Chapter 19
Chapter 19
kumai a ranta ba ganin dama ba baccin safe take ba. Itakam Nafi ta zake sai taimaka musu takeyi yau kam har su b'are maggi ace ta zuba tayi, tana yi fuskarta a sake kamar mai farin ciki da aikin, Goggo ce ta kalleta tace "Nafi kamar bakya gajiya da aiki? " Dariya tao tace "Goggo nikam ai na godema Umma data sa ni a nan nake aiki, inasan in iya abinci wlh ga abincinku nanan kanshi ma kad'ai ya isa mutum." Goggo tai murmushin farinciki tace "insha Allahu kuwa Nafi ni zan koya miki girki kala kala wanda duk ya kuskura yaci abincinki to lalai kashinshi ya bushe. " Da mamaki Nafi tace "kashe kuma bushashe? " Dariya suka mata Goggo tace "dolene inyaci abincinki sai ya kara. " Cikin tsananin farin ciki Nafi tace "ai kuwa Goggo danaji dad'i sosai. " Bayan sun gama ta karasa gurin wata a gun masu wanke wanke tad'an fita sai dai ba sosai ba, nan ta shiga tambayarta yanda ake gyaran d'aki, zama tai tamata bayanni sosai da yanda zatai mopping da goge_goge da wanke band'aki. Nafi tai godiya ta mike sunata tsokanar ta wai yanda take hausa kanaji kasan na bafullatana ce. Dariya kawai tai ta fito. D'aki ta shiga ganin Little ta fita yasa ta leka toilet tai sa'a ta tara mata ruwa, kulle kofar d'akin tai sannan ta shiga wanka, kaya tasa sannan ta shafa mai kamar yanda ta saba, har ta mike sai kuma ta koma tad'au tirare ta kalli kanta a madubi tace "in fesa? " Fesawa tai jin wani kanshin dadi, ido ta rufe sai kuma ta bud'e da sauri tace "Nafi me kikeyi hakan? " Mikewa tai tsaye da sauri ta hard'e hannayenta tai waje. √√√√√√ A d'aki Kuwa Umma ce zaune kusa da Aneesa ta kalleta cikin takaici tace "Me kike nufi? Kinfi san Ashraf akan yayanki Asim? " Aneesa tad'an turo baki tace "Umma ni da kaina zansa Ashraf ya fara aikinsa, ai company d'insa ne bana Ya Asim ba. " Cikin takaici Umma tace "wato ke miji dadi ko? Lalai Aneesa bakida hankali." Kai Aneesa ta juya cikin rashin damuwa, ta kula Umma farin cikinta bai wuce ace Ashraf ya hakura da aikinsa ba. " Umma ta mike sannan ta nunata da 'yatsa tace " wallahi ki shiha hankalinki Namiji ba d'an goyo bane balle a mazan ma irin Ashraf wanda baisan darajar d'an adam ba banda kansa wannan wa ya sani? " Aneesa ta juya kai tace " Umma Kema kinsani tunda na taso nake san Ashraf shima kuma haka, babu abinda zai rabani dashi, ni zan goya kayana. " Tana fad'a ta mike, Umma ta kalleta tare da rike hab'a cikin mamaki tace "lalai Aneesa kin girma, to wlh ki shiha hankalinki da wannan banzan san." Fita Aneesa tai batace komai ba, Umma ta bita da tsaki tace "Wai ni Aneesa ke cema zata goya Ashraf?" tai wata dariyar bakin ciki tace "Lalai Aneesa dadai ban sanki bane, ina nan a zaune Soyayya zata dawo dake hanyar danake so. " ¤¤¤¤¤¤¤ Nafi ta karasa b'angaren Ashraf da tsintsiya,a bin kwashe shara, mopper ne da sauransu ajiyewa tai sannan ta kwankwasa kofar, ta dade a tsaye kafin Ashraf ya bud'e mata, yana bud'ewa ko kallanta baiyi ba ya koma ciki, Nafi ta kinkimi shirginta tai ciki, ajiyewa tai sannan ta dukursa ta gaidashi. Lafiya kawai yace sannan ya karasa kan kujera, matsawa tai sannan tace "Yaya a fara da d'aki? " Eh Nafisa, kawai yace. Tai murmushi sannan ta d'au tsintsiyar laushi data kwakwa, harta je kusa da d'akin taji yace " Nafisa kar ki tab'amin kaya ki barsu a inda suke. " Kallansa tai cikin mamaki saidai bata iya cewa komai ba banda to, nan ta shiga da ban d'aki ta fara sai data wanke shi fes iya karfinta take sakewa saboda san ta burge Ashraf, nan ta dawo d'akin, aiki take iya karfinta tana gamawa da d'aki ta fito falo me zata gani? Ashraf ta gani a zaune a kasa jikinsa Dana Aneesa har suna tab'a juya, da alama kuka take yana bata hakuri, jin sheshekar kuka. Jitai wata irin zufa na zubo mata, ga wani abu ya tokare mata a makogaro idanunta kawai take kiftawa da sauri da sauri, sai bakinta da take ta motsawa. Jitai Ashraf yace "Aneesa meye abin kuka to? " Cikin kuka tace "taya zamuyi aure amma haryanzu baka fara aiki ba kullum kana zaune a gida yaya kasan me nakeji a raina kuwa? " Yace "ba dai aikin anayinsa bane saboda kudi ba? Ke kinsan inada kudi to meye abin tashin hankali. " Hannunsa ta rike cikin kuka tace "baka tsoron a kwace company d'in da mahaifinka ya gina da guminsa? " Ashraf ya mata murmushi yace "ya isa haka daina kuka kinji? " Ta kara narkewa tare da kankameshi. Da sauri Nafi ta juya ta koma cikin d'aki ta tsaya jitake kamar zuciyarta zata fashe ga wani abu ya tsaya mata a makogaro, ganin robar ruwa a gefen gadonsa kawai ta d'auka batare da tunanin komai ba kawai ta kafa kai ta kama sha, sai datasha sosai sannan ta ajiye, ji tai idanunta nata lumshewa batasan sanda ta zube a kasa ba tahau bacci sadidan. Shikam Ashraf dakyar ya lallab'a Aneesa ta hakura sannan ya sallamata waje, da sauri ya shigo d'akin yana fatan Allah yasa bata gansu ba. Ganinta a kwance a kasa yasa ya karasa gun da sauri ya d'agota ya fara jijigawa sai dai inaaa bacci take sosai kamar mataciya da sauri ya kalli robar ruwan maganin baccinsa wanda idan ciwonsa ya tashi yake sha dan samun bacci. Kai ya dafe sannan ya kalli Nafi tare da girgiza kai. D'agata yai cak ya d'aurata akan gadonsa sannan yaja mata kofa ya rufe. Can da Yamma Ashraf yana kwance a falo shima bacci ne ya zare shi, sama sama yaji murya kamar ta Habib a kusa dashi, idanunsa ya bud'e a hankali ganin Habib yasa ya bud'e idan gaba d'aya. Murmushi ya sakar mai sannan ya kanne mai ido d'aya yace "Hi Buddy! " Ashraf ya rufe idansa yace "a naci ka iso? " "to ya zanyi? Na kula in ma dade ban ganka ba zazzabine ke neman shigata. " Ashraf ya d'anyi wani murmushi yace "Shugaban yaudara kenan, to ban shiga ba. " Hanin ya zauna a kusa da Ashraf tare da sakin ajiyar zuciya yace "Kai mutumin wlh da akacemin wai an rasaka jinai kamar zam mutu. " Kai Ashraf ya girgiza, Habib Yace "yanzu Mumy zata iso da abincinmu tace d'azu ta aiko anata knocking baka bud'eba. " Baya Ashraf ya juya yace "ai tunda kazo shikenan rayuwata ta gama canzawa. " Dariya sukai a tare, jin an kwankwasa Habib ya mik'e ya bud'e Mumy tana shigowa cikin falon, Nafi wacce ta farka sai dai baccin bai gama sakinta ba ga kanta ba d'ankwali ta fito daga d'akin Ashraf tana tafe tana murza ido irin alamar baccin bai gama sakinta ba. Tiren juice d'in dake hannun Mumy ne ya fad'i wanda hakan ne ya kai hankalin Habib gun, hakan ne kuma yasa Ashraf dake kwance ya mike dan ganin meye, sam ya manta da Nafi na d'aki,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115