Skip to content

Chapter 101

Chapter 101

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,156 words 0 views Progress saved
Download Book

ce tacemai Ashraf. Nan ya koma cikin station din da sauri, can yaga Ashraf zaune kusa da Kabir suna magana, matsawa yai gunsu jiyai Ashraf yace "Yanzu Officer ba yanda za'ayi?" Kabir yace" dolene sai ya biya kud'ad'an nan dan kuwa hakkin jama'a ne." Kawu yai ajiyar zuciya da alama dai ba Ashraf bane nan yai waje. Kabir ya kalli Ashraf ya sa dariya. Shima dariya Ashraf din yai yace " Kb ka tabbatar ka tsareshi dakyau." Kabir yace " karka damu mutumina." Ashraf yazo ya lallaba Umma da Anisa ya kaisu gida, yana fitowa zai shiga b'angaren Mumy ya hango Nafi daga nesa. Ta sha kwalliya sosai da sosai, ya shagala sosai wajen kallanta tana tafe tana lallatsa waya, gani yai kamar ta kara wani irin mugun kyau. Ya shagala sosai da kallanta yaji alamar sako a wayarsa. Nan ya duba, daga Nafi ne, _Yaya zanje gidansu Ferry._ D'agowa yai da sauri dan ya kara ganinta sai dai me? Wayam ya gani ba Nafi. Da sauri ya matso yana nemanta, sai dai bai ganta ba. Gun mai gadi ya nufa da sauri yace " Nafisa ta fita ne?" Mai gadin yace " eh yanzun nan." Ashraf ya leka waje da sauri, yana ganinta ta shiga motar Nabil, jiyai ransa ya sosu sai dai kafin ya karasa fitowa sunyi gaba. Motar yabi da kallo sannan ya juya jiki a sanyaye. B'angaren Mumy ya shiga, tana zaune a falo tana cin abincin rana. Fuska ya daure tamau sannan ya zauna suka gaisa. Ta amsa a hankali tace " kaje gun Asim ne?" Bai amsa tambayarta ba sai cewa yai, passport dinki nake so." Kallan mamaki tamai tace " me za'ai dashi?" Yace " umara zakije kida Nafisa." Tace " Umara?" Ya kalleta yace " garin nake so ki bari, saboda in na barki anan Kawu zai yi tunanin amfani dake wajen tsaidani daga kamashi, sai dai banaji akwai abinda zai tsaidani, shiyasa nakesan ki bar garin in na kamashi sai ku dawo." Kallan sa tai cikin wani yanayi, yace " karkiyi tunanin yafe maki laifinki nai, in kika dawo kema zaki je kuto a miki naki hukuncin." Hawayenta ta maida sannan ta d'aga kai tace " ni naji nawa dalilin amma nafisa fa?" Yace " Tsoro nake kar wani abu ya sameta, duk da na juya mata baya saboda banasan mutanen gidan su damu da ita, amma a zuciyata kullum da ita nake kwana nake tashi, ku tafi tare ko Allah zaisa ma taga mahaifiyarta." Mumy ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " Ya Hisham fa?" Yace " Duk wanda yai laifi dole ne ya karbi hukuncin shi a duniya, shine kadai gatan da zan iya muku." Yana kaiwa nan yai waje. B'angarensu Little ya nufa, dan yanasan ganinta. Daga lungun kofar ya ganta tsaye itada Habib, kasa karasawa yai yatsaya kawai jikinsa duk yai sanyi, ya zasuji in komai ya fito? Ya sani Habib ba wai san Little yake ba amma ita fa? Gata yarinya ya zatai??? ************* Nafi kam Nabil na jan mota yace mata " mutuminki fa ya fito, ina kallansa ta madubi." Murmushi tai tace " share kawai Ya Nabil, shima hidimar gabansa ta mai yawa." Nabil yai dariya yace " ko dai fadan masoya kuke?" Tai dariya tace " ba wani fada, ko dan kaga nace inzaka wuce kazo mu tafi? Wannan ma ai dan naji kana anguwarmu ne." Nabil yai murmushi yace " Feenah Allah nikam Ashraf ya gama kwafsamin, da ya kwaceki." Harararsa tai tace " Ya Nabil ba nace ka daina min wannan zancen ba? Nifa kanwarka ce." Yai ajiyar zuciya yace "ya zanyi tunda an maidani yayan karfi da yaji." Zatai magana taji sako ya shigo wayarta. Ashraf ne hakan yasa ta bud'e da sauri _Wajen karfe 4 za'azo a d'aukeki akwai inda za'akaiki._ Ta dan turo baki tace " ina za'a kaini??? Nabil ya kalleta yace " ya akai?" Tace "bakomai." Shikam Ashraf Dan Litti ya kira ya sanar dashi karfe 4 yaje ya d'auki Nafisa ya kaita inda akeyin passport akwai wani abokinsa daya kira yace suje 4 lokacin mutane duk sun ragu. Dan Litti yace "da alama yau zanga Nafinmu kenan." Nace lalai anfa dade ba'a gamu ba.....Lol😄 *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _Sakonku ya isa gareni masoyana, insha Allah zanyi kokarin kammalawa zuwa sallah, ni kaina nakosa ingama, fatana dai kutayani addu'a Allah ya bani ikon gamawa lafiya...._ *Nagode kwarai!* *79* Da yamma kuwa Dan Litti ya nufi addreshin da Ashraf ya turomai na gidan su Ferry. Nan ya kira Ashraf ya sanar dash ya isa shikuma ya ma Nafi sako akan ta fita wanda zai kaita ya iso. Sunyi sallama dasu Umma sannan ta fito itada Ferry, ganin motar Ashraf yasa ta nufi motar. Dan Litti yana ganinsun iso ya fito sanye da sunglasses, zaresu yai ya kallesu, Nafi kallansa take cikin mamaki shima kallanta yake. Fuska ya hade tamau yace "malama lafiya?" Nafi tace " bangane ba?" Dan litti ya maida glass dinsa ya kalleta yace " Na fada miki bai kamata ki dinga bin mijin dake da aure ba, a kalla dai mutum ya dinga sanin darajarsa." Nafi ta hade rai itama tace " kai kuma a wani matsayin kenan kake sanar dani haka?" Mota ya bud'e yace " malama dan Allah kiyi gaba akwai wacce nake jira ne, tunda kinga ba mai motar bane ai sai ki kara mai." Nafi da Ferry suka kallu juna, ferry tace " ruwa zata kara ba mai ba, sannan kai wanene ma?" Ya kalli Ferry cikin isa yace " The Hand Right of Ashaf." Dariyarsu suka guntse Ferry ta kalli Nafi tace " ke kuma fa?" Nafi ta kalli Dan Litti tace " As his wife." Duk da kalmar taba Ferry mamaki sai dai ta dauka ko dan ta kular da Dan Litti ne yasa ta fadan haka. Idanu Dan Litti ya zaro yace " matarsa? Amma matan Ashraf ai na sansu." Kai ta juya, da sauri ya kira wayar Ashraf yasa a hands free. Ashraf ya daga yace " mutumin ya akai?" Dan Litti ya kalli Nafi yace " wata ce take tutiya wai matarka ce." Yace " wata kamar ya?" Ferry ta fizge wayar ta mikama Nafi. Nafi tace " Hello." Ashraf yace " Nafisa? Ya akai? Kinga Dan Littin?" Kallan juna sukai daga ita har Dan littin. Cikin mamaki tace " Dan Litti?" Shima yace " Nafisa?" Ashraf yai murmushi yace " Da alama baku hadu ba sai yau." ya kashe wayar. Dan Litti tsananin mamaki ya kamashi, kallan Nafi ya shiga yi. Nafi cikin mamaki tace " Dan Littin gayu? Kaine?" Kansa ya sosa yai kasa da kai yace " Hajiya Nafi wannan ko a mafarki naganki akacemin kece ai bazan yarda ba." Dariya tai, Ferry tace " au dama kunsan juna?" Nafi tace " Kauyenmu d'aya." Ferry tai dariya tace " lalai yau akwai hirar gida kenan, ni nayi ciki." Nan ta musu sallama tai gaba. Ashraf ya bud'ema Nafi gidan baya ta shiga. Mamaki har yanzu bai barsu ba. Ya ja mota yana tambayarta ya akai bai taba ganinta ba? Tace " wai da gaske a nan gida kake? Nima ban taba

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115