Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,156 words 0 views Progress saved
Download Book

yake jiki a sanyaye tace " Baffa naga jiyan dare yayi nasan kuma bazakaso inje rafi dadaddare ba. " " to yar gidan manyan mutane, kin rika sosai wato ina miki magana shine bakiji kunyar maidamin ba ko??" Duk maganar da sukeyi da yarensu sukeyi hakan yasa baisan me suke cewa ba amma tabbas ya fahimci abu daya masifa akema yarinyar, har kasan ransa yaji tausayinta masifa da sanyin safiyar nan? Nafi tai kasa dakai cikin hausarsa mara fita yace " Kin wuce ko kuwa? " Nan ta shigo ta dau kallabinta tai waje, yana kallan yanda take share kwalla dazata fita. Bokiti ta dauka cikin tsoro t nufi rafi, tayi sa'a gari ya fara haske, nan ta shiga debo ruwa sai datai sawu hud'u ta debo na karshen ne taje shiga gida taga maza carko carko a kofar gidan rike da sanda sunata masifa, cikin mamaki ta kallesu sai dai ganin yanda ransu yake a b'ace yasa ta shige gidan sukuku.... Tana juye ruwan ta shige daki dan da alama wad'annnan mutanen ba alheri ne ya kawo su ba, zama tai a kusa dashi tace " kasan me?" "Bansan me wasu maza sukazo yi ba amma da alama masifa sukazo yi, hmmm basusan halin Baffa bane. " Tad'an tab'e baki tace " ni kaina tsoronsa nake gani nake kamar ba shi ya haifen ba, mahaifiyata ma saboda masifarshi tsoronshi take, hmmm bansan ko su basa tsoron Baffan ba. " Dariya yake a cikin ransa lalai wannan akwai surutu. Jitai an fasa abu yasa ta mik'e da sauri tai waje, yabi bayanta dakallo tareda yin dariya lalai wannan yarinyar ga hausartata mai abin dariya. Tana fita taga mutanen nan ne suka fasa musu randa, ga mamakinta Baffa na zaune a gefe yana kallansu, wani daga cikinsu yace " wallahi kaji na fad'ama Datti ka bani kud'ina tun kafin rai ya b'aci. " Baffa ya juya kai yana murmushi yace " Nina rantar muku kud'i? " Mutumin yace " bakai bane amma ai matarka ce tace injika. " Yasa dariya yace " Matata? Wa kenan? " Haushi ya kara kamasu, Nafi dake tsaye jikin kofa ta matso kadan, ai kuwa Mutumin na ganinta ya matso tare da rike hannunta yace " Uwar wannan yarinyar." Baffa yai dariya yace "Ali kasan Allah ficikata bazatai ciwo ba dan ba ninace ka bata uban kudi ba, banda sacemin saniya datai har kake tunanin zan kara kashe mata wani kud? " Wanda ya kira da Ali shine ya matso a shekaru ya girmi baffa sai dai bai tsufa ba, yace " Datti wlh in har ka cigaba da batan rai to kuwa zan dauki wannan 'yar taka amaimakon kud'ina ne.? Baffa ya bugamai wani kallo, Nafi wanda tsananin tsoro ya kamata ta kalli Baffa hawaye suka fara zubo mata. Baffa ya juyar da kai. Ali yace " Aradun Allah ko ka biyani kud'ina ko kuma a yau d'innan insa a auramin 'yarka sai ka zab'a. Dan binni dake tsaye yana jinsu ya mike cikin tsananin mamaki kasancewar da hausa suke maganar yasa ya fahimta, ya kula su masu masifar kamar hausawa ne, meke faruwa? Muryar Nafi ce ta katseshi tana kuka tana cewa " Baffa dan Allah ka taimakeni kaji? " Baffa ya kallesu kallan wulakanci yace " kuna tunanin saboda 'yata sai in sadaukar da dukiyata? " Ya sa dariya yace " Dama na gaji da ita, in kanaso yanzu ma sai in aurama ita menene a ciki? " Ba Nafi ba ba kuma Dan binni ba hatta 'yan ansan bashi sai da tsananin mamaki ya kamasu, Nafi ta kalli Mahaifinta cikin tsananin mamaki sam tama kasa magana banda rawa da jikinta ya shigayi. Baffa yai tsaki yace " Zancen banza kenan. " Ali ya kalli mutanen gun yace " kowa yaji abinda Datti yace ko? " Duk suka amsa da eh, Ali yace dan haka anjima da azahar zamu dawo a bakin nan za'a daura aure lalai zanga karyar iskaninka Datti. " Suna kainan suka saki Nafi suka juya. Nafi kam haf yanzu jikinta rawa yake, baffa ya kalleta yace " ke menene damuwarki? Ali fa nada kudi da dabobbi sannan matansa uku sai 'ya'ya guda sha shida kinga gwara ki aureshi can ki xauna cikin mutane ko kyafiyin hankali. " Yana kainan ya juya yai waje. Dan binni yai tsuru yana kallan ikon Allah wace irin zuciya ce da wannan mutumin? Bakomai a ransa sai dukiyarsa? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 4⃣ D'akinta ta shiga tana tafe tana layi, shikam yana jin motsinta yai saurin kwanciya dan ya tabbata bazataso wani yaji wannan mumunan abun ba, Nafi na shiga ta karasa kusa dashi ta zauna hawaye ne kawai ke malala a idanunta, can tasa hannu ta goge sannan ta kalleshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace "Dan binni yazanyi da ke? Gashi baki farfad'o ba bare ki bar wannan gidan mai cike da abin takaici dasan zuciya. " Zuciyarshi ce ta karye da mamakin tana cikin wannan halin amma tausayinsa take? Wannan wace irin yarinya ce wacce zuciyarta take da tsananin kyau? Nafi ta kara sa hannunta ta goge hawayenta sannan ta cigaba " Dan Binni ina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, Mahaifina baisan komai ba sai dukiyarsa baya ganin mutunci ko darajar kowa banda ta dukiyarsa, mahaifiyata kuma san kanta ya mata yawa haka na taso a cikin irin iyayen nan, ba wanda ya damu da halin da nake ciki ko wanda zan shiga, a dazu nafijin haushin Baffa akan kin biyan bashin dayai sannan bai damu da in auri sa'ansa ba wanda a cikin 'ya'yansa akwai wad'anda suka girmeni ba. " Tai ajiyar zuciya sannan ta cigaba " yanzu kuwa nafijin haushin Inna ta, tafi kowa sannin halin Baffa amma duk da haka taje ta ranci kud'i da sunansa, ni kuma da ko naira biyar bangani ba bashi na neman............ " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasawa, mikewa tai tsaye tace "bari in samoma madara kasha nasan yunwa kake ji." Tana fita ya bud'e idanunsa ga mamakinsa jiyai gaba daya jikinsa yayi wani mugun sanyi, meyasa mutane basuda imani? Yanzu me wannan yarinyar tayi da hakan ke faruwa da ita? Shiru yai yana tunanin meya kamata yai dan cetan rayuwarta? Bata dade ba ta shigo dauke da kwarya karami da chokali, nan ta dagoshi kadan ta shiga bashi, mamaki tayi dan kuwa yau madarar bata zubewa sai dai batai tunanin komai ba. Shikam sha kawai yake gardin madarar ce kesashi sha sai dai rashin sigari yasa madarar batamai armashi sosai ba. Ganin yadansha dayawa yasa ta gyaramai kwanciya sannan ta mike tai waje. A can bangaren Datti kuwa yatafi rigar Mahaifinsa nan ya shiga suka gaisa da iyayensa da 'yan uwansa ya kuma sanar dasu auren Nafi wanda za'a daura anjima, tsananin mamaki ne ya kama Iyayensa da yayensa, mahaifinsa wanda ya tsufa sosai ya kalleshi yace " yanzu Datti za'ai auren Nahi shine sai ranar auren zaka sanar damu? " Datti cikin halin ko in kula yace " to Kawo menene aciki nima sai yau naji zancen auren. " Gaba daya suka kalleshi cikin tsananin mamakin kalamansa, Aji mahaifiyarsa tace " Datti me kake san kace? " Ya

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115