Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,185 words 0 views Progress saved
Download Book

ta hakura sai zuwa gobe ta samu yin magana da Ashraf in ma wasa yake to lalai kar ya sake mata irin wannan wasan. Shikam Ashraf hankalinsa a kwance yai baccinsa, itakam Nafi akan sallaya tai bacci tana jiran Little. Little ta shigo taga Nafi na bacci, shiru tai ta tsaya tana kallanta har ta kai hannu zata tasheta ta koma kan gado ko me ta tuna? Sai naga ta fasa, kayanta ta cire tai kwanciyarta. Mumy tana shiga b'angarensu taga Kawu a tsaye sai zirga zirga yake, yanzu in har da gaske Nafi matar Ashraf ce kenan ko sun kawar da Ashraf itama tanada gadonsa? Gadan me? Bayan ba wanda yasan da auren iya kaci su karyata hakan. Ya zarfafa a tunani sam baiji sallamar Mumy ba sai jiyai ta dafashi, kallanra yai sannan ya zare hannunta ya koma kan kujera ya zauna tare da daure fuska, Mumy ta karasa gunsa tace " Me ya faru?" Ya kalleta yace " Abinda yaran nan yai yana matukar damuna, nasan Ashraf bai daukeni a matsayin uba ba sai dai ban taba tunanin zai wulakantani haka ba." Mumy tai ajiyar zuciya tace " nikaina abin nan ya tabani, sai dai ina gani ya fadane kawai, gobe zanje in mai magana ai aure ba hauka bane." Washegari da sasafe su Nafi na bacci sukaji buga kofa kamar za'a b'ala kofar, a razane suka tashi, Little ta bud'e kofar da sauri. Anisa ce a gefenta kuma Umma ce fuskarnan kamar me? Banko kofar sukai tare da shigowa ciki suka gifta Little tare da wucewa gurin Nafi wacce ta mike zaune sai dai kana ganinta kasan a tsorace take, Anisa ta karaso a zuciye ta d'aga hannu zata kifa ma Nafi mari, da sauri Nafi ta rike hannunta duk da tana tsananin tsoron yanda taga fuskokinsu sai dai bazata yarda da duka ba kuma. Anisa ta kalleta cikin tsananin kishi tace " ke har kin......." Umma ce tai saurin kifa ma Nafi wani wawan mari ba tare da ta zata ba, Nafi ta sake hannun Anisa tare da rike kuncinta ta kafe Umma da ido, Umma cikin mamaki tace " ni kike ma wannan kallan?" Nafi ta dauke idanta jitai Anisa ta rufe ta da duka gaba daya hannayenta, Little ta karaso zata tare, Umma ce ta riketa tace "meye naki a ciki? Ke bakya kishin cin mutuncin da akama 'yar uwarki?" Little ta tsaya jiki a sanyaye, Anisa kam ta dage sai sauken takaicin ta take akan Nafi, can Nafi ta mike ta rike hannun Anisa, tace "Yaya Nisa inaji yanzu kin huce ai ko?" Anisa tai sototo tana kallanta, Umma tace " mene?" Nafi wacce taji zafin dukan iya zafi ta daure tace " gani nai dukan ya isa haka inkuma ba kasheni takesan yi ba." Umma a zuciye ta fizgo wayar charger dake jikin socket tai kan Nafi zata daketa, Nafi ganin ba sarki aikam ta sake hannun Anisa tai hanyar waje da gudu, jitai ta bugi mutum, ta tsaya tare da d'agowa ta kalleshi, Umma kuma wacce suka taho itada Anisa rike da bulala zata daketa itama ta tsaya cak. Ashraf ya kallesu, yace " me kuke tunani kuke aikatawa?" Umma ta fara hucci, Anisa kuma kallan yanda Nafi ke tsaye a jikinsa take, Ashraf ya kallesu yace "Umma me kukeyi?" Umma tace " Kai dan marasa tarbiya,kayi kadan ka wulakantamin 'yata akan wata banza yar daji, kuma wlh kaji na fada maka ko ba yau ba sai na mata dukan da sai an kwantar da ita a asibiti kamar yanda aka kwantar da tawa 'yar." Murmushi ya sakar mata wanda ya bata tsoro, yace "Umma kenan banaji ranar da zakiyi hakan 'yarki ma zata kwana a gida." Anisa ta matso cikin takaici tace "Yaya mai kake nufi? In umma ta daketa kana nufin nima dukana zakai ko me?" Hannu yasa ya shafi gefen fuskar Anisa yace " No no no, kinfi kowa sanin banasan harkar duka sai dai ina nufin a ranar zamana dake ya kare." Baya baya ta fara ja, tana girgiza kai, wannan ba Ashraf dinta bane, Ashraf ya kalli Umma wacce ta saki baki tana mai kallan mamaki yace " i tried really hard inga na boye abinda ke raina, sai dai naga alamar bakusan wannan ba, dan haka daga yanzu i won't tolerate anyone ko da kuwa Little ce." Yana kai nan ya kalli Nafi yace " koma ciki ki kwanta zanga wanda zai kara gigin tabaki." Nafi kam yau ta zama kurma, a hankali ta koma ciki, Umma ta kalleta cikin takaici, Ashraf ya kalli Little yace "kin bani kunya." ya juya zai fita jiyai Anisa tace "Yaya karka fita." Juyowa yai ya mata wani kallo yace " a matsayinki na wa?" Tace "ni ai matarka ce." Murmushi yai sannan ya tako a hankali har inda take ya rungumota jikinsa sannan yakai bakinsa kunnenta yace " mata wace take shan maganin hana daukan ciki? Wacce take binciken dukiyar mijinta? Wacce take jiran mijinta ya rasu ta samu gadon sa?" Kallan tsoro tamai, ya matso da fuskarta wajen kuncinta yace " why? Kin dauka duk ban sani ba?" Ya kara mata murmushi sannan ya juya yai gaba, zubewa tai a kasa tama kasa kukan sam, Umma ta matso tace "ke ya ce miki?" Kai kawai take girgizawa, ganin haka yasa umma ta cicibeta sukai waje. Little kam da sauri tabi yayanta. Nafi kam ita kanta a d'aki zaka tai dabas tana mamakin abinda Ashraf yakeyi tun jiya, ita kanta shakkarsa take taya za'ai ya dinga fadar bakar magana hankalinsa a kwance? Bata taba ganinsa a haka ba lalai kenan akwai wani hali nashi da ya boyema 'yan gidan. Ashraf na fita bangarensa ya nufa, yau kam gidan kamar ba safiya ba kowa ya tashi, a bakin kofarsa yaga Mumy hakan yasa ya gaidata kai tsaye ya bud'e kofarsa ya shiga. Shigowa tai itama, guri ya samu ya zauna itama ta zauna a kujerar da ke kallansa, Little ce ta shigo ganinsu tare yasa ta koma gun dinning ta zauna. Sunyi shiru kafin Mumy tace " Ashraf!" Kallanta yai batare da ya amsa ba. Tacigaba "me kake nufi da kalamanka na jiya?" Cikin rashin kulawa yace "me nake nufi kuwa?abinda kikaji shine gaskiya." Ido ta kuramai can tace " kasan me kake fada kuwa? Kasan me ake nufi da aure?" Dariya yai ya kalleta yace "Mumy kenan, na dauka ko dan shekara 18 yasan me ake nufi da aure, sannan banyi tunanin zaki damu ba in nayi aure ba tare da saninki be tunda kika sake aure ba tare da sanina ba sannan kika fita daga harkata tun ina karami." Idanunta ne ya ciciko tace " Nasani i am a bad mother to you, sai dai Ashraf kai kanka kasan ba inda uwa zataki danta." Idanu ya rufe yace "gashi kuwa na gani? Tunda nake dake kin taba tambayata yaya nake?meke damuna?menene matsalata? Banaji tun mutuwar mahaifina kin kara zama dani zama na uwa da danta." Mumy tai shiru, sai idannunta da suka ciciko, Ashraf ya dan rufe bakinsa sannan ya dan sa hannu ya shafi kansa yace " inaji a jikina ba san mahaifina dani kike ba." Yana kai nan ya mike zai shiga ciki, sunansa

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115