya yi rai b'ace yace "Saida safe." Har ya bud'e k'ofar kuma ya tsaya yace "Baba ba shi da lafiya ya na asibiti,ku yi k'ok'ari da safe ku je ku ga jikin shi." Fuskar ta kad'ai ta nuna mi shi damuwar da ta shiga a lokacin, saida ta matsa kusan shi tace "Me ya samu Baba? Ya jikin na shi yanzu? Ina fata fai da sauk'i?" Sharewa kawai ya yi yace "Da sauk'i." Kamar ansa shi dole, zai fita ta sake cewa "Ka tabbatar ya na lafiya? Gaba d'aya ba na jin dad'in jiki na." Sama da k'asa kawai ya kalle ta ya wuce abin shi, daskarewa ta yi a wajen ta na tunanin abin da ke shirin faruwa da su koma ya faru d'in, ta jima tsaye kafin ta kashe wuta ta wuce d'akin ta, alwala kawai ta d'oro ta zo ta kabbara sallah, tun daga nan ta fara kaiwa Allah kukan ta tana neman agaji da mafita, sai kusan *uku* na dare bacci ya d'auke ta, kuma ana kiran sallah ta farka ta taje ta tashi Bilal shim, Usman da kan shi ya zo ya tafi da shi suka shiga masallaci. Ko da gari ya yi haske Khadija ta shiiryawa Bilal abun kari ya ci, shiryawa ya yi Baban shi ya tafi kai shi islamiyya, daga nan kuma asibiti ya wuce ya samu jikin malam da sauk'i sosai ya na ta hirar shi akan gado, ya na dawowa ya gida ya sake kwanciyar shi , Khadija kuma ta shirya dan zuwa ganin Baba, ganin shiru babu wanda ya mata magana ya sa ta kira wayar shi, a lokacin Haseenah ta gama soya k'wai da dankalin turawa ta shirya cikin ado mai kyau, ta na ganin kiran amma ta yi banza da ita, ta na ji ta na gani ta hak'ura da tafiyar sai Hajia ta kira ta tambayi mai jikin tace za ta shigo anjima. Wani abun haushi shine a lokacin Haseenah ta tashi Usman daga bacci wai sai ya kaita asibiti ta ga Baba, tun ya na cewa bacci ya ke jin har ya wartsake ya tashi ya yi wanka ya shirya, wajen tebur suka nufa su ka cika cikin su kafin yace su tafi, *11:00* cif suka fita daga gidan ba tare da sanin Khadija ba, dan lokacin ita ma har bacci ya d'auke ta daga nan haka ma Uwani saboda shirun ya yi yawa. Da isar su asibiti ta samu su Hassana zaune a bakin wata bishiya akan tabarma su na ta hira, nan ta zauna suka fara gaisawa, Hajia da ke tsaye da buta a hannu ce ta fara cewa "Yo ina Khadija? Ai na d'auka tare za ku taho tunda ta kira ni." Kalar Haseenah ta sani kam sai cewa ta yi "Aunty ai ta na gida bacci ta ke, watak'ila sai da rana ta taho." "Uhum." Cewar Hajiar ta wuce sabgar gaban ta, Rabi'a ce ta fara cewa "Hum! 'Yar hutu ce kinsan, kuma shi ba zai iya tashin ta ba saboda gudun b'acin ran ta." Husseina ce tace "To kinsan da haka ma miye na wahalar da bakin ki wajen fad'a." Hassana ce ta kalli Haseenah tace "Haseenah dai ki dage sosai kinji ko da addu'a, kar a shantake ayi ta bacci, dan matar nan da ki ke gani ba Allah ne a gaban ta ba, ke ma wallahi watak'ila tsananin rabo ne ya shigo da ke gidan, tunda ba tun yau ake mi shi maganar k'ara aure ba, amma da an mi shi maganar yanda ki ka san ka zagi uwar shi da uban shi haka ya ke kallon ka, mufa har saida ta kai ya daina sakar mana fuska." Murmushi Haseenah ta yi tace "Insha Allahu su aunty babu abin da zai faru, Allah ai ba azzalumin bayin sa bane." Husseina ce tace "Allah sarki yar albarka, Allah ya kare ki daga sharrin ta." "Ameen." Ta fad'a da murmushi, mik'ewa ta yi tace "Bara na shiga na ga jikin Baban." Ledar bayan ta ta janyo mai d'auke da kayan marmari kala kala ta d'auka ta wuce, da kallo su ka bita kafin Hassana tace "Wallahi yarinyar tausayi ma take bani, sukuku da ita ba kazar kazar." Rabi'a ce ta yi tsal tace "Ai ba ki ga abun tausayi ba sai randa mu ka je gidan shegiyar nan ta kusa k'ona ta, wallahi inda kinga ta ma bud'e baki ta yi magana kasawa ta yi sai da k'yar." Haka su ka ci gaba da tattaunawa har suka fito su ka mu su sallama suka koma gida, saida ya wuce ya d'auko Bilal dan lokaci ya yi kafin su ka wuce gida, k'arar bud'a k'ofa ne da mai gadi ke yi ya sa Khadija farkawa, ta ga motar Usman ce sai dai ba ta ga tare da wa yake ba, Bilal na shigowa ya tabbatar mata da shine ya d'auko, d'aki ya wuce dan cire kaya Khadija kuma ta kalli Uwani tace "Bara na shiga madafar da kai na idan bata fara aiki ba na d'ora mi shi ko indomie ce." "To." Ta fad'a ta bita da kallo, ba ta samu kowa ba dan haka ta shiga abin da ya kawo ta da gaggawa, saida ta kammala ta fito dan d'auko farantin da za ta zuba, Bilal ta gani ya fito daga d'akin da da ledar bredi a hannu da gwangwanin madara, da sauri ta nufe shi ta karb'e madarar ta na fad'in "Sau nawa zan fad'a ma ka ba na son ka na anfani da madarar nan haka kawai idan ba a cikin shayi ba." Cikin kukan shagwab'a ya biyo bayan ta ya na fad'in "Mummy yunwa na ke ji fa, ki zuba min ko kad'an ce." Juyowa ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani taimaka dan Allah d'auko faranti a d'akin can ki juyo indomien da na dafa." "To." Dai ta sake fad'a ta nufi d'akin, Khadija dawowa ta yi ta zauna akan kujera tace "Zauna yanzu Uwani za ta kawo ma ka indomien ka ka ci." Cikin turo baki ya aje bredin ya zauna in da ta nuna masa, Uwani kuma na shiga ta samu Haseenah tsaye ta d'auki indomien nan ta na juyeta wajen da ake zuba ruwan datti, da sauri tace "Kai, aunty amarya Umman Bilal ce ta dafa ta yanzu." A wani gatsine ta juyo ta kalle ta tace "Wacece hakanan kuma?" Shiru Uwani ta yi dan ba ta san me za tace ma ta ba, hakan ne ya sa Haseenah zuwa ta shak'i wuyan rigar Uwani tace "Me na fad'a mi ki? Bance ba na son sake ganin ki a madafar nan ba idan ina girki? K'azama da ke kawai ki dinga cud'anya cikin mu sai kace kema wata matar shi ce, dallah fice min daga nan." Yanda ta tura Uwani da k'arfi sosai ya sa ta yi baya kan ta ya had'u da bango, fitowa ta yi dafe da kan ta ta samu Khadija ta fad'a mata komai, Khadija ta so ta yi magana kan abin da ta yi sai kawai ta share ta sa Uwani ta d'auko gas d'in ta suka kunna, ruwan d'umi ta fara d'orawa Bilal ta had'a mi shi shayi sannan ta sa Uwani ta

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117