Chapter 107
Chapter 107
ta yace Bilal na asibiti kwance a dalilin ta, to me ya samu Bilal d'in? Ta tambayi kanta, kallon maman ta tayi tace "Mama." "Um." Ta fad'a ta na kallon ta, cikin taushin murya tace "Mama me zai hana ke da Baba kuje ku dibo jikin Bilal?" Sake kafe ta da ido ta yi tace " Bilal kuma? D'an Usman d'in?" Ita ma ta na kallon ta tace "Eh mama." "Dama ba shi da lafiya amma ba ki fad'a ba sai yanzu?" Shiru ta yi ta na sosa kai, tsaki ta yi tace "Allah ya kyauta, Haseenah ko ba ku yi zaman mutumci da matar shi ba ai ina ga dai kya fad'a aje a duba shi ko dan awa Usman kara, ke da shi fa yanzu wata alak'a ce mai k'arfi ta shiga tsakanin ku, ki daina ganin ya sake ki hakan ba shi zai ruguza alak'ar ba." Da rana bayan Baban su ya shigo mahaifiyar su ta fad'a mi shi ta na so taje ta duba jikin Bilal, da yake dama matar ta fi shi hankali da hangen nesa shi ya sa yaran ma suka fi shakkar uwar akan uban, sai kawai yace ai babu mutumci tsakanin su da Khadija, 'yar su na gida ne saboda ita dan haka babu in da za ta je, nan ta nuna mi shi ba saboda Khadija zata je ba saboda Usman za su je, d'an shi na asibiti kwance ya na da kyau suje ganin shi, ai kuwa bai bari ta tafi ba dan sosai ya rufe ido shi bai yarda ba, haka ta hak'ura ba dan ranta ya mata dad'i ba. A wajen su Khadija kuma jikin Bilal da dama sosai, suna zaune tare da shi ya d'ora kan shi a k'afafun Mama su na hira, Mama ce tace "Wai ni kam banji motsin abokiyar zaman taki ba, ko bata nan ne?" Sai lokacin Khadija ta iya tuna bata fad'awa Mama ba, da sauri tace "Kai, Mama ashe baki sani ba ko? Wallahi bata nan gidan tunda na dawo." Mamaki fa a fuskar Mama tace "Bata gidan, to meya faru? In ce dai lafiya?" Cike da damuwa Khadija tace "Mama yace sakin ta ya yi, kuma na so yi masa magana amma ya nuna kawai babu ruwa na, sannan na yi magana da Hajia ita ma tace wai na fita harkar ta, sai dai ni gaskiya banji dad'i ba mama saboda ganin halin da take ciki abar a tausaya mata ce." Cike da jimami Mama tace "Ah sosai ma, komai ai hak'uri ake yi ba a yanke hukunci cikin hushi ba." Tab'e baki Khadija ta yi tace "Mama kullum tunani na shine idan ni ce ya zanyi? Abun baya min dad'i ko kad'an, amma tunda ya nuna baya so na rabu da sh." "A'a Khadija." Cewar Mama ta katseta kafin ta d'ora da "Duk da baya so ke ya mata kisan hanyar da za ki shawo kan shi cikin hikima, na sani Khadija kishiya babu dad'i, kuma burin kowace mace ta zauna ita kad'ai a gidan mijin ta, amma ina so ke ki zama ta daban a cikin mata, Khadija idan kika zama silar dawowar ta to kin saka mata alkairi da sharrin da ta mi ki, wannan kuma shine nagarcin addinin ki, yafiya, mantawa, kyautatawa, kinji ko Nana Khadija, ki yi wannan jarumtar ko da baya so, amma idan kinga abun zai zama matsala to sai ki barshi kawai." Da murmushi tace "Insha Allahu Mama zanyi, nima dama na so tun farko na yi hakan, amma yanzu kin k'ara k'arfafa min gwiwa, tunda ko ba komai sun ruga da sun zama d'aya shi da ita tunda ta na d'auke da cikin shi, rabuwar kuma ba dad'i musamman ita da k'ananan shekaru." "Gaskiya kam, dan hakan zai iya zama tozarci gare ta da b'ata mata suna." Cikin nutsuwa Khadija tace "Mama ba lallai ma a kalle ta da laifi ba, ni ba zan fita daga zargi ba tunda dama ana ganin na mallake shi, kinga yanzu za'a ce ni ce na fitar da ita daga gidan, babu wanda zai tuna lokacin da ni na d'auka a na mu gidan gaban iyaye na, nata ne yanzu zai fito fili kowa ya ji." Cike da gamsuwa mama tace "Gaskiya ne kam, dan ko ansan kin zauna a gidan ma za'a d'auka kishin ki ne ya tura ki gidan, mutum, mutum ai sai Allah." Murmushi Khadija ta yi tace " *Mutum mugun ice, ya mutu ma fa sai an d'aure shi Mama.*"Dariya Mama ta yi kafin suka ci gaba da tattaunawa. Washe gari da safe ma daga Haseenah sai maman ta a gidan duk kowa ya tafi harkar gaban shi, rana ta fito sosai Mariya ta shigo d'auke da kaya da alaman sabuwar d'auka ce ta yi, gaisawa su ka yi sosai har ta fara hira da maman ta akan kasuwancin na ta, sun jima nan kafin maman su ta tashi ta shiga d'akin su dan yin wani abun, Haseenah na ganin haka tace "Aunty Mariya, muje d'aki ina son magana da ke." Cikin rad'a tace "To lafiya dai ko?" Saida ta mik'e ta nufi d'akin tace "Ki zo kiji ke dai." Mik'ewa ta yi ta na fad'in "To na ji alkairi." Suna shiga bakin katifa suka zauna Haseenah ta tsareta da ido tace "Aunty Mariya, na d'auka abin da ya faru da ni za ki taimaka min wajen ganin na koma gidan Usman, amma ke ko a jikin ki ma sai harkokin gaban ki kike." Cewar Mariya "To me zanyi in ba harkokin gabana ba, sannan wane irin taimako ki ke buk'ata daga gare ni yanzun?" A daidai lokacin da Haseenah za ta yi magana a lokacin mahaifiyar su ta fito daga nata d'akin, za ta wuce ne taji Haseenah tace "Ki yi wani abu mana na koma gidan shi, Ko so ki ke na haihu gida?" Kallonta Mariya ta yi tace "Na yi me? Me ki ke nufi? Wai na sake komawa wajen malam? Sam wallahi ba da ni ba, ai na fad'a mi ki tun ranar Haseenah gaskiya ba zan iya binki mu tsunduma kogin da ki ke neman jefa mu a ciki ba, idan na yi haka to fa nan gaba ba naki auren bane zai mutu har da nawa." Wani kallo Haseenah ke mata amma ba tace komai ba, d'orawa ta yi da "Kinga k'anwa ta, ki yi hak'uri da abin da ya sameki ki rugumi k'addara, sakin aure ba'a kan ki aka fara ba bare ya k'are kan ki, yanzu idan mu ka ce zamu matsanta sosai to wallahi abubuwa ba za su yi kyau ba, dan ko da an sake juyar mi shi da tunani ya dawo kan ki wallahi ranar da ya sake dawowa hankalin shi a karo na biyu to fa zai sake koroki ne, dan haka abin da yafi kawai ki tuba ga Allah tare da rainon cikin ki har ki haihu, domin Allah fa kin cutar da su sosai, kin raba shi da matar shi, kinsa dangi suna mata kallon marar imani kuma mai laifi, alhalin kuma ke ce mai laifin, ke ba ma dangin shi ba kad'ai har dangin har yanzu suna kallon Khadija a matsayin wacce tasa aka sake ki,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117