Chapter 83
Chapter 83
rasu ba, haka ma Mahaifiyarta bazata kwanta rashin lafiya ba. Sanda Abbas yaje gaisuwa Hashim ya sanar dashi kada ya kuskura yasa a saki kayan basa so sun kuma fahimci abinda yake nufi." Yai dan hucci sannan yace kaji abinda ya faro. Ashraf banda Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un ba abinda yakeyi. Can ya daure yace " Nagode Uncle." Salim har ya bud'e kofa zai fita Ashraf yace " Maganae wasiyae Abba ta matata ta farko fa? Kasan dalilin sa nayin hakan?" Salim ya girgiza kai yace " bansani ba gaskiya sai dai nasan ana gobe zaiyi hatsari kunyi tafiya dakai dashi da malam kunje kauyuka bada taimako, yana dawowa a daren ya bani wannan takardar." Ashraf yai ajiyar zuciya sannan ya kara cewa Nagode. Salim har ya fita ya dawo yace " karfa ka kawo komai a ranka, kasan Hashim na sanka." Ashraf ya daga kai alamar to, Uncle na tafiya ya kwantar da kansa a jikin kujera yana fitar da numfashi sama sama....... *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *65* A hankali yaja mota ya nufi office ji yake numfashinsa na fita da sauri da sauri dole yai parking a gefen titi tare da kwantar da kansa kan kujera, waya ya dauka yama Dan Litti text din inda yake sannan ya maida kansa jikin kujerar. Nafi kam karfe 7 ta tashi saboda tanasan Ashraf yai break kafin ya fita, sai dai me? Bataga kowa a kusa da ita ba hakan yasa ta fito falo da sauri, nan ma ba Ashraf, ta zauna akan kujera tare da kiran numbersa, sai data kusa katsewa sannan taji ya daga cikin wata irin murya mai tsoratar da mai sauraro yace " Hello!" Mikewa tai a tsorace tace " Yaya menene? Me ya sameka?" Sama sama takejin numfashinsa ganin yanda ta rikice yasa yai saurin katse wayar. Zubewa tai a kasa tanajin zuciyarta tana kuna, hawaye ne ya zubo mata ta dafa kanta tace " wannan wani irin masifa ce? Ya Allah ka dubi wannan bawan naka ka sassautamai ka agazamai." Kara kiran wayar sa tai saima tajita a kashe. Mikewa tai da sauri ta nufi bangaren Mumy ba tare da tunanin komai ba. Mumy kam tana zaune kan sallaya tana kallan su Afra sun gama shiryawa zasu tafi makaranta, ta musu sallama sukai waje suna fita ita kuma Nafi tana shiga, Mumy cikin mamaki ta kalleta. Zubewa Nafi tai a gabanta idanunta na zubar da hawaye tace " Mumy dan Allah ki tausaya wa Yaya ki sanar dashi dalilinki nakin shiga harkarsa da kulashi da nunamai soyayya " Mumy ta buga mata wani kallo zatai magana Nafi ta katseta da sauri tare da hade hannayenta cikin sigar roko tana kuka sosai tace " kin taba tunanin yanda yake bacci da yanda yake rayuwarsa? A da na dauka ina cikin bayin Allah wanda suke bukatar a tausaya musu sai dai yanzu na fahimci cewa nice ya kamata in tausayama wasu badai a tausayamin ba, duk wahalar danasha a kauye har yaya ya tausayamin banaji nakai kashe 10 acikin 100 wanda yaya yake fuskanta" Tadan ja hanci sannan ta cigaba " He is so lonely, mutum ne wanda bai yarda da kowa ba sai kansa,Mumy nasan har kasan ranki kina tausayamai sai dai shi akullum kina daya daga cikin mutanen da suke bakin ciki ga rayuwarsa gani yake ba sanshi kike ba, kema kina daya daga kashe 20 bisa 100 na bakin cikin sa da damuwae dake ransa." Nafi ta kara matsowa tana kuka tace " Na rokeki Mumy ki tausayama wannan marayan Dan naki ki sanar dashi dalilinki na mai haka ki kuma ja shi a jiki, mutum ne wanda bai san dadin uwa ba." Idanun Mumy ne suka ciciko, Nafi tai kasa da kanta tare da share hawaye tace "indai nice bakyaso zan bar Yaya har abada zan koma kauyenmu sai dai dan Allah ki duba darajar Allah ki sassautama wannan dan naki, maraya ne shi kice gatansa in har kika nuna bakyasan jininki waye zai soshi? Na rokeki Mumy dan Allah........" Kuka ne ya kufce mata kawai ta kifa kanta akasa tana kuka, da sauri Mumy ta mike tai cikin daki, a bakin gado ta zauna itama tana kuka. Nafi kam ta dade agun kafin ta tashi a hankali tai waje, taje fita daga bangaren sai ga Anisa. Sam bata kula da ita ba saboda hankalinta sam baya jikinta. Ji tai an bangajeta da karfi har tai baya tala tala kamar zata fadi, ta dago idanunta da suka sha kuka ta kalli Anisa. Anisa ta sa hannu ta daki kafadarta da karfi tace " me? Kuka kike dan ance dole ki rabu da mijina? Ko kuwa da kina tunanin banza ta shani ne?" Ran Nafi yakai kololuwa gun b'aci, ta kafe ta da wani mugun kallo, Anisa ta matso tace " ke? Ni kike ma wannan kallon?" ta fada tana kallan Nafi. Nafi ta ki dauke idanta, haushi ya kama Anisa ta daga hannu zata mari Nafi. Nafi ta rike hannun da sauri sannan cikin dakakiyar zuciya tace " kada ki kuskura ki kara tunanin dukana, nice matar yaya ta farko, balle kiyi tunanin na miki kwace, sannan uban me kika tsinana ma Yaya? Bakin ciki? Ko me? Tun da kike dashi kin taba kula da halin da yake ciki? Kin damu da cinsa? Sannan sai anyi magana kice ke matarsa ce?" Ta cillar da hannun Anisa tace " da rashin wayau ne yasa nabar Mijina a kulawar ki sai dai yanzu ni zan kula da abina, ni zan bashi hakkin da mace ke ba mijinta." Tana kai nan tai waje a fusace. Anisa kam kasa motsi tai mamaki da tsoron yanda yarinya karama ta kafeta da ido da kalamai takeyi. Tana shiga d'akinsu ta fada kan gado, Little ce ta shigo rike da flask na abinci a hannunta, Nafi ta kalleta haka kawai taji zafin ganin Little da kular abinci. Ganin kallan da take mata Little tace " Feenah menene?" Nafi ta share kwallar ta tace " Little me yasa bakya jan dan uwanki a jiki?" Little ta mata kallan mamaki tace " wani dan uwana kuma?" Kai Nafi ta girgiza alamar ba komai sannan ta maida kanta kan gado, yau zafin kowa takeji har ita kanta, yanda numfashin Ashraf ke fita da sauri ya kasa barin kunnenta idanu ta runtse cikin kunar zuci tace " Allah ka agazama wannan bawa naka." Nima nace Amin. Ashraf nanan a zaune Dan litti ya iso akan babur. Nan Ashraf ya mike ya matsa daya bangaren shikuma ya shiga. Kallansa Dan litti yai cikin kulawa yace " me ya faru?" Kai Ashraf ya girgiza akan ba komai sannan yace " mu tafi office." Sun isa Ashraf ya shiga office dinsa ya kule kofar tare da ba secretary dinsa umarnin kar abar kowa ya shigo. Takarda ya d'ako babba ya rubuta. ABBAS / | Muktar. | Hashim | / Rumah Auwal Mask??? Shiru yai yana kallab takardar kafin yace " komai yayi connecting da Mumy, yayanta, mijinta nada, mijinta na yanzu." Itama da ita aka dau fansa saboda suna ganin Abba ne sanadiyar mutuwar mahaifinta?? Da sauri ya girgiza kai yace "
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115