Chapter 44
Chapter 44
sannan ya kalli window yace " inba abu kikesan fad'amin ba me zai sa kizo b'angarena kinsan inada mata kizo ki tsaya a waje?" Baki ta tab'e a ranta tace " da cewa nai bakada mata?" Ya kalleta sannan taji yace " da alama kin manta inada mata inba haka ba mezai sa kije b'angaren? Ai sai ki kirani a wayar Little ko ta saurayinki." Nafi ta saki baki tana kallan sa tace " to ni menace?" Ya juya kai sannan yace " Ki tambayi abinda kika ce a zuciyarki." Nafi tai shiru rai b'ace. Ashraf yace " to fad'amin? Menene?" Nafi tai shiru tare da maida kanta kasa. Ashraf ya kara had'e rai yace "zan saukeki fa inja motata inyi gaba ko ce miki akai banda abinyi??" Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, cikin wani irin murya tace "banifa da lafiya, xaka saukeni." Wani murmushi ya saki na rainin hankali yace " harda karya kika koyo a makarantar? " Ta kalleshi sannan ta d'an shagwab'e murya tace " nifa Yaya ba karyar dana koyo." Har cikin ransa sai dayaji wani abu, sai dai ya sake dakewa yace " ke jiranki nakeyi ko?" Nafi ta kalleshi tace " Yaya dan Allah kar kaje gun aiki yau." Kallan mamaki ya mata yace " bangane ba? Ke harkinkai matsayin da zaki hanani abu?to ko Aneesa bata samu wannan matsayin ba." Nafi ta kalleshi cikin wani yanayi tace " Na sani Yaya banida wannan matsayin kuma ban kai kaina wannan gun ba, sai dai ba dan nibaaa ba kuma dan halina ba sai dai ka duba darajar Allah ka hakura da zuwa aikin nan yau." Ta karasa magana tare da kawar da kanta alamar idanunta nasan kawo kwalla, kallan mamaki yake mata, sai dai yanzu yasan tabbas da wani abun....... *THE INNOCENT TEAM* 🏌🏻 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *35*} Yanda yake kallanta yasa ta had'e rai tare da maida kallanta wajen window, itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma 'yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata tsauri. Ga mamakinta jitai yace " tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida." Nafi ta kalleshi a tsorace tace " Sauka zanyi a haka??" Kai ya d'aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace " taya zan iya fita ahaka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud'in da zan tafi da kaina." Ya d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b'aci a zuciye ta matsa da niyyar bud'e kofa, har ta zura kafa d'aya zata fita sai taji yace " shigo in ajiyeki ba dan halinki ba inada abinyi." Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud'e kofa zata fita sai kuma ta juyo tace " Yaya ina zaka?" Kallanta yai yace " banaji wannan yana d'aya daga cikin damuwarki tunda dai baki fad'amin me kike nufi da kar inje aiki ba, kin kuma san halina ba a sani abu." Nafi ta kalleshi cikin kulawa tace " Yaya tunda kaga na furta hakan ai kasan da dalili, in ba haka ba meye nawa da zance karkaje aikinka?ni ba matarka ba?" Juyowa yai ya kalleta kalamanta na karshe sun tsayamai a wuya, sai dai ya share yace " ke nake jira zan fita ko?" Nafi batasan sanda wani takaici ya kamata ba ta kafeshi da ido na takaici, kallanta yai sannan ya juya ya d'au wayarsa, bakin ciki ya hanata d'auke idanunsa daga kansa jitai ya tada mota, alamar zan tafi, takaici yasata ta fito daga motar a zuciye tana kallo yaja motarsa ya tafi, tabi motar da kallan takaici. Wannan wani irin mutum ne, duk yanda na damu da rayuwarsa amma shi ko a jikinsa?? Sai ma rashin mutunci ne zai biyo baya?. Sam ta kasa d'auke idanunta daga hanyar daya wuce, jitai an dafa ta a firgice ta juyo, Mumy ta gani tsaye itada Little. Nafi tai saurin share kwallarta sannan ta kakaro murmushi tace " Mumy ina kwana???" tafad'a tare da risinawa, mumy ta amsa sannan tace " Nafi me kike yi anan? Little duk ta damu tanata nemanki?" Nafi ta kalli Little sannan tai murmushi tace " Ayya My Sisto tuba nake." Little ta harareta sannan ta juya tai b'angarensu, Mumy ta kalli Nafi databi bayan Little da kallo tace " Nafisa ina kika je???" Nafi tai kasa dakai, Mumy tai murmushi sannan tace " shikenan, kije gun 'yar uwar taki dan hankalinta ya tashi." Nafi ta d'aga kai sannan tai bayan Little da sauri. A tsaye ta ga Little ta cire kaya daga ita sai towel da alama wanka zata shiga, Nafi ta karasa gunta ta zauna akan gado tana kallan Little wacce ta had'e rai. Nafi tai murmushi tace " Little bazaki kulani ba?" Little ta juya tai hanyar toilet, tanaji Nafi ta kara cewa " My Sisto tuba nake kinji kiyi hakuri." Little ta wuce toilet ba tare da ta amsa mata ba, nan Nafi ta mik'e ta gyara d'akinsu ta gama shara kenan Little ta fito, Nafi ta kalleta zatai magana taji Little tace " ki je kiyi wanka Yusra tun d'azu take kira wai dan Allah muje yanzu." Nafi ta mike ta karaso gun Little ta rungumeta tare da cewa " Little wlh wani abu ne ya taso min dayai gaba da duk tunanina." Little tace " Shikenan Feena ni kin barni anan cikin tsoro tunda na tashi naga banganki ba na kuma fita kaf na zaga ban ganki ba." Nafi tace " Sry nayi laifi." Murmushi sukama junansu, nan Nafi ta saketa sannan itama tasa nata towel d'in ta nufi toilet, har taje zata bud'e kofar ta juyo tace " Little nikam a iya sanina ba wata matsala dake tsakanin Mumy da Umma ko?" Little ta kalli Nafi tace " Feena kenan, a haka dai kamar babu, sai dai inaji a jikina kamar da wani abu." Nafi ta kalleta tace " kamar me??" Little ta d'an tab'e baki tace " kinsan a duniya in har akace kud'i to fa an gama komai, kud'i da kike ganinsu sune matsalolin komai na rayuwar duniyar nan, duk wata matsala inka dubashi daga kasa to fa lalai zakiga kud'i shine silar komai." Nafi ta shiru tana mamaki, can tace " Amma dai nan banaji za'ai fad'a akan kud'i ko? tunda dai naga kowa yanada shi." Little ta furzar da iska sannan tace " Feena kenan ai a gidan da ake da kud'in anfi samun matsala akan kud'in tun balle in dukiyar da mai ita." Nafi ta mata kallan mamaki, Little tai murmushi sannan tace " share kawai." Jiki a sanyaye Nafi ta shiga wanka, sam wanka take amma tanata nanata kalaman Little dukiyar da mai ita? Kawu kenan? To in shine meye na neman kashe Ya Ashraf?" Ta dad'e kafin ta fito, tana fitowa taga Little ta ciro musu dinkin Less anko ne shima, Nafi ta zauna itama ta fara shafe shafe. A b'angaren Ashraf kuwa yana fita daga gidan ya nufi gidan abokin babansa ko ince
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115