Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,154 words 0 views Progress saved
Download Book

" Little wa aka saima kayan nan? " Little ta kalleta rai b'ace tace " Ya Neesa me ya dameki da wanda aka saiwa? " Aneesa ranta ya b'aci ga kawarta a zaune a kusa da ita, tace " mene?" Little a zuciye ta karaso tace " Ya Neesa wai meke damunki ne? Taya zakiga kayan mutane kawai ki zubar a kasa? " Kawar Aneesa ta kalli Little tace " lalai Little yaushe kika zama mara kunya haka? Aneesa ba yayarki bace? Sannan yanzu da kika ganni anan tsara shirye shiryen da za'ai da bikinta da yayanki mukeyi ai ko bata zama matarsa ba ai yayarki ce bare an kusa. " Little ta kalleta a kule sai dai ta kasa magana ta kalli Nafi cikin takaici ta wani takure kanta a kasa zatai magana kawai sukaji ance "Tsugunna ki kwashe kayan da kika zubar. " Gaban Aneesa ne ya fad'i ta juyo a tsorace, ba ita ba Little da Nafi ma kofa suka kalla haka ma kawar. Ashraf ne a tsaya kana ganinsa kasan ba wasa a fuskarsa, Little ta kalli Habib wanda ke tsaye daga kofa, a ranta tace " yaushe ya kira shi? " Aneesa ta kalleshi tace " Yaya.... " Wani kallo ya mata wanda yasa ta had'iye maganar ta cikin tsawa wacce ta razana kowa dake falon yace " Kowa ya fita." Nafi kam jikinta rawa ya kauri dashi, bata tabajin yayi tsawa haka ba, Little ta kamata sukai waje a sukwane itama kawar Aneesa da sauri tai waje ta nufi d'akin Umman Aneesa. Ya rage daga Aneesa sai Ashraf a d'akin, ya kara kallanta yace " ba dake nake ba? " Idanunta na kansa kallan mamakin dizgata dayai take, ta daure tace " Yaya ni zaka wulakanta akan Nafi? " Shi baimasan a hannun Nafi aka anshi kayanba, shidai Habib yace yazo akwai matsala a b'angaren su Little, da ya iso shine yake cemai Mumy ta siyo kaya Aneesa ta zubar. Ashraf ya kara kallanta, idanunta suka ciciko tace " Yaya kana san ka nunamin ka fifita Nafi akaina kenan ko me? " Ashraf ya kalleta cikin tsananin takaici zaiyi magana kawai sai ga Asim da Umma sun shigo cikin masifa........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* *25* Nafi wacce little ke janta akan su tafi b'angaren Mumy tana ganin Umma da Aslam sunyi b'angarensu a fusace yasa ta turje tare da kallan Little tace " Maryam wannan abun duk laifinane, kina ganin abun nan yana neman ya zama babba? Sannan ni kuma in gudu?" Little ta tsaya itama tare da cewa " Laifinki? Ta ina ya zama laifinki?" " laifinane mana tunda dai a hununa aka amshi kayan." Haushi ya kama Little ta rasa Nafi wace irin yarinya ce, ta kalleta tare da dafata tace " Naji a kaddara laifinki ne mai zakiyi in kika koma?" " Hakuri zan bada mana kina ganin su Umma sun tafi nasan kowa laifin yaya zai gani." Ta karasa maganar cikin rawar murya. Little ta kalleta sai dai ta rasa me ma zata ce mata, gani tai Nafi ta fara tafiya nan ta bita tana mata magiya akan su tafi sai dai itakam gani take gwara taje kawai. A falo kuwa Ashraf ne ya had'e rai kamar zai dake Aneesa ita kuma tana tsaye kyam kusa da kaya, ta kalleshi tace " Yaya nice fa?" Ya buga mata wani kallo yace " kece wa? Ko dama a duniya akwai wanda ya isa inyayi ba daidai ba a kasa hukuntashi?" Daga bayansa yaji ance kwarai kuwa, Asim ne yai maganar ya sani shiyasa kuma bai juya ba, Asim ya karaso rai b'ace sannan ya sa hannunsa ta bayan Ashraf iya karfinsa da niyar kai mai duka, Umma tai saurin rike hannun tare da balamai hararra. Ashraf ya kalli Aneesa yace " idan kika bari na irga uku acikin raina wlh sai kinyi dana sanin wannan ranar." Umma tai charaf tace " ai kuwa sai dai tayi dana sanin dan kaf duniya ba wanda ya isa ya sa 'yata ta kwashi kayan wannan yar kauyen." Ashraf bai kalli Umma ba haka kuma bai bata amsa ba sai Aneesa da yake kallo yace " kin amince da abinda aka ce?" Aneesa ta goge kwallarta tace " yaya me zakayi in na ki kwashewa? Badai cewa zakai ka fasa aurena akan wannan shirman ba?" Ashraf ya saki wani mugun murmushi yace " me? Kina ganin bazan iya ba?" Kallan mamaki sukamai su duka ukun, Aneesa wacce duk ta gama rikicewa tace " Ya Ashraf me kake fada haka?" Ya kalleta yace " in kina tunanin bazan iya ba ki bar kayan nan har na karasa bakin kofa, ni kuma zan nuna miki magana d'aya nakeyi." Nan ya juya Aneesa ko kara wata maganar batai ba ta shiga saurin kwashe kaya kamar zata kifa kansu, Ashraf kam ko a jikinsa ya wuce ta jikin Asim ba tare da ko kallan su yayi ba, bai kuma kara duba Aneesa ba dan yasan tabbas zata kwashe kayan nan. Ana kai kofa, Nafi wacce ke tsaye jikinta sai rawa yake ta kalleshi a tsorace, bai kulata ba yai wucewarsa, Little ta dafa Nafi tace " Nafi jikinki rawa yake." Juyowa Nafi tai cikin tsananin tsoro tace " Maryam wani irin mutum ne yayanki? Da gaske sai ya raba auren nan a dalilin da baikai ya kawo ba?" Little tai shiru dan itama abin ya bata tsoro, Nafi ganin haka yasa ta girgiza kai tace " Maryam yayanki na bani tsoro dan ko Baffa banajin tsoronsa kamar yanda nake jin na yayanki." Little ta dafata tace " yayana yaga rayuwa wanda itace ta maidashi haka, baya tausayin kowa ba kuma ya shakkar kowa, abu d'aya ya tsana kuka bayan wannan banaji akwai abinda ke tab'a mai rai." Nafi tabi bayan inda Ashraf yabi da kallo, ace wacce zaka aura kuma kake so ita zaka dizga haka agaban iyayenta da yayanta? Kuma ya juya ya fita kamar ba abinda ya faru? Little ce ta katseta da cewa "Nafi ina zuwa."ta juya da sauri. A falo kam Aneesa tana ganin fitarsa bayan ta gama kwashe kayan ta tsugunna agun tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, Umma ta karaso kusa da ita jikinta itama a sanyaye ta jawota jikinta. Kuka sosai Aneesa takeyi, Asim ya kalli Umma cikin takaici yace " Umma haka zamu zauna yaron nan yqna ci mana mutunci?" Umma ta kalli Aneesa tace " da kinsani baki kwashe ba inga ta karyar iskanci." Aneesa ta mike daga jikin Umma tace " Umma kamar bakisan Ashraf ba? Kin manta abinda ya faru shekarun baya da suka wuce? Kina sane da ciwon danai tayi a lokacin dayace bazai aureni ba, ya kuma daina kulani." Umma tai shiru, Aneesa cikin kuka tace" alokacin bansan ciwon kaina sosai ba, kina tunanin inya fasa aurena yanzu zan iya rayuwa?" Asim a kule yace " Dalla yima mutane shiru, sai ki kasa rayuwa dan an rabaki da Ashraf?" Aneesa ta harareshi sannan ta mike cikin fushi tana kuka tace " kana tunanin in Ashraf bai aureni ba zai barka a matsayin da kake ne? " Asim yai shiru, Umma tace " ya isa,

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115