Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,169 words 0 views Progress saved
Download Book

Abban bazaiso in barsu su kara b'ata ba." Lawyer yai dariya sannan yace " Hakane, dama ance Eye for eye, tooth for tooth." Sunyi sallama Ashraf ya bud'e mota ya fito, Asim ya gani ya nufoshi yana wata tafiyar kasaita. Ashraf yaja tsaki yace " The biggest fool is here." Asim ya karaso cikin isa sannan ya shiga tafama Ashraf, kallansa Ashraf yai yace " kai kuma me ke damunka?" Asim ya saki dariya sannan yace " Ashraf shi yasa nace maka ka kiyayeni ni ba sa'an yin ka bane." Kallan sa Ashraf yai yace " kana tunanin kaika aikata hakan?" Asim ya jinjina kai yace " sosai ma tunda ninasa aka sace project din." Kai Ashraf ya jijiga alamar tausayawa sannan ya matso yad'an bigi kafadar Asim da hannu yace " u are such a big fool, ka daiyi tunani dakyau amma ninasan kanka bashida wannan basirar, kaidai basirarka d'aya ka turo a kasheni." Yana kai nan ya juya yai gaba. Asim yabishi da kallo cikin kuluwa yace " me? Yasan Abbanane yasani ko me?"kai ya jijiga alamar a'a sannan yace " ai ba yanda zaiyi ya zargi mijin mahaifiyarsa. Ashraf kam office ya koma ya cigaba da aikinsa, wanda akasa ya saci takardun a cikin members dinsa sai b'uya yake yi, sam Ashraf bai kulashi ba sai ma wani abu dake mai yawo a zuciya, wato kawu abin tsoro ne na gaske, ya tura d'ansa yayi abu yanzu in asiri ya tuno fa? Lalai mutumin nan wato akan abinda yakeso he can use anyone." Yaja tsakin takaici inya tuna uwarsa ma amfani yake da ita. Sai yamma ya tashi nan lawyer ya sanar dashi yace Slc ya sanar musu sai dai sunce a jira director ya shigo gobe dan shine yai proposing din project din. Gida Ashraf ya wuce, yana shiga yai parking sannan ya kira Little a waya, bayan ta d'aga ne yace " turomin kawarki." Little tace " wa kenan?" Ashraf ya had'e fuska yace " wace kawa zance ki turon bayan Nafisa." Da mamaki tace " naga kunyi sallama d'azu ta tafi ai." Da sauri taji yace " bangane ba? Ina ta tafi?" Little tace "Skul ba ta kiraka ba?" Katse wayar yai sannan yai wirgi da ita gefen kujera sai a lokacin ya tuno mai sukai, yai hucci sannan yace " waya bata permission?" Kansa ya shafa sannan ya fito ransa duk a jagule, b'angarensa ya nufa ya bud'e kofa ya shiga, kamshin turaren daya jine yasa ya d'ago dan ganin meke faruwa? Anisa ya gani sanye da wasu 'yan iskan kaya riga ce iya cibiya sai wani mini siket a jikinta tayi kyau sosai sannan kwalliyace ta tada hankalin duk wani namiji indai yanada lafiya, duk da shigar ta daki Ashraf matuka gashi dama ya dade rabonsa da ita dan dama ko da tana gidan haushin abinda takemai yasa yake kin kusantarta. Idanu ya kankance yace " ke kuma me kikeyi anan?" Cikin takun jan hankali ta taso ta fara tahowa tana tuno shawarar Umma ki maidashi naki, zuciya da gangan jiki bayan mun gama amfani dashi sai mu munamai yayi kuskuren fifita kucakar yarinyarcan akanki." Ta karaso tare da zura hannayenta ta wuyansa ta kwanto a jikinsa sannan ta saki ajiyar zuciya tace " Hubby do u know how much i miss u?" Ashraf ya d'agota sannan yace " me kikeyi anan......." Bakinta ta saka a nashi nan fa kaji tsit malam....Duk yanda yaso ya daure ya ture Anisa ya kasa dan kuwa in zuciyarsa bataso to fa jikinsa naso. Nan ya sungumeta sukai d'aki........Ni kuma da jawo musu kofa nai gaba. Bayan sun gama ne sunyi wanka sannan Ashraf ya had'e fuska tamau, ta matso kusa dashi tare da daura kanta akan kirjinsa Tace " Hubby bazaka yafemin ba?" Kallanta yai sannan yace " Anisa sam ni na rasa mai ke damunki." Ta cusa kanta a kirjinsa tare da sakala hannunta ta bayansa tace " tuba nake dear, kaji? Bazan sake ba." Yai shiru hakan yasa ta cigaba " Bakasan yanda nakeji ba in ina zaune a gun Umma." D'agota yai zaiyi magana Nafi ta fad'o mai a rai, jiya ya tuno sanda ya rungumeta a jikinsa me yasa bayajin irin wannan yanayin inyana tare da Anisa? Mikewa yai tsaye ya wuce toilet tabi bayanshi da kallo sannan ta tuno sanda tagansu sun shiga mota da Nafi. Ashraf kam a toilet ruwa kawai ya sakar ma kansa a ya sa hannunsa ya rike bango ruwa na dukansa a bayansa, idanu ya runtse sai dai abin takaici Nafi ya hango sanda ta shiga cikin ruwa, ya bud'e idanunsa tare da kallan madubin dake toilet din mamakin kansa yakeyi ace kamar shi yazauna yana tunanin wata 'yar karamar yarinya?" ********** Nafi kam tun bayan isarta makaranta sam ta rage ko magana dan daba ba kawar da zatai hira da ita, karatunta kawai takeyi sai dai a 'yan kwanakin nan har rama tai saboda ko abinci takeci tunanin Ashraf takeyi wannan abun duk ya isheta ta kosa su Ferry su dawo ko dan ta samu damuwar dake damunta ta ragu. ****** Scl hankalinsu ya tashi jin gaskiyar al'amari agun director cewarsa abokinsa ne ya bashi, wannan dalili yasa suka rubuta takardar hakuri suka aika company din su Ashraf wanda hakan ya sa ma'aikatan company d'in suka tausaya ma Ashraf sannan sukai dana sanin abinda suka aikata a gareshi, matsayinsa ya d'aukaka dan su cewa sukai a bashi matsayi babba wanda ya dace dashi. Kawu kam duk yanda kaso kasan bakin cikin dake ransa bazaka taba sani ba a fili yafi kowa farin ciki dan har murna aka dinga tayashi ganin yanda yake ta farin ciki kamar me. Sai dai Ashraf kam kallansa kawai yakeyi dan yasan sarai yafi kowa bakin ciki. ********* Sati biyu da komawar Nafi makaranta 'yan skul suka dawo, farin ciki agunta kuwa ba'a magana, nan suka had'u da Ferry da Ferry da Jibiya, sai dai Ferry na ganinta tasan akwai abinda ke damunta. Da daddare bayan jibiya tayi bacci Ferry ta kalli Nafi tace " Feenah meke damunki?" Nafi tai yake tace " ba komai." Ferry tasa hannu ta dafata tace " Nafi akan yayanki ne?" Hawayen da ta dade tana had'iyewa ne suka zubo, Ferry hankalinta ya tashi tace " Feenah menene?" Nafi ta goge hawayenta sannan cikin muryar tausayi da radad'in zuci tace " Ferry inaji san Yaya Ashraf shine zai zama ajalina." Ferry ta kalleta tace " Feena me kike fad'a haka?" Nafi ta kara share hawayenta tace " Ferry ko bacci nake da tunanin mutum nan nake kwana kullum sai nayi mafarkinsa, rashin ganinsa na hanani komai a rayuwan nan na rasa ina zansa kaina." Ita kanta jikin Ferry sai dayai sanyi tace " Feenah." Yanda ta kira sunan Nafi ne yasa Nafi ta tattara hankalinta kanta. Ferry ta cigaba " Na fahimceki sai dai Feenah inaso ki koyama kanki danne so, kada ki kuskura ki bari shi wanda kikema wannan san ya fahimceki in kuwa kika bari har hakan ta faro? Maganar gaskiya ko shima yana sanki zai dinga wulakanta ki." Nafi ta kalleta tace ta ya ya? Ferry tai dariya tace karki damu zan koya miki yanda zakiyi ki mamaye zuciyar wannan yayan naki,

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115