Chapter 95
Chapter 95
tare da ya mik'e tsaye ba, shiru ta yi shi kuma ya sake kamo k'afar ta yace "Ke fa na ke saurare, muguwa kawai, da meye nufin ki to? Ban cancanci zama uban d'an ba ko kuma ke kad'ai ke da shi? Allah sai kin fad'a min dalilin ki ko na rabu da ke." Tangale kanta ta yi da hannayen ta ta rufe fuska ta na tunani, a hankali taji ya d'an d'ago ya zauna bakin gadon ya rumgumota jikin shi, cikin taushin murya yace "Nana, ki fad'a min komai da ya faru mana, meye ake b'oye min haka da ba'a so na sani? Kowa na tambaya sai ya yi shiru ba ya son fad'a min komai." D'agowa ta yi daga jikinshi tace "Kaje ka tambayi Hajia ko Baba su za su fad'a ma ka komai." "Ban damu da sanin komai ba Khadija, na fi damuwa da sanin abin da ya sa ki ke zaune gida." Tallabo fuskarta ya yi yasa idonta cikin na shi yace "Khadija me nai mi ki da zafi haka?" Kamar za ta fashe da kuka tace "Mun samu sab'ani ne da kai akan amaryar ka, sab'anin da ya sa ka yi abin da ba ka tab'a yi ba a rayuwar ka, shine ni kuma na dawo gida gaba d'aya a lokacin ba ka buk'ata ta a gidan ka." Da tsantsar mamaki yace "Sab'ani? Amma me na yi to?" "Duka, duka na ka yi." Ta k'arashe da sunkuyar da kan ta k'asa tana hawaye, dafe kan shi ya yi yace "Duka? Ni da hannu na?" Tsaye ya mik'e jiki a sanyaye ya sake sunkuyawa gabanta ya d'ago fuskarta yace "Ki yi hak'uri Khadija, wallahi Allah bansan na yi ba sai yanzu da ki ke fad'a min, ki gafarce ni dan Allah kar ki hukuntani da laifin da bansan na aikata ba, yanzu haka kunyar had'a ido na ke da ke da ahalin ki." Ya na fad'a ya tashi ya fita ko juyowa baiyi ba, Mama ya samu a in da ya barta da alama kan ta ya d'au zafi, sunkuyawa ya yi yace "Mama, Khadija ta fad'a min abin da ya faru, Mama ina mai baku hak'uri da gaba d'aya zuciya ta, ku yafe min dan Allah, ba dagangan na yi ba, kuma banyi dan cin zarafin ku ba, hasalima abu ne da sam banyi tsammani ko tunanin faruwar shi ba." Mik'ewa ya yi tare da cewa "Saida safe Mama." Ya fad'a ya na barin falon ba tare da jiran me za ta ce ba, Mama kam sai taji tausayin shi ya kamata sosai, watak'ila har ya yi anfani da maganin da Garba ya kawo cewar Mama a zuciyar ta, Khadija ma tausayin mijin ta ne ya sa ko fitowa ba ta yi ba ta kwanta daga nan kuma bacci ma ya d'auke ta. Kai tsaye gida ya sake komawa ya samu malam zaune k'ofar gida sai Bilal gefen shi da wayar shi a hannu, zaune ya yi akan tabarmar ganin haka ya sa malam cewa "Fodio lafiya dai na gan ka haka?" Idon shi cikin na malam yace "Ba lafiya Baba, Baba ka fad'a min dan Allah me ya faru da ni ne? Sannan me na aikata a lokacin da na rasa tunani na? Kawai ganin abubuwa na ke kamar sabi kuma kamar a almara." Tank'washe k'afafu malam ya yi yace "Fodio, abubuwa sun faru da dama, idan da ka nutsu kai da kan ka za ka iya tuna komai, amma ka kasa kwantar da hankalin ka ma bare har ka samu nutsuwar." Cike da damuwa yace "Baba ina maganar nutsuwa ga wanda ya na kallo rayuwar shi ke barazanar fita daga gangar jikin shi, a yanzu haka fa Khadija na gidan iyauen ta zaune da kuma ciki na a jikin ta, Baba ban ma san tsawon lokacin da ta d'auka acan d'in ba." Murmushi sosai malam ya yi yace "Watan ta uku yanzu." "Wata uku?" Ya fad'a da k'arfi da zaro ido kafin ya d'ora da "Baba da sakin ta na yi fa da yanzu ta kammala idda kenan? Kutumar bala'i, Allah ya ceceni." Dariya malam ya yi kafin yace "Ai kam dai, dan ni dai ka ganni nan ba zan tashi zuwa yi ma ka biko ba da girman ka da komai." "Yanzu dai malam ku fad'a min abin da ke faruwa da ni, ina so na sani." Gyara zama malam ya sake yi bayan dogon tunani da ya yi kafin yace "Abin da ya faru da kai ba zamu dangana shi da kowa ba, dan har yanzu ba mu san mai wannan alhakin ba, dan haka kai ma ba na so ka d'auki laifin ka d'ora kan wani ko wata, ka barwa Allah kawai shine zai ma ka sakayya." Jinjina kai Usman ya yi alamar gamsuwa kafin malam ya ci gaba da bashi labarin iya abin da ya sani kawai daga barin Khadija gida zuwa yau d'in nan, sosai al'amarin ya girgiza Usman tare da bashi mamaki, to shi kam waye abokin gabar shi da har zai mi shi haka? Kasa tunawa ya yi sai kuma zuciyar shi tafi ta'allak'a mi shi komai da Haseenah, dan a ganin shi ita ce za ta iya sawa ya manta da Khadija dan ta bar gidan ita ta zauna, to amma kuma malam yace kar ya d'orawa kowa laifi, ya barwa Allah zai ma sa sakayya dan haka ya ja baki ya yi shiru, amma kuma abin da ya ji yanzun ya sa ya tuna da abubuwa dayawa da su ka faru, sai dai ba duka ba, saida safe ya mi shi dan lokacin har bacci ya d'auki Bilal daga nan, ganin zai shiga mota ya sa malam cewa "To matar ta ka fa wa ka barwa ita anan? Ko nan za ta kwana ne?" Zaune ya yi cikin motar ya kira ta a waya yace ta fito, ba wani jimawa ta fito cikin takun k'asaita da izza dan dama zaman gidan ya isheta, kafe fuskata ya yi da ido har ta k'araso, tabbas ba munin fuska ba ko munin halitta, sai dai wani abun al'ajabi wani irin haushin ta ne yake ji na taso mi shi, wanda ko farko duk da ba wani son ta yake sosai ba amma dai ba ya mata irin wannan k'iyayyar, zagayawa ta yi ta shiga suka d'auki hanya ba tare da sunwa juna magana ba, jin shirun ya yi yawa kuma ya d'auki hanyar gida ya sa tace "Kasan fa ba mu da abin da za mu ci a gida, ka siya mana kafin mu wuce ko." Cikin isa da gadara ya juyo ya kalle ta, a hankali kuma ya d'auke kan shi daga kallon ta cikin mak'oshi yace "Uhum." Saida ya tsaya ya siya mata iya cikin ta kafin suka wuce gida, suna shiga ya nufi k'ofar na shi falon, da sauri tace "Beby, ina kuma za ka je?" Juyowa ya yi yace "... *Gidan uban da ki ka aike shi mana.*🙊🙈 04/03/2020 à 19:43 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑 _SAMIRA HAROUNA_ *Litattafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117