Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,171 words 0 views Progress saved
Download Book

kuje asibiti sannan kice ta bar aikin sai ta warke. " abinda ya fada kenan ya kashe wayar. Nan Little ta fada mata gani tai Nafi ta shiga yin murmushi tana kasa da kai, zuciyarta taji tayi wasai kenan ba haushinta yaji ba? Kenan zata cigaba da mai aiki? " Little ta saki baki tana kallanta, me kenan? " *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Sry jiya nayi mistake zansa 16 nakara sa 15.* *Nagode kwarai da tunatar dani.... LYSM* 1⃣7⃣ Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin. Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita, me zata gani? Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa, hucin da yake fitowa daga bakinsa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba, a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani, itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun, ya kara daurewa ya bud'e ido, yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon." Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube, hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake, da sauri ta d'auko ta mikamai, nuna mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. " Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara, ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'angaren sa na haggu. Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun, mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura, da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i, kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji ba, yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta, a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa, sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke, tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai. Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? " A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. " Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai, sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba, Ashraf kam ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi, meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi. Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta tana mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. " Kai ya girgiza mata alamar a'a, idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah, in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. " Idanu ya bud'e a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?" Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. " Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki, xaka iya ci? " Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh" Da sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate, tazo kusa dashi, kallanta yai baice komai ba. Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba. Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi, kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biyu kenan Ina tsaye. " Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. " Falo ta fito ta maida abincin sannan ta shiga gyara, har ta gama bai farka ba, itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sai dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa, ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba. Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta fita tabarshi shi kad'ai, kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso. Haka tanaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin. _Kauye_ Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba. Sun fito suka tarar da D'an Litti a inda sukai zai jirasu, Kowa ya kalli D'an litti sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha, riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa, ya kawo hula irin tamu ta hausa ya saka, sannan ya kwama glass dinsa, gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka. Tsayawa yai ya wani karkace, su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi, wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su fura ne, kayan mata ne, gayayyaki na magani, su daddawa ne, kub'ewa busassa da sauransu. Datti ya kalli D'an litti yace " kai amma wannan yaron kana burgeni, ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. " Dan Litti ya juyo cikin gayunsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. " Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. " Sun isa Gwaram suka samu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige, Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya." Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. " Ta kalleshi tace " Dan boko banajin turanci. " Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba " Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. " Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba tare da ka sanmana ba? " Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima." Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115