Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,130 words 0 views Progress saved
Download Book

katon kitchen d'in inda masu aiki keta hidima Umma ta tafa hannun ta hakan yasa duk suka taho, Umma ta kallesu tace " Yauwa dama so nake in sanar daku kun samu kari. " Kallan juna sukai na mamaki, tasa hannu ta finciko Nafi tace " gatannan da safe zatazo ta tayaku aiki sannan da rana ma haka." Nafi ta kara kasa da kanta, Umma tace "na umarceku ku sata aiki sosai, saboda ita ta fiku cin riba dan inda zata kwanta yafi naku haka abincinta da suturarta tafi taku. " Suka amsa da to, ta kalli Nafi tace." Ke kuma dan gidanku kullum da sasaafe in ganki anan hakama da rana, bazaki dinga cin abinci a banza ba. " Nafi ta d'aga kai, Umma taja kunenta tace " kuma wlh inji maganarnan abakin wani ko da Little ce bare Ashraf Allah sai kin gane kuranki. " Tana kai nan tai gaba. Nafi tai shiru, jitai ance ajiye kwanukan ki tafi gobe kya fara zuwa, Nafi ta kalli mai maganar wata babba ce a kalla zatai sa'ar Innarta, ta ajiye tiren sannan ta gaidasu tare da musu sallama. ********** D'aki ta koma ta zauna a kasa tai shiru, bacci ne yai gaba da ita. Ashraf kam bayan ya fito daga d'aki Aneesa yama waya yace ta fito ta rakashi an guwa. Jifatu ya wuce da ita, tanata murna ganin yau gata ga masoyinta, suna tafiya ne ta kalleshi tace " Yaya ya maganar sa ranar da akai ai tana nan ko? " Ya kalleta tare da murmushi yace " eh mana ko musa a kara matsowa da shi? " Idanu ta rufe tace " Kai yaya wata biyu ai kamar yau ne. " Aneesa ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace " Yaya wlh ni kad'ai nasan missing dinka danai jiya. " Titi kawai ya kalla baice komai ba sai murmushi da yai. A bakin jifatu yai parking, nan ta fito shims ya fito suka shiga ciki, bangaren kaya na atamfofi lace da mayafai sukai, ce mata yai kawai ta zab'a, hakan yasa tai tunanin nata ne, sosai ta jidi kaya shima yana tayata, suks wuce gun takalmi, nan ne dai yace banda takalmi sai dai jaka, saboda shikam yasan baisan size dinta ba. Itakam Aneesa sai farin ciki take har suka gama zaben suka fito, sun shiga mota ta kalleshi cikin kauna tace " Yaya na gode sosai. " Ya kalleta cikin mamaki yace " name fa? " Tace "na kaya mana. " Murmushi yai yace "Aneesa ke kuma mai zakiyi da kaya? Duk yawan kayanki? " Fuska ta had'e tace " na waye to? " Ya kalli titi yace " Nafeesa. " Gabanta ne ya fad'i cikin tsoro ta kalleshi sai dai gani tai shi ko a jikin sa, ranta yai mugun b'aci........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣1⃣ Ashraf ne ya kalleta kadan yace "Aneesah tailorn ki kuwa yana nan? " Fuska ta kara daurewa tamau tace " menene? " "kayan Nafisa nake tunanin muje akai mai can naga ba laifi ya iya d'inki sosai. " Jitai zuciyarta na neman tsagewa saboda takaici, rasa ma mai zata cemai tai, kawai sai ido ta bishi dashi, ganin kamar bai ma fahimci ranta a b'ace yake ba yasa tace " Yaya d'anyi parking." Cikin mamaki ya kalleta yace " parking kuma? " Kai ta d'aga hakan yasa ya gangara gefen titi, ta bud'e kofar ta sannan ta kalleshi tace " randa zaka fita domin ni ka d'aukoni amma bazan zauna kusa da kai domin wata ba. " tana kai nan tai waje, ya bita da kallo cikin mamaki, me take nufi domin wata? Yana kallanta ta tari adaidaita, ga magrib ta kawo kai,shima ya ja mota yai gaba. Aneesa na shiga mota ta fara matsar kwalla dan tsabar takaici ita zai d'auka su zaboma wannan kucakar kaya? Tana isa gida ta wuce gun ummanta da gudu nan ta sanar da Ummanta duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa " Umma kinga lesukan dana zab'a kuwa? Na d'auka nawa ne? Ina wannan kucakar ina sa kayan dubu talatin? " Umma ma da ranta yakai kololuwar tashi tace " kwantar da hankalinki ita d'in banza? Har ta isa tasaki kuka? Bare har ta had'aku fad'a da Ashraf?" Aneesa ta goge kwallarta tace " Umma me Ashraf yake cemin? " "Neesah mana, tun kina karama yake fad'a miki haka shi yasa wasu ma haka suke ce miki." Aneesa tai kwafa tace " to Umma tunda na cemai wannan yarinyar ta d'auka ita ya kira d'azu bai sake cemin Neesah ba har yanzu. " Umma ta kanne ido cikin b'acin rai tace " Aneesa kada ki kuskura ki kara yadda Ashraf yasan bakyasan yarinyar nan, sannan karki kara yimai musu akanta." Aneesa ta mata kallan mamaki, Umma tace " tabayan gida zamu b'ulo mata, ni na fad'a miki bazata cika sati a gidan nan ba zata d'auki tsuman kafafuwanta tayi gaba. " Aneesa ta jinjina kai alamar gasuwa tace " Umma ni ko ganinta ma bana sanyi wlh. " Umma tai murmushi tace " d'aure kinji 'yata, sati d'aya yayi yawa. " Nan sukai murmushin mugunta su dukansu. Nafi kam tana zaune a d'aki ita kad'ai mahaifinta ne ya fad'o mata a ranta tace " ko baffa yana me? " Jitai an kwankwasa kofa hakan yasa ta mike tare da yafa d'an kwalinta ta bud'e kofar, Matar data gani d'azu itace ta gani yanzu, ko ba'a fad'a ba tasan Mahaifiyar Ashraf ce, murmushi ta mata sannan tace "fito falo muyi magana." Tai gaba Nafi ta bita a baya, akan kujera ta zauna hakan yasa Nafi ta zauna daga nesa kadan a kasa, Mumy ta kalleta tace " ya sunan? " "Nafi. " ta fad'a kanta a kasa. Mumy tace " Nafisa kenan ai." Nafi tace " Eh." tai maganar cikin sanyin murya. Mumy ta kalleta da gani batafi sa'ar Little ba tace " kinsan ko ni wacce? " Nafi tad'an kalleta kad'an sannan tace " Mamar Dan Binni ko? " Mumy tai dariya tace " Ashraf kenan? " Kai ta d'aga itama tana murmushi, Mumy tace " Nafi iyayenki fa? " Kallan Mumy tai jiki a sanyaye batace komai ba, Mumy tace " Nafi karkiji komai ki sanar dani duk abinda ya faru babu wani abu, ni mahaifiyar Ashraf ce." Nafi tai shiru me zatace? Me zatace? Jitai Mumy tace " Nafi!! " A hankali Nafi tace " Mahaifiyata ta koma saudiyya da zama, mahaifina shine yake kokarin aurar dani ga babban mutum shine Dan binni ya taho dani. " Mumy tai shiru ba shakka yarinyar abin tausayi ce amma ita tasan Ashraf sarai shi ba mai shiga abinda bai shafeshi bane bare har ya d'auko yarinya daga gaban mahaifinta. Ta kalli Nafi tace " Kidinga kirana Mumy kamar yanda kowa yake cemin, sannan ki saki jikinki kamar nan ma gidanku ne. " Nafi ta d'ago ta kalli Mumy idanunta suka ciciko, Mumy tai murmushi tace " Karki damu kinji? Sannan karki kara cema Ashraf dan binni kidinga cemai Yaya kamar yanda kowa ke cemai. " Ta d'aga kai, ba shakka yanda taga yanayin 'yan gidan lalai in tsautsayi ya sa akasan an d'aura

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115