Skip to content

Chapter 104

Chapter 104

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,166 words 0 views Progress saved
Download Book

dan murguda baki tace " nidai ban fadi suna ba." Kallanta ya tsaya yi, ta debi ruwa a hannunra ta watsa mai tace " yallabai kallan fa?" Dariya yai yace " fada kikeso?" Ta tsuke baki, shima hannu yasa duka biyu ya riga watsa mata ruwa, nan itama ta dage tana watsa mai, dariya sosai suke yi wanda kana ganinsu kasan suna cikin tsananin kaunar juna. Bayan sun gama wanka, ta jawo towel d'aya ta rufa sannan tace " na fita." Kallanta yai yace " nifa?" Tamai gwallo tace " ka dauka da kanka." Tai d'akinsa tare da zama kan gado tana dariya. Ashraf ya fito yana zuwa ya sa hannu a gugunta ya matse da karfi, wanda ya sa ta saku kara yace " ni kika ki daukoma towel?" Tana ihu da dariya tace " sry Yayana na tuba na daina." Yace " inaa baki dainaba sai na hukuntaki tukun na." Ganin yaki saketa yasa tace " Yaya Nisa?" D'agowa yai da sauri ta mike da gudu tana dariya. Murmushi yai sannan ya mike sambal akan gado tare da rufe idansa. Ahhh na kosa in gama wannan case din in ganni tare da matata kullum. Abinda yake fada kenan a ransa. *#ASHRAFEENAH TEAM* [8/28, 19:57] Umar Dalha: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Gareku yan gro din World of Hausa Novel, Mumbari M.Jabo, Maryam mai dala grp na gode kwarai da yanda kuke san littafin nan. ILYSM😍* *81* Washegari da safe bayan Kawu ya fita, Dan Litti yazo ya dauki Mumy da Nafi yai abuja dasu dan tacan zasu tashi gobe. Little kam taji takaici sai dai Nafi tace mata ai ita saboda makaranta, tunda su sai nan da 1mnt akace list dinsu ma zai fito. Ashraf sai dayaga tafiyarsu sannan ya kira Kb yace " a ina kace an samu Dan Siyasan?" Kb yace " yana nan asibitin Murtala ashe bashida lafiya ne shiyasa akaita nemansa aka rasa." Ashraf yai murmushi sannan yace " ganinan zuwa ka turon ward din da yake da number d'akinsa." Nan take Kb yamai Text Ashraf yaja mota yai gaba. Bayan ya isa asibitin ne ya tafi ward din masu cancer sannan ya duba number d'akin. Knocking yai nan akace ya shiga, a hankali ya tura kofar d'akin, wani ne a kwance jikin nan duk ya rame kamar me kanjamau sannan ga wani matashi a kusa dashi a zaune. Jiki a sanyaye Ashraf ya shiga tare da karasawa bakin gadon. Matashin wanda baifi shi ba yace " ban gane ba?" Ashraf yai murmushi sannan ya dauko complimentary card dinsa ya mika mai yace " sunana Ashraf." Kallansa yai, wanda hakan yasa Ashraf yace " ba Dan siyasan dayai House of rep bane da?" Matashin yace " shine." Ashraf ya kalli mara lafiyan yace " Alhaji Uba ka san Mansir?" Kallan Ashraf yai fuskarsa dauke da alamar tambaya, Ashraf yace, " Mansir kanin Abbas marigayi mai A&A Food. Ltd?" Haryanzu dai bai fahimta ba sai dai ya maimaita kalmar A&A?" Ashraf yace " eh wanda yake auren kanwar Hisham." Jin sunan Hisham yasa ya fara kokarin mekewa zaune, hakan yasa d'ansa ya taimakamai ya zauna, kallan Ashraf yai yace " ina Hisham? Ka taimaka ka kiramin shi." Ashraf yace " baya kasar ne yanzu haka ma shiya turoni nadubaka, baisan baka da lafiya ba." Hannun Ashraf ya kama guda d'aya wanda Ashraf ya dana start da d'ayan hannunsa a wayarsa dake aljihunsa. Mutumin yace " Yaro ka ba Hisham hakuri, a zahirin gaskiya nayi laifuka da dama a rayuwata ta duniyar nan, wasu na nemi yafiya wasu kuma banma san inda mutanen dana cuta suke ba, na hau mulki, dadinta yasa na manta da Allah na kwashi dukiyar jama'a sannan na cuci jama'a Hisham na d'aya daga cikin mutanen da bazan taba mantawa ba saboda nine sanadin talaucewarsa." Ashraf yai shiru tausayin mutumin ya kamashi, ita dama rayuwa haka ne, yau in kaine gove ba kai bane. Mutumin ya cigaba, ka san kanin mijin kanwarsa?" Ashraf ya ce "eh shine Mansir din ai.", Mutumin yai ajiyar zuciya yace " kacema Hisham wlh wannan mutumin shine ya sani komai, shawara yazomin da ita ta neman kudi, nikuma alokacin idona ya rufe, zuciyata ta zarme ina ganin zan samu kudi mai yawa da xai sa inyi campaign ba tare da matsala ba, shi yasa na dauki shawararsa, sai dai dalilina yasa aka kama dukiyarsu mai yawa har hakan yakai ga ajalin mahaifinsa, wanda tsoro yasa nakasa fadar abinda ya faru a lokacin, ina tsoron kar nima azal ta fadamin." Kuka ne yaci karfin mutumin ya shiga yin tari a hankali,yace " yanzu gashinan kowa ya gujeni, wannan yaron shi kadai ke taimaka ta, shi kuma ba jinina bane rikonsa nai, nawa 'yayan duk sun gudu sun barni." Idanun Ashraf ne ya ciciko, yasa stop sannan yace "amma wace irin cancer ce ke damunka?" Murmushin yake yai yace " blood, anyi maganin har an gaji shiyasa nace shima yaron nan ya barni kawai a gida in kwanana yazo in tafi." Ashraf ya kalli matashin, hawaye yaga yana gogewa, tausayi ya kara kamashi, ya kalleshi yace " ya sunanka?" "Abdulmalik." Ya fada Ashraf yace " wani aiki kake?" Yace " kasuwanci nake a kwari, inada karamin shago." Ashraf ya kara tausaya mai, yace " aure fa?" Yace " shekarar Alhaji 5 kenan ba lafiya ina ni ina tunanin aure?" Ashraf yai shiru kafin daga baya yace " ka zo ka sameni a address din dake jikin katin, inada sha'awar kasuwanci inyaso sai in bude ma babban shago sai ka dinga mana." Kallan mamaki Abdulmalik yama Ashraf, shikam Uba kuka kawai ya saka yana godiya kamar me, Ashraf yace ba komai, sannan ya ajiye musu kudi dubu 30 ya fita. Yana fita ya runtse ido cikin tsananin tausayi yace " Rayuwa kenan." ********** Kawu ne zaune kusa da Asim ya kalleshi yace " wlh kaji na rantsema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba." Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa. Kawu yace " to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma......" Da sauri Asim yace " Sata nai a d'akin Ashraf." Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace "mene?" Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru. Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace " bakada hankali ne? Me yasa ne nikam kwakwalwar kifi Allah ya d'orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron, shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d'akinsa?" Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace " kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba." Waje yai da sauri cikin takaici, yana fitowa Anisa ta kirashi tace "Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?" Cikin fada yace " kamar ya?" Tace " a'a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya."

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115