Chapter 55
Chapter 55
Suzo tare amma ba magana sai kawai yai gaba ya barta, so yake ya nunama kowa bashida hadi da ita ko me? Jitai ance " in bazaki jeba shiga mota in maidake gida ko ki hau adaidaita ki tafi, kina tunanin banda abinyi ne?" Ta juyo ta kalleshi yana tsaye ya had'e fuska sosai, d'azu ta tuno sanda ya sakar mata fuska wannan wani irin mutum ne?" Ran Ashraf ya kara b'aci ganin wayar a hannunta, ta d'aure tace " yaya kasan ban taba zuwa ba amma kana ajiyeni kai gaba kabar ni, ya kakeso inyi?" Ranshi ya sake b'aci yace " bakida kafa ne ko kuwa jaririya ce ke?" Nafi ma cikin b'acin rai tace " duk da ni ba d'aya daga cikin abinda ka lissafa bace amma ai nima inasan kulawa, taya zamu taho tare ace kana can gaba ni kuma ina can baya?" Ashraf ya kalleta zaiyi magana yaji tace " so kake ka nunama kowa bakada alaka dani?na sani kafi karfin ajina balle har ka jera dani sai dai na rasa me yasa nakeji zafin hakan aduk lokacin da kamin, nasan da hakan har kasan zuciya ta to why nakejin zafi?" Ta fad'a tare da juyawa tana neman maida kwallarta, jikinsa ne yai sanyi sam matsalarshi kenan bayasan yaga ya sa mace kuka, kallanta yai sannan yace " zaki iya tahowa yanzu?" Kallansa tai sannan ta fara takawa a hankali, Yana gaba kad'an tana binshi a baya, har suka isa cikin shop right nan ya nuna mata babban cart ita kuma ta jawo suka fara zagawa, ita take nunamai abin bukatar makaranta inta sa d'aya sai ya kara biyu a ciki su zama uku, haka suka sai kaya sosai, ita har tsoro take nawa za ace musu in akazo gun biyan kud'i? Bai bari taji ba ana fad'an nawa ne yai saurin mika Atm card dinsa nam aka cira sannan akasa wani ya kai musu mota. Suna fitowa sukaga gari ya turnuke sosai, nan sukai sauri suka shiga mota, ko fita daga mall din basuyi ba aka fara yayyafi, kafin kace me? Ruwa ya tsuge sosai ruwa mai karfin gaske wanda ko gaban mutum baka gani. Nan Ashraf ya gangara gefen titi yai parking, sunyi shiru sai kallan yanda ruwa yake sauka kawai sukeyi, Nafi batai auni ba taji muryar Ashraf cikin sanyi yace " karki sake cemin nafi karfinki wai ko na tafi saboda bazan iya jera wa dake ba." Kallansa tai cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa ya juyo shima ya kalleta, ganin yanda take kallansa yasa yaji wani abu na ratsamai jiki, kansa ya d'auke da sauri, ya had'e rai sosai, Nafi ta matso sannan tace " Yaya ni..." Wayarta ce ta sake katseta ya juyo ya kalleta tare da kallan wayar, number d'azu ce, ta kalleshi cikin tsoro kafada ya d'aga mata sannan ya mata alama akan ta amsa wayarta. Jiki a sanyaye Nafi ta d'aga tare da sallama, Alamin yai ajiyar zuciya yace " At last kin d'au wayata." Nafi idanunta nakan Ashraf tace " sry d'azun ma wani abu nakeyi." Ashraf kam wayarsa ce a hannunsa yana dannawa sai dai hankalinsa na kan wayar da take. Alamin ya saki murmushi sannan yace " Feenah plz ki daina jamin rai wlh zuciyata zata iya kamuwa da ciwo in har baki tausaya kin amince da ita ba." Har yanzu idanta nakan Ashraf sai dai jin kalaman Alamin sun sa ta d'an sassauta murya kamar mai rad'a tace " Alamin ya kake so inyi wai?" Yace " ki amince dani na zama saurayinki ni kadai." Tace " bangane ka zama saurayina kai kadai ba??" Ashraf ne ya juyo ya buga mata wani mugun kallo wanda batasan sanda ta sauke wayar ba daga kunnenta hannubya bata akan ta bashi wayar ba musu kuwa ta mikamai ya sa hannu ya amsa tare da kashe wayar gaba d'aya, mamaki ya kamata a ranta tace ko kishin ne?? Jitai yace " ku mata wani sa'in me yasa bakuda tunani ne?" Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace name fa? Ya kalli wayar yace " ke kina ganin burgewa ne saurayi yaba budurwa waya ba wata magana mai karfi a kasa?" Nafi ta turo baki batare da ta amsa ba, yace darajarta take ragewa agunsa alama kuke nunawa na abin hannunsa kuke so. Nafi cikin takaici tace " ai ba ni nace ya bani ba sannan magana mai karfi ai za'ayita in na gama makaranta." Dariya taga yayi sannan taji yace " kin manta me nace miki kenan ko? Randa zakizo garin nan." Kallan mamaki tamai yace " cewa nai sai na yarda da yaron sannan zan baki takardarki." Kallan sa tai sai dai zuciyarta taji ba dadi haryanzu wato yana tunanin bata takarda ko?????? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *45* Ranta yakai koluluwa gun b'aci Ashraf bai tsamani ba kawai yaga ta bud'e motar ta fita, ga ruwa ake sosai, da sauri shima ya bud'e kofa ya fita, tafiya kawai take tsabar ruwa batama san ina take sa kafarta ba, Ashraf ya hanzarta ya riko hannunta. Kallansa tai sannan ta fizge hannunta da karfe ta nemi ci gaba da tafiya, hannayensa biyu yasa ya rike kafad'arta ya juyo da ita saitinsa yace " Nafisa!!" ya fad'a tare da jijiga mata kafad'a, Nafi ta shiga neman kwace jikinta ganin yanda ruwa ke dukansu gashi da alama taurin kai take nemanyi yasa kawai ya d'agata cak yai mota da ita ahakan ma saj wutsul wutsul take, ya bud'e mota ya sata sannan ya zaga da sauri ya shiga tare da sama motar lock. Nafi ta juya kanta gefe, hannunta ya kamo yace " menene wai?kanki d'aya kuwa?" Ta kalleshi da idanunta da suka ciciko cikin wani irin murya ta kalleshi tare da cewa " yaya ni nace ka aureni?" Kallan mamaki ya mata, ta share hawayenta duk da tasan abanza dan kuwa hawayen sai ma kara zubowa takeyi, ta kalleshi sannan ta cigaba " Yaya ni bw mutum bace?dutse ce ni ko kuwa?" Kallanta kawai yake sam ya kasa magana, hawayen da takeyi da kalamanta sune kawai ke ratsa shi, ta kara share wasu kwallan sannan ta cigaba " ka tab'a ganin inda mace a ranar da aka daura mata aure miji yake mata zancen saki? Ka taba tunanin yanda wannan matar zataji duk da yarintar dake damunta a lokacin??" Ashraf jikinsa ya mutu sosai, Nafi ta sake goge kwallar sannan tace " ka bani takarda ta yanzu inaji shine kawai abinda ya kamata, a gun iyaye da mutanen garinmu ne kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad'a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?" Ashraf ya kara rike hannunta yace " Nafisa!" Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace " na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawara ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata." Idanu Ashraf ya runtse sannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115