Skip to content

Chapter 105

Chapter 105

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,176 words 0 views Progress saved
Download Book

Cikin tashin hankali yace " ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d'azun nan fa na barta a gida." Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada. Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf. Kallansa ya dingayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace " ina Uwarka?" Ashraf yai dariya yace " haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?" Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace " no no no ai bai kamata ka nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won't be fun." Ya sake murmushi sannan yai ciki. Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki😏 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *82* Kawu cikin tashin hankali yai gida, b'angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, yana zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b'angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan. Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na 'ya'ya, shikam a yanda yakejin zuciyarsa gaskiya bai yarda da hakan ba, kaunar Ruma da yakeyi bayaji ko tsufa yai da ita zai daina santa. Ashraf kam gun Kb ya shiga Kb yace " kaje kuwa?" Ashraf yace " naje sai dai abin ba dadi." Ganin bayasan maganar yasa Kb yace " yanzu mutuminka ya fita." Ashraf yadan yi tsaki kadan yace " na ganshi, ya waccan fa?" Ya fada yana kallan inda aka killace Asim." Kb yace " yanacan." Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje inada abinyi." Nan ya fito, baiga kawu ba hakan yasa yai murmushin mugunta yace " ko kaifa, dan banaso ka badani." "********** Kawu kuwa gida ya taho da gudun gaske yana zuwa ya ajiye mota ya fito, ko kofar bai rufe ba saboda tsananin firgici, bangaren Mumy ya nufa, kwado kuwa ya gani daga kofar da zata sadaka da bangarenta, kofar ya shiga jijigawa cikin wani irin kunar rai, ba shakka bazai taba yarda a dauke mai Rumansa ba, shifa a iya saninsa yaji ance in har mace da namiji sukai aure na wasu dan shekaru to fa soyayyarsu na tafiya sai dai kimma da hakuri yasa zama ya d'ore, sai dai shikam abin ba haka yake ba, yanaji dole ne ya zauna da Ruma ko ya samu nutsuwa, kofar ya dinga jijigawa, ganin ba yanda zaiyi yasa yai b'angarensa cikin tashin hankali. Waya ya dauka ya dinga kiran layinta sai dai duk a kashe, tashin hankali kam ya shigeshi a wannan ranar. ******** A can bangarensu Nafi kuwa, sun isa Abuja lafiya, sai dai tun da suka sauka Nafi ke kwara amai, gashi sam ta kasa cin komai, Mumy cikin damuwa tace " Nafi anya kuwa ayi tafiyarnan dubifa yanda kiketa amai." Murmushin yake Nafi tai tace " Mumy karki damu, tafiyar mota ce kawai ta sani haka, kinsan mu filanuwa akwai mu da hararwar mota." Mumy ta gamsu da zancen Nafi, a haka har suka kwanta bacci. Da safe kuwa jirginsu ya d'aga. Sai kasa mai tsarki. *********** Shikam Ashraf da safe bayan ya tashi ya fito daga gidan shi da Dan Litti, wata envelope ya mikama Dan Litti yace " yaje gidan Dady kawai ya ba mai gadi yace a bashi, ya juyo karya bari Habib ko wani daga cikin gidan ya ganshi." Dan Litti ya amsa da to, sannan ya ja mota yai gaba, yana zuwa kofar gidan kuwa yai sa'a ba kowa a gun sai mai gadi, hakan yasa ya mai horn, mai gadi ya taso da sauri, Dan Litti ya kwama sunglasses tare da kallansa ya mikamai envelope din nan yace " kaga mai gidan." Mai gadi ya amsa yana kokarin tambayarsa inji wa, yaga Dan litti ya ja mota yai gaba. Cikin rashin kulawa ya koma ciki ya nufi ban garen Dady, Dady lokacin yana kishingide a falo abin duniya duk ya taru yamai yawa yaji kwankwasa kofa, nan yace a Shigo. Mai gadi ya shiga a hankali ya gaidashi tare da mikamai sakon, Dady yace " inji wa kenan?" Mai gadi ya dan sosa keya yace " wlh ni kaina ban sani ba." Dady ya sallameshi sannan ya bude wannan envelope din wata karamar Mp3 ce ta fado tare da yar karamai takarda. Fuskarsa dauke da mamaki ya sa earphone din a kunnensa tare da danna play. Kallo d'aya zakamai kasan yana cikin tsananin tashin hankali da jin abinda ake fada, mikewa yai tsaye cikin tashin hankali idanunsa suka kada sukai jaa, mamaki tare da firgice ne suka kamashi, takardar ya sunkuya ya dauka a kasa bayan ya gamajin sharhi daga bakin Alhaji Uba, address ne kawai rubuce a jiki na asibiti tare da number d'aki. Makullin mota kawai ya dauka ya fito da sauri tare da fadawa cikin motarsa, ya ja ta da gudu yai waje. Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin Nassarawa. Nan yabi address har zuwa inda ya isa number d'akin, jikinsa ne yai sanyi ya kasa bude dakin, ba shakka in har abinda yaji gaskiya ne shikam rayuwarsa ta kare, kenan ya zalinci Abbas akan hakkin da ba ruwansa, kenan duk yanda ya dauki Mansir ashe shi ne babban soko yana zaune ana amfani dashi. Dashi Mansir yai amfani yai achieving din duk abinda yakeso a duniya. Yana tsaye rike da kofar yaji an bude kofar daga ciki, wata nurse ce ta fito, kallansa tai ta gaisheshi sannan tai gaba. Kofar a bude take hakan yasa daga waje yana kallan Uba wanda ke kwance duk ya tsome, shikanshi Uban kallansa yake dan tabbas bazai iya manta fuskar Hisham ba. A hankali Hisham ya fara takawa zuwa ciki har ya isa kusa da gadon ya kalli Uba zaiyi magana Uba yai saurin katseshi da cewa " Hisham na gode da ka ziyarceni kafin rayuwata ta kare, ka yafemin abinda ya faru." Dady kallansa yai cikin wani yanayi yace " me nakeji game da Mansir....." Uba ya kamo hannunsa hakan yasa Dady ya zauna kusa dashi, Uba ya kara zayyanamai komai daya faru tare da doramai " nayi babban laifi, sai dai ba'a maida hannun agogo baya, Ka yafemin Hisham." Hankalin Dady yayi mugun tashi, ya mike jiki a sanyaye ba tare da yace komai ba yai waje. Tafiya yake kamar mara laka a jiki, har ya isa motarsa, ya shiga ciki ya zauna tare da dora kansa akan sityarin motar, me na aikata? Abinda zuciyarsa ke tambayarsa kenan, waya ya dauka dan kiran kanwarsa, sai dai a kashe ya jita, haka nan ya tada mota cikin karyewar zuciya yai gidansa. Yanzu kam ya gane komai daya faru dama trap ne da Mansir ya shirya. ********* Ashraf bayan ya ga Dady

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115