Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,139 words 0 views Progress saved
Download Book

zaki hakura da zuwa? " Kai Nafi ta girgiza tace " Muje nima ina san zuwa ai, kuma kan yama daina. " Nan suka mike Nafi ta kara gyara fuskarta sannan suka fito, sunzo shiga mota shikuma ya fito daga b'angaren Mumy, yana kallansu har suka shiga ya d'an yi wani smiling yace " lalai yara sun girma." abinda ya fada kawai kenan yai gaba. Su kuma suka shiga motar Little 'yar karama wanda Kawu ya sai mata wai murnar gama secondary. ¤¤¤¤¤¤¤ Umma na zaune kusa da Asim acan kuryar d'aki, Asim ya nisa yace " Umma tanashan maganin nan kuwa?" Umma tai murmushi tace " Ai tunda muka bata magani tai b'arin nan na tsoratar da ita akan in har ta haihu yanzu da Ashraf to fa lalai wulakantata xaiyi dan kuwa maza basasan mace mai saurin haihuwa." Asim yace " to kidai tabbatar tanasha dan kuwa in har ta haihu da Ashraf to fa komai bazai yiwu ba, bazata taba bamu hadin kai ba, sannan muma in muka halaka Ashraf bayan mun amshe company d'insa da sauran dukiyarsa in har abinda aka haifa ya girma ya gano nan ma kinga akwai matsala. " Umma ta jinjina kai tace "karka damu da wannan amma nikam har yanzu fa hankalina bai kwanta da wannan wasiyar da ya bata ba. " Asim ya kurawa kasa ido, sannan can yace " karya yakeyi ai ni da farko na yarda sai da naga wani murmushi da Kawu yai bayan ta kawomai haka kawai jikina yaban ba haka bane, sai daga baya nai tunani ta ina mutumin da zai mutu zai bar wasiyar kud'i kawai???? " Umma ta jinjina kai tace " nima yanda naga babanka nayi ne yasa nasan ba haka bane sannan nasan halin Yaya sarai bazai bada kudi kawai haka ba. " Nan suka cigaba da kule kulensu....Nikam nace Allah ya kyauta dama ita zuciya kowa da irin tasa. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su Little kam an d'auko Amarya suka wuce inda za'ai event d'in, suna tafe ana hira saboda duk kawayene, Nafi ma yanzu bata kunyar shiga hira, har suka isa. Guri yayi kyau bayan Amarya tazo ne aka fara gudanar da shagalin biki, Nafi tana zaune daga gefe ganin yanda 'yan mata keta rawa su Little ma an zake sosai, Nafi dai tana gefe rike da wayar Little tana dadanawa, tunanin kiran Ferry ne yazo mata, nan ta mike ta d'an matsa kadan daga inda ake shagalin. Daga can ferry ta d'auka nan suka shiga hira, tana nan a tsaye suna waya sai dai suk sanda ta kalli gun idanunsa na kanta, hakan yasa ta fara tsarguwa, daga gani shima gun bikin yazo yana zaune akan motarsa. Ganin kallan ya fara isarta yasa ta matsa daga gun, bayan sun gama waya Nafi ta juya da shirin komawa. Ganin mutum tai kawai a bayanta tana juyawa suka hada ido, Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace " Malam lafiya? " Wani lalausan Murmushi ya sakar mata sannan yace " Aminci Allah su tabbata a gareki. " Ta kalleshi cikin mamaki sannan ta d'an motsa baki a hankali tace "tare da naka, amma..... " " Shiiii dan Allah karki koreni kar kuma ki nuna bakya sona daga gani na yau d'aya." Nafi cikin mamaki ta kalleshi, sai dai har kasan ranta yaso sata dariya yanda yai, ya cigaba da cewa " Sunana Al-Amin masoyin wannan yarinyar. " Juyawa tai bayanta dan ganin wace yarinyar, ya sakar mata murmushi yace " ina kike dubawa bayan gatanan a tsaye. " Nafi ta harareshi yanzu kam ta gane da ita yake, ya d'an rike kunnuwansa yace " Tuba nake ranki ya dade da alama na b'ata miki rai. " Nafi batasan sanda tai murmushi ba tace " ba wani b'ata rai sai dai kayi hakuri ni matar aurece. " Gani tai ya hau dariya, ya kalleta yace " matar aure? Wow na gode da alama da wuri zamuyi aure in killeceki a d'aki." Nafi ta makamai harara, da sauri ya kara rike kunne, yace " Taya zakice min ke matar aurece? Ina mijin? " Shiru Nafi tai a ranta ta ce " inafa yake? Yana can gun matarsa. " Al-Amin yai murmushi yace " please ki amince dani, zan kula dake yanda bakya tunani, ni d'an Katsina ne, sannan kanwar maman yarinyar da ake aurenta ne. " Nafi ta kalleshi sannan tace " lalai yayi kyau." Hannunsa ya had'e guri d'aya yace " Dan Allah sunanki?????? " *FEENAH* abinda ta fada kenan, yace "wow nice name, a ina kike? " Ta juya kai tace " zan koma ciki. " Bata jira amsarsa ba ta fara tafiya, Biyota ya fara yi sai data juyo tace " dan Allah Al-Amin ka kyaleni. " Kansa ya shafa yace " kai!!! Naji dadi dan sake ki kiran sunana." ta kara harararsa sannan ta juya. Taji dad'i sosai dataga bai biyota ba, haka kawai taji ta saki murmushi. Sai da aka gama, wajen isha'i sannan suka fito zasu tafi, suna fitowa ya taso ya karaso gunsu tare da musu sallama, Little ta amsa tana mai kallan sani sai dai ta rasa a inane, yace " Little manya, can na ganki ai kinata rawa ana bikin Aminiya. " Little ta nunashi da yatsa tace " Ya Al-Amin." "Bingo!" ya fad'a yana murmushi, itama murmushin tai tace " Ya Al-Amin ace kaine, nifa ince na rasaka sam ashe ka zama babba ko a hanya na ganka zanyi wahalar ganeka. " Ya harareta yace " Haba Little a gaban Swt Feenah kike fadar hakan? " Ta kalleshi sannan ta kalli Nafi data juya kanta, tace " yaushe ka ganta?" Yace " gatannan sai wulakantani take ashe kawarki ce." Little ta kalli Naf tace " Feena d'an uwan namu kike wulakantawa? " Nafi ta kalli Little kamar zatai kuka, yace " wlh ina zuwa na ajiye su Hajiya na dawo dan in kaita gida " Nafi ta harareshi tace "cewa nai zan bika? " Ya kara had'e hannayensa yace " Little please." Little ta juya da sauri ta shige motarta taja tai gaba tana dariyar mugunta. Nafi ta saki baki tana kallan Little cikin mamaki, Al-Amin ya kalleta yace " Cwt Feena da alama dai nid'in nan nine zan kaiki. " Ta juya kai cikin takaici tace " da wayace kazo nan ma. " Yace " Matata tana guri ba dole inzo ba?" Nafi ta kalli agoggon hannunta karfe 8 ga gun duk ba mutane, katseta yai da cewa. " Please Cwt Feenah ki taimaka, ai indai gidansu Little ne na sani. " Nafi ba dan ranta yaso ba ta karasa gun motar ta shiga rai a b'ace, tana shiga ya zuge glass tare da kunna mata AC, itakam kanta ta maida gefe tana kallan waje. Sun fara tafiya shi kad'ai yake mata magana, ganin batada niyyar kulashi yasa yai shiru. A daidai kofar gidan yai parking, a wannan lokacin kuma, Ashraf ya fito kenan zai fita, kallan motar yai cikin mamaki, har zai wuce sai yaga alamar mace ce a ciki, badai Little bace? Abinda yazo mai kenan, hakan yasa ya ja motar yai parking a gefe. Itakam Nafi tazo fita yasa lock cikin mamaki ta kalleshi ya kashe mata ido sannan yace "

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115