Chapter 91
Chapter 91
taga Mumy ta mike tayi waje, ta bita da kallon tausayi. Ta dade a zaune agun kafin ta d'au wayarta ta kira Ashraf, sai dai duk yanda wayar ke ringing bai d'auka ba. Ta ajiye wayar tare da kwantar da kanta jikin kujera. *********** A b'angaren Ashraf kuwa yana azahar ya wuce gidan Uncle bayan sun zauna a falo sun gaisa Ashraf ya kalli Salim yace " Uncle a labarin da ka bani kwanaki banaji kacemin an anso kayan su Dady." Salim yai shiru yana kallan Ashraf. Ashraf ya cigaba " nasan asibiti da makarantar sa na Abba ne amma bansan gidajen hayansa nawaye ba." Salim ya shafi fuskarsa da hannayensa yace " Ashraf you are very smart,ban taba tunanin zakai zargin wani abu ba game da wannan, shiyasa ma ban sanar dakai komai ba." Ashraf ya kalli Uncle yace " me ke faruwa?" Salim yaja numfashi yace " a lokacin da mahaifin Ruma ya rasu bayan an gama zaman makoki Hisham ya shiga gararin rayuwa, kaf kudinsa sun kare bayan rashin kudin ashe har loan yaci a banki wanda ya jinginar da gidansa. Bayan an gama zaman makoki 'yan bankin sukazo amsar kudinsu kamar yanda ya sanar dasu lokacin dazai biyasu. Sai dai a lokacin gidansa abincin ma dazasuci nema yake ya gagaresu. Da yake Ruma na gidan ita ta kira Abbas ta sanar dashi halin da ake ciki nan ya je bankin ya biyasu kudinsu sannan makarantar da yake masifar so ya mallakama Hisham duk dan ya farantamasa, sai dai kwanansa d'aya da bashi makarantar Allah ya d'auki ran Abbas." Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " asibitin fa?" Salim yai ajiyar zuciya yace " Ashraf wannan sai bayan rasuwar mahaifinka sukazo min da takarda akan Abbas ya mallakama Hisham asibitinsa da aka gama ginawa ko fara aiki ma ba'ai ba." Ashraf cikin rashin fahimta yace " ta yaya ya bashi makaranta mai girma irin wannan ya sai mai gida sannan ya kuma bashi asibiti?" Salim ya kalli Ashraf yace " nima da naki yarda da bada takardun asibitin to amma abin mamaki rubutun mahaifinka ne." Cikin fada Ashraf yace " zasu iya sa expert su kwaikwaya ai." Salim yace " yes shiyasa naki yarda sai dai mahaifiyarka itace tace tabbas Abbas ne ya rubuta." Shiru Ashraf yai kafin yace " gidajensa fa?" Salim yace " bansan wannan ba gaskiya sai dai bayan mutuwar Abbas naji jita jita akan bai daina safarar bindigogi ba zai iya yiwuwa da su ya siya ko kuma gadon Ruma ne." Cikin mamaki Ashraf yace " gadon Mumy?" Salim yace " ban tabbatar ba amma tunda kace gidaje dayawa nasan tanadasu dan Abbas tun yana da rai yake siyan gida da sunanta sannan da ya rasu aka bata gadon wasu." Ashraf yai shiru baice komai ba, Salim ya dafashi yace " Ashraf mahaifinka burinshi kai rayuwa mai dadi ba wai ta wahala da kunci haka ba." Murmushi Ashraf yai yace " Uncle kana tunanin zanyi rayuwa mai dadi bayan duk 'yan uwana makiyan Abba da ni suna zagaye da ni?" Salim baice komai ba sai kallan Ashraf dayake yi. Ashraf ya sake murmushi yace " ka binciko min inda Auwal Max din yake?" Salim yace " eh to wanda yake binciken yace yana zariya sai dai yace in kara mai 1day ya tabbatar da shi din ne." Kai Ashraf ya jinjina sannan ya mike yace " kace kafin Abba ya rubutawa matata wasiya munyi tafiya zuwa wani kauye dashi ko?" Salim ya jinjina kai yace " kwarai kuwa saboda bazan manta lokacin ba nayi mamaki kwarai daya kawon wasiyyar da daddare." Ashraf yace " Malam Mahmud ko?" Salim ya daga kai alamar eh. Ashraf yai godiya kafin yai waje. Mota ya fad'a ya d'aga wayarsa sakon Nafi ne yaga ya shigo kamar haka " _Yaya dafatan kaci abinci?_" Ya dade yana kallan sakon kafin ya ajiye wayar ba tare da ya mata reply ba. Makaranta ya wuce, yai sa'a kuwa yana zuwa Malam na kokarin fita, nan ya ajiye mota ya karasa suka gaisa, Malam yai murmushi yace " Muhammad daga ina haka?" Ashraf yai murmushi yace " gaisawa nazo muyi." Malam yai dariya yace " nagode da baka manta da wannan tsohon ba." Nan sukai dariya, Malam yace " Ina Matar taka?" Ashraf yace " tana nan." Malam yace " yarinyar fa nake nufi." Ashraf yadan sosa keya. Malam yai murmushi yace " da alama tana nan." Ashraf ya kalleshi yace " malam tambaya nazo da ita." Malam yace " Allah g yasa na sani." Ashraf ya nisa sannan yace " kafin Abba ya rasu munyi tafiya ni da kai da shi ko?" Malam yace " Hakkun." Ashraf yace " Malam zaka iya tuna abinda ya faru a lokacin?" Malam yai murmushi yace " shekarun da yawa na dai san munje zagaye da taimakon bayin Allah dake da bukata, wannan shine tafiyarsa ta karshe." Ashraf ya jinjina kai yace " ba wani abu na mamaki da ya faru game da ni?" Malam yai shiru kafin yace " tabbas akwai na tuna, abinda ya dade yana bani mamaki." Ashraf ya kalleshi cikin zakuwa da sanjin menene. Malam yace " mu shiga ciki." Nan suka nufi makarantar. ********** Yau Datti yana tsakiyar bacci ya tashi cikin firgice tare da kwallama Nafi kira, sai kuma ya saki wani irin kuka mai ban tausayi. Yayansa ya shigo d'akin a tsorace ganin tsakar dare ne gashi ya tashi mutane da dama. Datti yana kuka yana cewa " a kiramin Nafi dan Allah ku taimaken ku kiramin Nafi." Yayansa ya shiga lalabashi yana cewa kai shiru Datti da alama ka samu lafiya tunda ka fara magana. Sai dai ina Datti kam abin ya canza salo daga kuka sai a kira masa Nafi kawai yake cewa. Nan suka shiga tambayarsa a wani gari Nafin take a kirata?" Kai kawai ya girgixawa alamar bai sani ba. Mamaki da tsoro ya kamasu. Mahaifiyarsa dake kwance ba lafiya tace "kila saidata yai saboda tsabar san kudinsa nikam na shiga uku na." Datti kam cewa yake a kira masa Nafi...... Nace ta yaya kenan?🤔 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *72* Bayan sun zauna Malam ya kalli Ashraf wanda ya nutsu yana kallansa. Ashraf ganin Malam na kallansa baice komai ba yace " Malam ya akai?" Malam yai murmushi yace " tunowa nai lokacin da mukai wannan tafiyae bakafi dan haka ba " ya fada yana gwada tsayin Ashraf a lokacin. Ashraf yai kasa dakai yana murmushi. Malam yace " A wannan rana munje kauyuka da dama na kusa da na nesa, a karshe muka isa wani gungurmin kauye, wanda 'yan garin kana ganinsu kasan suna cikin tsananin wuya da talauci, nan muka isa gun mai garin aka tara 'yan garin aka fara basu sadaka, kaima kana mikawa. Gun yayi cunkoso wanda ya janyo turereniya agun, wasu suka dinga faduwa saboda karfin da kowa yake gwadawa. Ganinka mukai kabar gun rabon da dan gudunka. Nan Abbas ya leka ya ganka gaban wani bawan Allah, tsoho ne tukuf gaba d'aya gashin kansa fari ne ya tsufa sosai, wanda aka tureshi garin rigima ya fadi kasa. Da saurinka ka karasa kana neman d'aga mutumin,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115