Chapter 76
Chapter 76
Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara yin sanda tana bin inda takejin karar gashi a bin mamaki ba'a d'aga wayar ba. D'akinsa taji karar na fitowa a hankali ta murd'a tare da yin addu'oi a ranta, kwan wuta ta kuna da sauri tana tsoron kafin a maketa gwara taga waye. A binda ta gani ne yasa gaba d'aya jikinta ya mutu, tsayawa tai cak tana kallan Ashraf wanda ke zaune a kasa ya hada kai da gwiwa, ga kuma wayarsa nan a hanunsa yanaji ana kira bai dauka ba, sai dai ta kula ba wayarsa bace da yake amfani da ita. Ganin haske ya kewaye d'akin ne yasa ya d'ago ya kalleta da idanunsa wadanda sukai jaa, a hankali yace " Nafisa can u please get out?" Kallansa tai cikin tsananin mamakin halin data ganshi cikin rawar murya tace " Ya Ashraf?" Idanu ya runtse yace " please can u get out, banasan ki ganni cikin wannan halin....." ya karasa maganar cikin wata irin murya, sakon da aka turo mai yana kokarin bud'e kofa ne yasashi cikin wannan halin. Kawu ne yai reply kamar haka "Max na d'auka kunyi da Yaya akan bazaka kara nemana ba? To shi yace kaje yana nemanka." wannan sako ya d'agama Ashraf hankali, a iya saninsa Kawu mahaifin Habib kawai yake cema Yaya, sai dai tayaya za'ace da hannun yayan mahaifiyarsa????? Ganin bai maida reply ba yasa Kawu ke ta kiransa. Kashe wutar Nafi tai sannan a hankali ta taka zuwa inda yake, ta tsugunna tare da rungumoshi jikinta, idanunta sun cika taf da kwalla tun da take bata taba ganin Ashraf a irin wannan yanayin ba, hawaye ne ya ziraro mata a hankali tace " taya zan iya tafiya na barka cikin wannan yanayin?" Ashraf ya d'an zare jikinsa kadan yace " Nafisa please......" Hannu tasa ta rufe bakinsa sannan ta kara kankameshi hawaye suka fara zirya a idanunta cikin kuka tace " Yaya can u please share ur burden with me? Zuciyata tana zafi idan na duba naga bansan abinda ke faruwa dakai ba, bansan a wani hali kake ciki ba, Yaya ka taimaka ka sanar dani damuwar ka dan Allah...." Kuka take sosai wanda yasa jikinsa yin sanyi, kankameta yai sosai a hankali yaji hawaye ya gangaro ta idanunsa, yace " Nafisa ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata, duk wanda nake tunanin yana sona sai na duba sai inga makiyi na ne, duk wanda nake tunanin yadamu dani sai in duba inga ashe amfani yake dani a b'oye, na d'auka i am smart sai dai yanzu na tabbatar i am the biggest foolish in the world, me yasa Allah ya d'auke Abbana ya barni? Meyasa....." Kuka take sosai ta sa hannu ta toshe bakinsa tana girgiza mai kai" Yaya ka daina fadar haka, Allah na tare da kai sannan duk wanda ya zalunceka Allah bazai barshi ba ko shi wanene." Idanu Ashraf ya runtse wasu zafafan hawaye suka zubo mai yace " me ya kaini binciken abinda ya riga ya shud'e, why???" Nafi ta kankameshi tana girgiza kai tace " laifinane yaya ko ma menene laifina ne, please ka yafemin, da ban sanar dakai ba banaji zakai binciken nan, yaya ka yafemin Laifinane, nice na ja maka shiga wannan halin." Ashraf ya sa hannu ya shafi bayanta yace " ba laifinki bane, na dade ina bincikena, iya kace ke taimakamin kikai, karki sake cewa laifinki ne." Nafi shasheka kawai takeyi, bata san me ya jiyo ba amma ta tabbata abin ya shafi danginsa. Sunyi shiru suna manne da juna cikin duhu, Ashraf can cikin wata sansanyar murya taji yace " Thank u Nafisa." D'agowa tai cikin mamaki duk da ba haske ba ganinsa take ba sai dai mamaki karara ya bayyana a fuskarta, wannan itace rana ta farko data tabajin Ashraf yayi godiya bama ga ita ba, a'a bata tabajin yace ma wani bama. Murmushi taji yayi ya d'an ja numfashi kadan yace " kina mamaki ko? Ni kaina rabon danaji na fadi wannan kalma ba naji zan iya tunawa." Hannayenta tasa akan fuskarsa sannan ta hada goshinsu tace " Yaya in kamin godiya akan me kenan? Ni kuma ince me kenan, yarinyar datake yar kauye ka..........." Hannu yasa ya d'an turo kanta bakinsa yakai cikin nata, wani irin salon soyayya suke ma juna wanda kana gani kasan son da sukema junansu lalai a bayyana yake, sun dade suna sumbatar juna kafin a hankali bakin Ashraf ya sauko kan wuyanta, wani irin yarr taji a jikinta wanda yasata yin numfashi, Ashraf sam ya manta da zancen sai ta aminta dashi, sarafata ya shiga yi sai dai itama duk da batasan kan abun ba haka kawai taji lalai tabbas tanasan ba Ashraf dinta farin cikin da yake nema. Soyayya mai karfi suke nuna ma juna sam bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba sai jitai yabrabata da rigarta, ba shakka tsoro da fargaba ne ke damunta sai dai bataji duk wani wahala da ake fada zata iya bijirema Ashraf. Ya gama fita daga hayyacinsa haka itama a daidai wannan lokacin mai afkuwa ta amfku............Nikam ganin haka yasa na fito ga duhu wanda yasa ni yin tuntube da kujera😭 ************ A kauye kuwa Datti yau ya dawo ya taradda matarsa Mairo ta yimasa tuwo miyar kubewa bushashiya sai dai da zabuwa akai miyar, mamaki ya kamashi ya kalleta yace "mairo badai da zab......" Katseshi tai cikin salonta na jan hankali tace " Haba Datti bada zabuwarka bane, zabuwa ta ce data kasa na yanka mana ita." Baki taga ya washe yace " kai Mairo Allah ya miki albarka kinsan darajar dan adam." Nan ya yanko malmalar tuwo ya zuba nama sosai da miya ya hau ci, sai uban santi yake zubawa. Itakam sai murmushi takemai. Yaci yai hani'an ya tauna kasusuwa sannan ya kalleta yace " kai Mairo Allah ya barmin ke " Tace " Amin Datti." Ya kara washe baki yace "rabon dana kai nama bakina har na manta sai dai in gani a kwanon wani." Tai dan fari tace " ai banga laifinka ba, yanzu ba gashinan kafi kowa dukiyar dabobi ba duk yankin nan." Ya sake washe baki yace " Zabina guda 20 ne kaji guda 30 banda raguna, saniyoyi da akuya." Ta matso kusa dashi tace " yaushe za ka nunamin ne nima in gansu." Dariya ya kwashe dashi yace " karki damu gobe da kaina zan kaiki ki gansu." Tace to Datti Allah yabarmu tare. Yace Amin Mairoro ta.... Nace inma Maikoko ce...Lol masu suna Mairo tuba nake🤢 *#ASHRAFEENAH* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *61* Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace " Uncle tambaya nazo da ita." Uncle yace " ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta." Numfashi Ashraf yaja sannan yace " Kasan Auwal Max?" Kallan mamaki Uncle yamai yace " kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare." Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace " menene?" Ashraf yad'an numfasa sannan yace " Yana ina yanzu?" Kai Uncle ya girgiza yace " Allahu a'alam, tun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115