Skip to content

Chapter 113

Chapter 113

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,165 words 0 views Progress saved
Download Book

Cikin mamaki tace " amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?" Ya hade fuska yace " kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina." Nafi tai murmushi tace " amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?" Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace " kabarta ma da abinda takeji plx karka saketa." Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace " wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi." Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace " ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba." Kanta ta kwantar a bayansa tace" amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?" Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru. Dariya sosai tai tace " amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba." Ashraf yai dariya yace " nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shine yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura." Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace " amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka kuwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu." Ashraf yace " haka ne, amma bakya ganin ya kamata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?" Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace " karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida." Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar tsoron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya. Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kansa yace gidajenta za'a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba. Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da sauri, a kwance ta ganta a d'aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri. Little tace " Nafisa da wani ido zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?" Nafi ya rike hannayenta tace " Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?" Little hawaye na zubo mata tace " ta ya zakice ban aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?" Kai Nafi ta girgiza mata tace " karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara." Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta jata bangaren Mumy. Little na zuwa ta fada kanta tana kuka. Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi sosai ya tam sannan tace yaje yai wanka. Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare. ********** Da daddare Ashraf yana zaune ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace " yaya ya akai?" Yace " wai bazaki taho gun mijinki ba?" Tace " gun mijina?" Yace " da kina so kicemin a gun Little zaki kwana?" Tace " naga da acan nake kwana?" Yace "da kenan yanzu ai kayanki zaki tattaro ki dawo bangaren mijinki." Murmushi tai tace " ni dai kunya nake ji gaskiya." Yace " kunya ko? To ni bari nazo na daukeki." Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya tai tace " in zaka iya kenan ba." Ta koma suka cigaba da hira, batai minti 10 da zama ba suka ji sallamar Ashraf. Little tai kasa da kanta, shigowa yai ya zauna kusa da Little tare da dagota yace " kanwata ko neman Habib kike ne?" Dagowa tai da sauri tace "ni kuma?" Murmushi yai yace " to ni kike nema?" Kasa tai da kanta tana murmushi, Ashraf ya harari Nafi yace " malama tashi ko?" Nafi ta zaro ido ta kalli Mumy da Inna cikin tsananin mamaki, wai keke damun Ashraf? Abinda tafada kenan a ranta. Mumy tai murmushi tace " Ashraf bafa inda zataje." Kallan Mumy yai cikin mamaki. Mumy tace " Nafisa tana bukatar wani shagalin biki dan a kara shaida auranku, mutane dayawa basu san matarka bace, ita kanta kunya ya hanata sanar da kawayenta." Cikin tsantsan mamaki ya kalli Mumy yace " to ai...." Mumy ta hade rai tace " mun yanke hukunci da mahaifiyarta nan da sati d'aya za'ai ko yar walima ce sannan ta tare." Haushi ya kama Ashraf yace "har sati?" ya fada yana kallan Nafi. B'oyewa tai bayan Little tamai gwalo, haushi ya kamashi ya mike yace " hmm amma da ina tunanin gobe zamuje kauye tare da Inna dan ta nemi yafiyar Datti." Mumy tace " hakan yayi kyau, inyaso sai Little ta rakaku." Yace " amma mu biyu ma....." Mumy ta katseshi zan ma Habib magana shima kila zaiso yaje kauyen kaga sai kuje da armashin ku sai ku dauki babbar mota, gashi Afra nan ma xasuyi rakiya." Haushi ya kama Ashraf yai waje cikin takaici, bangarensa ya nufa ya kalli yanda ya tsara musu bangarensu yace " har wani sati? Sannan goben ma baza'a barmu mu biyu ba???" ********** Washegari haka suka shirya suka dauki mota babba, Little, Inna,Nafi, Afra da Amra, Dan Litti Habib da Ashraf suka nufi kauyen su Nafi. A hanya Ashraf yai musu siyayya sosai duk da Habib ne ya sashi dan shi gani yake bazai iya kaima Datti komai ba, haka suka isa kauyen A kauyen su Dan Litti suka fara sauka aka saukeshi mutane sai kallansu sukeyi, sannan suka wuce rigar Datti. Sun samu ba kowa a gidan gidan ma a rufe yake nan fa hankalinsu ya tashi sai ga wani yazo wucewa nan ya sanar dasu ai yana gidansu. Nan suka shiga mota suka gangara, Datti na kwance a karkashin bishiya shi kadai abin

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115