Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,146 words 0 views Progress saved
Download Book

da makullin. Yanaji sanda ta d'an zabura kad'an shi dariya ma taso bashi, ta d'ago tare da kafeshi da ido, mamaki ne ya kamata ganin hankalinsa ma baya kanta. Idanunta na kansa sam ta kasa d'aukewa, jitai yace " kallan bai isa ba? " Da sauri tai kasa da kanta, yace " ba jiranki ake ba? " Kallansa tai da mamaki taya za'ai ta tafi bayan ya rike hannunta? Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " So kike kuyi dare ko da wani abin da zaki fad'amin? " Nafi ta d'an yi rau rau da ido tace " Yaya Hanuna fa? " Yanda tai maganar ita kanta batasan ta iya ba, ya kalleta sannan ya kalli hannun, sakin hannun ta yai tare da zare makullin, ya kalleta yace "zan ajiye in ko in dawo sai kizo ki amsa. " Ta kalleshi da mamakin kalamansa, ta daure kawaj sai cewa tai " Yaya nagode insha Allah bazan baka kunya ba. " Ya mata wani kallo sannan yace " kada dai kije ki biyewa kawayen banza, sannan kar ki kuskura kiyi kuka da sunan wai kinyi rashin mahaifinki ko nan. " Nafi ta d'aga kai jiki a sanyaye, nan tamai sallama ta juya a hankali take tafiya har ta fita daga kofar. Tayiwa Mumy sallama nan Mumy ta bata dubu biyar wai kudin kashewa, itakam Nafi kin amsa tai sai da taga ran mumy ya b'aci tukunna, nan tai godiya suka fito, b'angaren Umma sukaje. Tana zaune a falo, Aneesa na gefe itada kawarta suna kallan wasu kaya, da kyar aka amsa sallamar ta, jiki a sanyaye ta shiga sannan ta tsuguna tagaida Umma sannan tagaida Aneesa da kyar suka amsa suna mata kallan uku saura kwata, Umma tace " ai anyi dabara da aka saki boarding dan na gaji da ganin yar rigar fulani tana yawo a gidan nan. " Nafi batace komai ba, Aneesa ta harareta tace " Allah ya raka taki gona. " Jiki a sanyaye Nafi ta fito daga b'angaren nan ta karasa kitchen tama su Goggo sallama. A mota ta taradda Little zaune a gaban Mota kusa da Habib suna hira, tasa hannu ta goge fuskarta sannan ta karasa cikin mota. Habib ya juyo ya kalleta yace " Gimbiya Nafeesa irin wannan jira da aka sani haka? " Murmushi ta d'anyi sannan tace " Tuba nake, amma gimbiya ai Maryam ce bani ba. " Habib ya kalli Little wacce taji dadin kalaman Nafi, yace " to me kike so indinga ce miki? " "sunana mana. " Habib yai dariya yace " ai ni bana fadan sunan mutum, kowa da sunan da nake cemai. " Nafi ta kalli little tace " Little ki zabarmin to. " Su dukansu dariya sukai, nan Habib ya tada mota, Nafi dama tana baya, ita kuna Little na gaba. Sun fara tafiya Little ta juyo tace " Kinje kunyi sallama da yayan? " Nafi tai murmushi tare da dg mata kai, Habib ya kalli Nafi yace " me yakeyi? " Tace " na daiga yana danna abu irin na Little a falo. " Suka sa mata dariya sannan Habib yace " Ashraf kenan, yanada kwakwalwa ga iya aiki amma har yanzu na rasa me yake hanashi yin aikinsa. " Nafi ta kalli Habib da mamaki sai dai batasan me zata tambaya ba, jitai Little tace " anya ba abin da bane yake damunsa? " Habib yai ajiyar zuciya yace " nima ina tunanin wannan, ai ko waye dole ne abin ya zamarmai Karma. " Kai Little ta jinjina tace " Shiyasa bana ganin laifinsa in yana fada, itama Mumyn ai.... " Sai kuma tai shiru. Nafi kam ta kasa shiru ta kalli Little tace " Me ya sameshi dan Allah. " Little tai ajiyan zuciya tace " Nafi ki bari sai kin dawo zan sanar dake." Habib ya kalli Little baice komai ba. Har suka isa makaranta zuciyar Nafi fal take da tunani kala kala menene ya faru da Ashraf? Ita kanta tana mamakin Mumy da ta auri kanin babansa kuma harda 'ya a tsakaninsu. Sun shiga makaranta nan Principal ta hadata da wata Copper wacce zata dinga nata extra lessons, sunyi sallama Little ta shiga mota duk tausayin Nafi ya kamata. Nafi kam sai data b'oye hawayenta, Habib ya mata alkawarin zuwa d'aukota shida Little in biki yazo, itakam batace komai ba dan bata wani damu taje bikin ba. Tana nan a tsaye har suka shiga mota suka tafi, ta goge hawayenta sannan ta karasa gun House Captain dinsu da aka kira, nan ta kira yara yan Js 1 suka kwashi kayan Nafi. ¤¤¤¤¤ A gida kam har yanzu Ashraf bai sakema Aneesa kamar da ba, sai dai yanzu tana iya kokarinta wurin ganin ta farantamai rai, sosai take kula dashi, sai dai wannan ba damuwarsa bace in fact gani yakema ta takura mai bayan shi mutum ne dayakesan ya zauna shi kad'ai. Mumy da ita da mahaifiyar Habib suka shiga kasuwan ni kala kala mall da sauransu, suka had'a lefe na gani na fad'a, sunso suje Dubai sai dai Ashraf ya hanasu, yace " shi baiga wani abu da za'a siya da har za'a rasashi anan kasar ba. " Kaya kam anyishi, naira ta gurzu, sai dai wannan ba komai bane a kan irin dumbin kud'in da Ashraf yake dasu. ¤¤¤¤¤¤ An ba Nafi d'aki cikin 'yan ajinsu, gaishesu ta shiga yi dan ita a gunta hakan shine daidai. Dariya sosai suka mata, jin hausarta yasa suka san bafulatana ce, d'aya daga cikinsu wacce kana ganinta kaga wayayyiya tana kwance saman up na gado, sanye da vest da wando ta zuro kai tace " lalai da alama mun sami yar kwana. " Dariya suka kara kwashewa dashi wata tace " Ferry ashe kin gano? Da alama kan ba komai sai iyaye suka sami kud'in gomnati. " tafad'a tana kallan tulin kayan provision din Nafi. Dariya suka kara sawa, Nafi tana nan tsaye idanunta suka fara neman kawo ruwa, watace ta dafata tace " ki shiga da kayanki, sai ki zauna a up gadan dake kallan na Ferry. " Nafi ta d'aga kai alamar to, sannan ta shiga da kayan, daga ganin yanda suke mata kallan wulakanci yasa tasan bazataji dadin wannan zaman ba. Sai dai ya zatai????? Tana gama jera kayanta aka turo wata yarinya akan ta fito karatu karfe 2 tayi, Nafi tayi mamaki ganin ai yau tazo, sai dai ba yanda zatai sallah kawai tai tafita waje tanaji suna gulmar ta. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Gaisuwa da jinjinar ban girma gareku masoyan arziki, soyayyarku daban take 'yan group d'ina na The Queen Bee da Ayusher Fan Club..... ILYSM💋* { *27*} Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata, sai karfe 5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa. A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta, ba kowa a d'akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had'a ta zauna tasha, jin cikinta ya d'auka yasa ta fito tai alwala tai sallar la'asar. Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi 'yan d'akin sun dawo.

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115