Skip to content

Chapter 69

Chapter 69

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,181 words 0 views Progress saved
Download Book

rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan." Nafi ta ture hannunta tace "naki na gwada din." Ferry tace "shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada." jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada. Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne. Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya. Nafi tace "wai ina zamu?" Ferry tai dariya tace "sirri ne." Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d'au wayar tai waje. Nafi ta tabe baki tace "ferry kenan uwar soyayya." Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi. Nafi tai dariya tace "lalai to ke yaushe zaki shirya?" Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma. Nafi tace "Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?" Ferry tai dariya tace "sauko." Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad'aba ta mike a hankali suka sauko. Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya. Nafi tai godiya suka sauko. Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa. Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace "Me kakeyi anan?" Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace " Ba Ashraf bane?" Kallan mamaki Ashraf yamai yace "nine...Amma???" Baba yace " me kake anan?" Ashraf ya kalleshi yace "a ina kasan ni amma?" Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace "na ganka a magazine ne." Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida. Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai. Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya itama, ferry tace "muje mana sanyin ranki ne." Nafi ta kalleta tace "ya akai yasan gidan nan?" Ferry ta nuna kanta da hannu, tace "kina wasa dani ko?" Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d'auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?" Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d'ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad'an shagwab'e fuska. Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace "yaya ni zan koma." Ashraf ya kalleta yace "Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici." Dariya tai tace " ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya." Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d'auko wallet dinsa ba?" Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace "karki damu zan kawo tukuicin daga baya." Tace "ba komai yaya." Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, "ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan." Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace "muje ko?" Tad'an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace " bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba." Ta kalleshi fuska a shagwab'e tace " me nai da za'amin fada?" Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata " Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina." Itama a hankali tace "Name fa?" Yace "nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba." Idanu ta lumshe sannan tace " nifa ba yau naso komawa ba." D'agota yai yace " kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?" Kallansa tai tace " ni kam ban saba da zancen miji ba." Ya matso da bakinsa kuncinta yace " ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d'in nan?" Idanu ta zaro da sauri tace " a'a bance ba." Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d'ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace "Allah ka d'auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin." Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace " b'angarena zamuje." Idanu ta zaro tace "muyi me?" Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace "uwar tsoro abu kawai zan baki." Tai murmushi batace komai ba. Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b'angarensa yace "ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d'aki." Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya. Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita. Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace "kwanta." Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d'an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin. Ashraf fuskarta yake kallo yace " gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?" Kai ta d'agamai fuskarta d'auke da murmushi. Idanu ta bud'e a hankali tace " na d'agama hankali da baka gan ni ba?" "Hmm, ban taba zatan zanji haka ba." Tai murmushi tace " I can't help dole ne in sake guduwa wani gun." Harararta yai ya had'e rai yace " in kika sake gwadawa zakiga b'acin raina da baki taba gani ba kuwa." Ta turo baki tace " sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba." Hararata yai yace " ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina." Tace "mekenan?" Yai furzar da iska yace "bazan iya fada ba." Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah. A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud'e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d'an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare. Da sauri tace " Yaya." A hankali yace "Uhmm." Tace "Abba hatsarin mota yai ko?" Kallanta yai yace "eh." Tace "kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?" Yace eh. Tace " Motar Abba alokacin an duba meya jawo

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115