Chapter 99
Chapter 99
a gaba da fada. Tundaga wannan rana Nafi bata kara bari sun hadu da Ashraf ba, sai dai tana ganinsa a b'oye ganib hankalinsa kamar a kwance yake yasa itama ta kara kwantae da nata. ********** Yau Ashraf na zaune a office Salin ya kirashi ya sanar dashi tabbas Auwal Max an ganshi yanzu ma suna tare da wanda yasa ya nemoshi suna hanyar zuwa kano tare. Dadi sosai ya kama Ashraf ya kira dan sandan nan abokinsa yace " ka nemomin Dan siyasan nan dana ce maka?" Yace " haryanzu dai ranka ya dade ba labari." Ashraf yai ajiyar zuciya. Nan sukai sallama, Ashraf ya kalli Dan Litti dake tsaye yace " ana azahar kazo mu tafi." Yace " ok sir, amma maganar Asim." Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ya d'ebi kudin company din?" Dan litti yace " inaji dan d'azu Zakari ya kira yace yakaimai cikon kud'in." Ashraf ya hada hannayensa yace " good, kace ya bashi takardun company din ya kuma yi signing." Dan litti cikin mamaki yace " amma in akai haka ba a bashi company din ba?" Ashraf yai murmushi yace " ai dama so nake ya zama nashi." Dan litti yamai kallan mamaki sannan yace " ko da yake Ina ni ina sanin abinda Kake tunani?" Dariya sukama juna kafin Dan Litti ya fita. Nace Hmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *77* Ana azahar Dan Litti yazo suka fita shida Ashraf, gidan Salim suka wuce. Falo suka nufa inda Salim yace musu Auwal max na ciki, Ashraf ya kalli Dan Litti yace " dole ne ka hade rai ka maida abu serious." Dan litti ya jinjina kai sannan suka shiga. Ashraf da sauri ya isa gun Auwal ya kama hannunsa cikin nuna tsananin kulawa yace " Uncle kana lafiya? Badai abinda ya sameka ko?" Auwal cikin tsananin mamaki ya ke kallan Ashraf. Ashraf yace " ko ba Auwal bane?" Yace " nine Auwal Max" Ashraf ya zaunar dashi sannan ya zauna a gefensa ya kama hannunsa yace " nine Asim, babban d'an gidan Mansir." Sai a lokacin Auwal ya saki fuska, Ashraf ya kara rike hannun sa Yace " Abba ne yace in tabbata na samoka kafin Ashraf ya fara samunka." Auwal yace "Ashraf D'an....?" Ashraf ya karasamai " dan Abbas marigayi." Idanu Auwal ya zaro cikin tsananin tsoro yace " ya akai ya sanni?" Ashraf ya dan saki fuska cikin yanayin damuwa, Dan litti yace " bincike yake akan abinda ya faru a baya." Auwal cikin tsananin rud'ewa yace " inalilahi ya zanyi? Nikam na shiga uku, banda masifun da suke afkuwa akaina yanzu kuma wannan?" Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Abba yace inkula dakai sannan yace in tambayeka ranar meya faru? Har dakai akai hatsarin ko yaya?" Auwal ya kalli Ashraf yace " mantawa yai? Ai na sanar dashi komai." Shiru Ashraf yai yana tunani, sai jin Auwal yai yace " bayan mun shiga mota ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, aikuwa tana kira yace inje shi bari yaja motar, da alama dai Mansir ya manta da hakan." Ashraf yai dariya yace " da alama kasan yanzu abubuwa sunmai yawa dole ne mantuwa ta dinga shiga." Auwal ya jinjina kai, Ashraf yace " amma ai ba wata hanya da Ashraf zai gane kaine ka lalata birkin ko?" Auwal yai shiru yana tunani kafin daga bisani yace " kai, babu sai dai in mahaifiyarka." Cikin mamaki Ashrad yace " Umma?" Auwal ya jinjina kai yace " ita kadai ce ta ganni lokacin da nake aikin, bayan ita gaskiya ba kowa." Ashraf yai murmushi yace " ai bakomai indai Umma ce, amma Dady fa?" Auwal yace "Dady?" "Hisham nake nufi." Auwal yai dariya yace " shi ai bashi ya sani ba shine dai ya bani kudin aikina." Ashraf yace " nasan wannan wai nufina baku kara haduwa ba?" Auwal yace " ina zanganshi nida na koma garinmu?" Ashraf ya kara rike hannunsa yace "karka damu Abba yace inkula dakai ba abinda zai faru." Auwal yai ajiyar zuciya sannan yace "tunda na taho gabana ke faduwa sai yanzu hankalina ya kwanta." Ashraf yamai murmushi. Auwal ya kalli Ashraf yace " Amma kafi kama da Abbas, sam baka kama da mansir." Ashraf ya shafi fuskarsa yace " duk ba jini d'aya bane su? Kowa haka yake cemin wai nafi kama da Marigayi, shikuma Ashraf din inka ganshi abin mamaki kamarsu d'aya da Abbana." Auwal yace " ikon Allah, ai nikam bazan taba mantawa da Abbas ba, naci amanarsa na yaudaresa shiyasa nake ganin ishara kala kala." Ashraf yace " karka damu ka kwantar da hankalinka." Auwal ya daga kai. Ashraf ya kalli Dan litti yace " ka maidashi gidana na Darmanawa." Dan litti ya amsa da to, sannan ya kalli Auwal yace muje ko? Ashraf ya mikamai kudi yace kasai mai abinda zai bukata na nan da sati d'aya. Kallansa Auwal yai yace "har sati zanyi anan?" Ashraf yace " tsoro nake kar mu maidaka Ashraf ya sa a kamaka." Jin zancen kamawa yasa yace "to ai ba laifi satin ma." Nan sukai waje Ashraf ya bishi da wani kallo na takaici, sannan ya zaro wayarsa dayai recording ya sa a computer ya yanke maganar daga inda yace " _Nine Auwal Max_" Ya tura ma Kawu da d'aya wayarsa. Kawu wanda ya fito daga meeting kenan ya ga anturo mai email yana bud'ewa yaji muryar Auwal da abinda yace. Mamaki ya kamashi, meye hakan kuma???? Bai kawo komai ba yai gaba. Salim ya kalli Ashraf yace " amma kana tunanin zaiji wani abu dan yaji suna kawai?" Ashraf yai wani murmushi yace " it won't be fun in na turamai komai a lokaci d'aya, so nake naga yanda hankalinsa zai fita daga jikinsa a kowace rana, yana wannan case din ga kuma na d'ansa." Salim ya dafa Ashraf yace " U are very smart Ashraf sai dai please kayi a hankali dan ina tsoron wannan kawun naka." Ashraf yace " karka damu Uncle, sannan ina tunanin Mumy ne, in barta anan ko inkaita wata kasar, kar ya hanani komai saboda ita." Salim yai shiru sannan yace " tabbas kayi tunani dan kuwa zai iya cewa zai mata illa inkaki bin umarninsa." Ashraf yace " shi nake tsoro." Uncle yace " ka sata kawai ta tafi umara, taje ma ta nemi yafiya tai ibada ko ta samu rangwame." Ashraf yace " nagode Uncle." Nan ya fito. ********** Su Asim an mallaki company murna a wannan rana ba'a magana, dashi da Anisa da Umma da sauran kannansa sunje sunga guri kowa ya yaba sannan ya kira mahaifinsa ya sanar dashi. Mamaki ya kama Kawu a ina Asim ya samu kudin siyan Company? Sai dai haka ya karasa company din dan tabbatarma idanunsa. Mamaki sosai yakeyi ganin wannan katon guri wai mallakin d'ansa ne, ya kalli Asim cikin zargi yace " ina ka samu kud'i?" Asim yai shiru yana tunanin karyar da zaiyi, sai dai kafin ya furta komai sai ga wasu mutane ne nan su hud'u sanye da kayan 'yan sanda sunzo kusa da Asim. Nan fa kowa ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115