Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Kallon Kitse Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fahimta shine Haseenah ba ta ji dad'in abin da ta yi ba, ita kuma ta yi ne saboda ita ce silar zubar mata da girkin da ta d'ora, juyawa ta yi ita ma za ta tafi sai kuma ta juyo, idon su ne suka had'u da na Usman da ke kallonta, kamar yanda tasan ba ya iya shirya kansa da kyau in ba ita ta taimaka masa ba, hakan ta ke da yak'inin ba zai iya zuba abincin nan ba in ba wani ya zuba masa ba, dawowa ta yi ta zuba mi shi ta zauna nesa da shi tace "To maza ka bada himma." Kwab'e fuska ya yi yace "In dai ba za ki ci ba ni ma haka." Kallon shi ta yi tace "Gaskiya sai dai ka jira Haseenah ta zo ku ci, wanka yanzu kawai na ke son yi." Rumgume hannaye ya yi a k'irji yace "Da alamar maganar ki ke so." Wata dubara ce ta fad'o mata dan haka ta mik'e tace "Shikenan to ina zuwa, bara na kira Bilal." Ta na fita ta samu Bilal a falo tace "Bilal, tashi mahaifin ka na jiran ka ku ci abinci, ina zuwa yanzu ka ji." "To Mummy." Ya fad'a yana nufa falon, wanka ta shiga shi kuma ya na zuwa Usman ya rumgumo shi jikin shi ya na fad'in "Yarima na ya ka ke?" Baice komai ba ya kalli Usman d'in ya na turo baki, lab'e baki Usman ya yi yace "Ko dai yaro hushi ya ke da baban sa ne saboda bai je d'aukar shi ba?" Sai lokacin ya saki fuska yace "A'a Abba, bacci na ke ji." Duk da girman yaron amma haka ya zaunar da shi akan cinyar shi yace "To idan mun ci abinci sai ka yi baccin ko?" A tare suka saka hannu su na cin abincin su na hira, har sun ida su na nan zaune suna ci gaba da hirar su irin ta d'a da uba Haseenah ta shigo, kallon ta Bilal ya yi yace "Sannu aunty." Da murmushi har kunne ta amsa da "Sannu yarima, ya ka ke?" "Lafiya lau." Ya fad'a ya na saukowa daga k'afafun Usman, fita ya yi daga d'akin Usman bai hana shu saboda ya na so ya yi magana da ita, ya na ganin fitar shi ya kalle ta da kyau lokacin da take shirin zaunawa, riga da siket ne na kanti wanda su ka kama jikin ta sosai, siket d'in ko k'asa bai gama sauka ba, sannan babu d'an kwali a kan ta, sai da ta zauna yace "Haseenah, yanzu ki na ji a jikin ki wannan kayan sun dace ki saka su a yanzu kuma har ki fito da su?" Da mamaki tace "Ban gane ba? Me wannan kayan su ka yi?" Murmushi ya yi yace "Ba fa mu kad'ai bane a gidan nan, wannan kayan da ya dace ki saka ne da dare lokacin da mu ka rage daga ni sai ke." Cike da tsiwa irin ta yan zamani tace "Matsala, wannan ita ce matsalar da ake magana in dai har ka auri me mata, ba ka isa ka sake ka wataya yanda ka ke so ba, yanzu dan Allah me wannan kayan su ka yi? Na ga kai miji na ne, me ye dan na saka wannan kayan a gida na?" Har kas'an zuciya maganar ta ta tsaya mi shi a rai, amma sai ya kawar da kai kawai ya mik'e yace "Zan fita ni sai anjima." Binshi kawai ta yi da harara, dan yau ita zuciyar ta fal take da tarin k'unci, wani faranti ta janyo gaban ta ta bud'a kwanukan, sai da taja numfashi saboda k'amshin da ya daki hancin ta, ai kuwa zubawa ta yi sosai ta kuma ci ta k'oshi ta ma manta waya girka, dan har ga Allah abincin ya mata bala'in dad'i, ko dan ta na jin yunwa ne oho. Khadija ma na gama shiryawa sai da ta yi sallah kafin ta cika cikin ta da kayan marmari da yan dubaru, daga nan kuma bacci ta shiga dan a huta ma rai. Kiran sallah ne ya tashe su duka gidan, Bilal masallaci ya nufa kafin ya dawo ya shirya zuwa makaranta, Usman da kan shi ya zo ya d'auke shi su ka tafi lokacin Haseenah har ta shiga girkin dare. *Mummyn Sultan* *Mamienmu* *My sweet Hawwer* *My lovely Hawwer* *Mummyn Ameer & Khairat* *Sis Alawiyya* *Sis Fusseina* *Momyn Rasil* _Da duk wanda baiji sunan sa ba, zaiji anan gaba insha Allah._ 23/01/2020 Γ  13:43 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ *KALLON KITSE* _(Ake wa rogo)_ πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘ _SAMIRA HAROUNA_ *Littatafan marubuciyar* *1* _KAUSSAR_ *2* _D'AUKAR FANSA_ *3* _BA SO BANE_ *4* _AUREN HAD'I_ *5* _SANIN MASOYI_ *6* _JIHADI_ *7* _K'ANGIN RAYUWA_ *8* _ITACE K'ADDARARMU_ *9* _KAWU NA NE_ *10* _MAATA_ *11* _KALLON KITSE..._ *SADAUKARWA GA* _MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)* πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S* _(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€› ```Fatan alkairi masoya``` _Bismillahir rahamanir rahim_ *15* Haseenah dai a shirye take da samu zuciyar mijinta ita ma, hakan ya sa yau ma abinci ware mu su na su ta yi ta kai falon ta, sannan ta zuba maganin saboda ta na so yau ya ci na uku kenan, Bilal ta k'walawa kira tun daga madafar, hankalin shi ya tafi kan kallon da ya ke a *mbc action*, Khadija da ta fito daga d'aki cikin doguwar riga ta shadda ne tace "Bilal ba ka ji auntyn ka na kiran ka ne?" Da sauri ya mik'e ya nufi k'ofar ya na fad'in "Banji ba Mummy." Ganin ya nufi k'ofar falon ta ya sa tace "Ta na madafa ina jin." Da sauri ya nufi can, ya na zuwa ta mik'o mi shi kular abinci tace "Abincin ku kai da maman ka." Jiki a sanyaye ya karb'a ya na kallon ta da mamaki, haka ya juyo ya fito ya kawo abincin maman shi na zaune, aje kwanan ya yi gaban ta ya d'ago ya fad'a kusan k'afafun ta yace "Mummy abincin mu ne wai inji aunty." "Abinci kuma?" Cewar Khadija ta na yamutsa fuska, "Eh." Cewar shima Bilal d'in, gyara zamanta ta yi kamar wata hamshak'iya matar shugaba akan kujerar tace "Ka kaiwa mai gadi shi." Ba musu ya d'auki kwanon ya fita da shi, ya na zuwa ma har ya samu ya na cin na shi abincin, cike da ladabi ya aje kwanon gaban shi yace "Baba *Garba* ga abincin ka." Da mamaki ya kalle shi yace "Abinci na kuma d'an Alhaji? Ai gashi nan har na kusan kai shi k'arshe ma, ko dai makuwa ka yi." Da dariya Bilal yace "A'a Baba, wannan Mummy e tace na kawo ma ka." Jim ya d'anyi kafin ya janyo kwanon gaban shi ya na fad'in "Allah sarki, Hajia ta d'auka ba a aiko min da shi bane ina ga? To ka ce angode ka ji ko, ai ba'a maida abinci ba, ko almajirai na bawa tun da na koshi ma." Juyawa Bilal ya yi Garba ya bi shi da "Sai da safe d'an Alhaji." Duk abin da ya faru akan idon Haseenah wacce ke shirin rufe madafar, k'wafa ta yi tare da mirmushi ta rufe kafin ta wuce d'akin ta, sai da ta gama shirinta tsaf cikin riga da wando masu

Table of Contents

Chapters

117 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117