Skip to content

Chapter 114

Chapter 114

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,169 words 0 views Progress saved
Download Book

duniya duk ya isheshi yana ganin mota ma ta tsaya amma ko alamar mikewa baiyi ba, mutane suka zagaye motar, nan fa su Nafi suka fito ba wanda ya ganesu gwarama Inna yayan Datti na ganinta ya ganeta. Sai da aka musu iso suka zauna a ciki sannan yayan datti ya aika a kirashi. Ba'a dade ba sai gashi nan, nan yaga inna sai dai maimakon masifa gani sukai ya saki kuka yana ce mata " innar Nafi mun shiga uku na saida ma masu yankan kai Nafi." Kuka yake sosai wanda saida yasa Nafi ma kuka, Ashrad ya kalleshi yace " baka gane ni ba baffa?" Kallansa yai yanasan gano fuskar sai dai ya kasa, Ashraf yai murmushi yace " mijin Nafi ne." Nan fa aka dau salati, nan Ashraf ya zayyane musu komai, Inna ta nemi yafiya shima datti ya nemi yafiyar ta data Nafi. Sun dade kafin daga bisani suce zasu tafi,Datti yace ai auransa nanan da matarsa, jin matsalar data sameshi yasa Ashraf ya ciro kudi masu yawa ya bashi yace ya sai wasu dabobbin, sannan suyi shawara in sunfisan zaman nan to in kuma sunfisan birni sai ya turo a daukosu. Nan ya musu sha tara ta arziki suka fito, kowa sai sha'awar Nafi yake, nan Hanne ma dataji labari tazo taganta alokacib itakuma 'ya'yantama 2. Su kadai suka taho dan dan litti yace sai yayi kwana biyu, zai dai dawo lokacin bikinsu da Nafi. *********** Duk yanda Ashraf yaso su kebe da Nafi abin yaci tura har ranar zagayowar sati, Nafi tayi rabon Iv gida ya cika sai dai Anisa da Umma sukam suna zaune a bangarensu ko fitowa ba sayi. Nafi da kanta ta sai kusu kayan da zasu sa a cikin kudin dake katin da ASHRAF ya bata. Ta aikama Anisa da umma. Hall aka kama, ga innarta ta zo itada mahaifinta da hanne, dama ta shirya musu dinkuna. Su ferry da Little amara kirjin biki kenan sai hidima sukeyi, duk inda Little ta wuce Habib binta kawai yake da ido, sosai guri ya cika Abdulkadir wanda ke kula da dan siyasan nan shima yazo dan yanzu ya zama babban mutum Ashraf ya bude mai shago babba anan titin Zoo road inda yake saida kayan masarufai yanzo ko motar da yake hawa ka kalla sai ka kuma kallo, tunda ya iso shikuma ya kyalla ido yaga ferry hankalinsa ya tashi, sosai ta birgeshi. Anyi shagalin biki sosai mutane kowa ya tayasu murna, sai dai Nafi tunda ta zauna Ashraf ya hanata tashi, ko kiranta Dj yai sai yace a mata uzuri haushi duk ya isheta datai magana sai yace wai bazai yarda a wahalar mai da baby ba. Haka aka gama taro aka watse, Little da Ferry sune suka kai Amarya Nafi bangarenta inda Little tai ta mamakin sanda aka canza komai na bangaren. Duk yanda Habib yaso suyi magana da Little abin ya faskara, haka suka kai Nafi bayan sun ajiyeta Little ta juya zata tafi Habib yai saurin binta suna fita yace " Little haka zamu dawamma ko magana babu?" Kallansa tai tace " yaya da wani idon kakeso na kalleka bayan mahaifina shine sillar lalacewar rayuwar Dady?" Habib ya kalleta yace " amma wannan ba ya wuce ba?" Kai ta girgiza mai tai gaba zata wuce, hannu yasa ya rikota da sauri ta tsaya cak gabanta na faduwa yace " Little bantaba tunanin ina sanku haka ba sai bayan faruwar wannan abun." Juyowa tai ta kalleshi tace " nifa?" tafada hawaye na gangaro mata, tace " nifa da nake sanka tun ina yarinya?" Wani irin kallo suka shiga yi ma juna....... Ferry kam da Abdul bansan ya akai ba can na gansu tare suna hira mamaki ya kamani nace hmmm lalai...... Shikam Ango ana watsewa ya yaye mayafin dake rufe a fuskar Nafi yace " su Amarya am gama gudun?" Tai kasa dakai wai kunya, dariya yai yace " au abin Amaren gaske zakimin?" Ta turo baki tace " ba amaryar bace?" Yai dariya yace lalai su Amarya bari in kaiki ciki in gwada ingani ko Amarya ce da gaske." Zatai magana taji ya sureta.......... Washegari da safe taga bangarenta sosai taji dadi sai dai tace ya dawo da Anisa, ya aminta da shawarar sai dai yace sai dai a gyara mata wani bangaren dake cikin gidan dan kuwa inhar ta zauna dasu gaskiya itace a wahale dan kuwa bazai iya adalci ba zai kuma sanar da ita hakan. Da zai fita zuwa gun Anisa ne ya zaro takarda ya mika mata yace " uwar gida ga wasiyyar ki." Yai gaba Kan kujera ta kwanta a hankali ta bude takardae. _Zuwa ga sirikata_ _Bansan me zance miki ba, ban kuma san dalilina na yin wasikarnan ba sai dai nasan abu d'aya shine ke rinjayata, dan Allah ina rokonki da kularmin da wannan yaron nawa, amanace na baki kisoshi saboda Allah bawai dan dukiyarsa ba, ki nunamai kulawar dazaisa yamanta shi marayane, wannan ita kadaice rokon da zan iya miki a rayuwa._ _Ga nawa gudun mawar na auranku, ba yawa sai dai wannan nine nake daburin baki ba wanda yasan da zamansu sai ni sai ke sai Lawyer na Salim, nagode kwarai._ Murmushi tai sannan tace " Abba zan kula da yaya sosai, zan sadaukar da komai nawa a kansa." Nanta zaro takardar dake bayan wasiyyar, takardace ta nuna mallakin wani gida da kuma shago, mamaki ya kamata, da alama kuma gida ne babba sosai hakama shagon. ************** Bayan shekara d'aya, sauri take sosai tana hada breakfast Ashraf da babynta mace wato Zainab suna zaune akan dinning ya daurata a cinyarsa yana bubuga mata kan dinning da cokali wai tai sauri su yunwa sukeji. Nafi ta taho da sauri rike da plate ta ajiye a gabansa ta sa hannu ta ja kunnensa da karfi yadanyi kara kadan yace " muguntar ta motsa kenan?" Harararsa tai ta rike kugu tace "Yaya daga nan ina zaka?" Yace " zama zanyi in huta kadan kafin na fita aiki." Ta hade fuska tace " dama shigaban Company an bashi damar kin zuwa da wuri?" Yace " an fara akaina?" ya fada yana murmushi tace " ni kuma fa daga nan ina zani?" Yace " makaranta zaki." Ya fada tare da sumbatare Zee, Nafi tai kwafa tace " kai da zaka zauna a gida, mu da zamu fita shine kake min kidan yunwa?" Ya tabe baku yace " to ya zamuyi Zee ma yunwa takeji." Ta kalli agoggo ganin lokaci yayi yasa tai daki da gudu ta dauko mayafinta da jakarta ta zo kusa dashi tamai kiss a kunci sannan tama Zee tace "yaya inkun gama wasab naku ka kaita gun Ya nisa." Ya mata salute yace " yes ma." Dariya tai sannan tai waje. Motarta ta fada sannan ta kata key tai gaba. Little ansa ranar auransu da Habib. Dan Litti kuma Ashraf ya turashi kasar Spain dan yin karatu. ku samu complete Hausa Novels a shafin mu 👇 👇 👇 👇 👇 👇 👇 👇 👇 👇 https://hausanovels001.com.ng *ALHAMDULILA* _Nan ne na kawo karshen littafina na zuciya kowa da irin tasa, darusan dake ciki Allah ya bamu ikon fani dasu, kura kuran da ke ciki Allah ka yafe mana, Ameen suma Ameen._ Godiya

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115