Chapter 9
Chapter 9
" D'an litti ya had'iyi miyau yace " Kai Ashraf gaskiya she is beautiful. " Ashraf ya sakeshi tare da mikama Datti rigarsa yace" mu zamu wuce. " Datti kam sam ya kasa magana, kallan Nafi yai yace " muje ko? " Kallan mamaki tamai dan ita batasan shine mijin ba lokacin kanta ma kasa sai dai ta kasa mai musu nan ta kalli Datti tace "Baba mun wuce. " "Ah to shikenan, sai munzo ganin gida, d'an litti ya kawo mu. "datti yai maganar yana kalle kalle. Nafi tace to. Maman Hanne ta mata sallama sai dai ganin yanda Hanne ta hade rai yasa Nafi ta juya ba tare da ta mata magana ba. " Sunanan tsaye har suka hau mashin, nan suka nufi hanyar Gwaram inda zasu hau mota. ******** Sunyi tafiya sosai kafin su isa, nan D'an litti yakaisu inda zasu shiga mota, wata karamar golf suka samu D'an litti jiyai Ashraf yace " Shata muke so. " Dasauri ya jawo rigarsa yace " Ashraf kasan me kake fad'a kuwa? Inkace shata yana nufin fa ku biyu za'a kai har kano kaga kuwa zaka biya money panty. " Ashraf yai d'an murmushi yace " meye kuma panty? " D'an litti yace " Kudi dayawa nake nufi. " Kafadarsa Ashraf ya dafa yace " Plenty ake nufi. " Yana kainan ya wuce gun driver yace " Muje ko? " Nafi ce ta kalleshi sanda taga ya bud'e mata bayan mota ta shiga, ya dawo inda yabar D'an litti a tsaye kamar gunki ya ciro dubu uku ya bashi yace " Nagode sosai d'an litti Allah ya karama ilimi. " Kallan kudin yai yace " Ashraf ina zan kai kudin nan? " Murmushi yamai sannan ya mikamai wata dubu d'ayan yace " ka ba abokinka. " Ya juya ya nufi motar, tsayawa yai yana tunanin ko dai yabada number wayarsa in case ko iyayenta zasuzo Kano? Kai ya girgiza alamar a'a lalai dole ne ya koya musu sanin darajar yarinyar nan, dan ya kula zaman dasuke tare da ita ne yasa ba wanda yake ganin darajarta da mutuncinta. Shima bayan motar ya shiga, Nafi kam tana zaune duk jikinta a sanyaye, bata taba shiga mota ba sai yau, sai dai taitajin labarin agun Hanne yau gataa ciki, Driver ya tada mota. D'an litti ne ya matso da sauri ya turo kansa ta window yace " Nagodee Ashraf sannan yanzu na rike plenty ko? " Ashraf ya mai murmushi yace " kana burgeni ta yanda kake kokarin yin turancin nan, Allah ya hada fuskokinmu da alkairi. " Murmushi sukama juna D'an litti ya dagamai hannu yace "Sai munxo gidan ka. " Kai ya daga nan mota ta ja suka fara tafiya.......... Sun danyi nisa a hanya kad'an Ashraf ya kalli Nafi sannan yai gyaran murya, d'agowa tai ta kalleshi da idanunta, Yad'an mata murmushi sannan yace " Nafisa? " Gabanta ne ya fad'i jin ankirata da cikaken sunnanta, sai dai bata amsa ba sai dai hankalinta data tattara zuwa kansa. Ashraf ya cigaba " ki nutsu zamuyi magana mai mahimmanci ne. " Ta d'aga kai alamar tanaji. Ashraf yadanyi ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa bazan miki alkawarin so ba, ba kuma zan miki alkawarin kulawa ba sai dai zan miki alkawarin ni Ashraf bazan taba bari ki wulakanta ba. " Kanta na kasa sai dai gaba daya gabanta har yanzu bai daina bugawa ba, ya cigaba " Na aureki ne domin ceton rayuwarki daga gun mutanen nan da babu imani a zuciyarsu, sai dai inaso ki kama bakinki kamar yanda nima zan kama. " Dagowa tai cikin mamaki ta kalleshi yace " kada ki kuskura ki fadama kowa na aureki, wannan sirri ne a tsakaninmu ni dake, karki fadama kowa wannan shine abinda zai kareki." Idanunta ne suka fara cicikowa nan ta shiga kokarin maidasu, kai ta daga mai alamar ta fahimta, Ashraf ya cigaba " Nafisa zan ajiyeki a gidanmu har Allah ya kawo miki wanda kike so shima yake sanki, in kun aminta da juna sai in sauwake miki ki aureshi......... " Kallan datamai ne yasa yai shiru shima, me kenan? Abinda zuciyarta ke raya mata kenan? Wani irin aurene a ranar aurenta ake mata zancen saki???? Ashraf yadan juya kai sannan yace " Bazaki fahimci me nake nufi ba yanzu amma na sani nan gaba zaki gane, a inda zamuje zakiga zuciyoyin mutane iri iri sai dai inaso ki daure ki zauna da kowa a yanda yake. " Nafi wanda hawaye yake yawo a fuskarta tai saurin jan mayafi ta tarufe fuskarta, kallanta yai sai dai ya za'ayi? Dole ne ya fadamata gaskiya....... Nafi tai shiru sai dai tunanin dake zuciyarta yawa garesu sai dai tasan abu d'aya dama, tabbas Dan binni ba santa yake ba taimakon ta kawai yai kamar yanda ta taimakeshi, tana ta tunani har bacci yai awun gaba da ita. Ashraf kam yayi shiru yana tunani, tabbas motarsa lafiya kalau ya ajiye ta, to amma mezai sa lokaci daya burkin motar yakiyi? Girgiza kai yai da sauri yace " zato zunubi, ikon Allah ne. " *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 8⃣ Bakin wani katon gida Ashraf yace mai yai parking, daga bakin gate din mutane ne sosai a tsatsaye sannan wasu dauke da speaker da cameras hakan yasa Ashraf yasan 'yan jarida ne a gun, kallan Nafi yai wacce ke zaune yace " Nafisa kin gaji ko? " Kallansa tai sannan ta girgiza kai alamar a'a, ya dan murmusa sannan yace " mun iso. " Ta kalli waje ganin mutane yasa ta kalleshi, ya bud'e motar ya sauka sannan ya zaga ya bud'e mata, a hankali ta fito jikinta duk a sanyaye, ya kalli driver d'in yace " bari in kawo ma kudin ka. " Ya amsa da to, juyawa yai ya fara tafiya, bai karasa gun mutanen ba kawun sa wato kanin babansa ya hangoshi cikin tsananin mamaki da farinciki ya taho da saurinsa, kusa da Ashraf ya tsaya yama kasa magana sai dariya kawai da yake ya kankame hannun Ashraf, mamakin da ya kamani banga Ashraf yana farinciki sosai ba sai dai yace " Kawu na tada muku hankali ko? " Wanda ya kira da kawun ya gari fadada murmushinsa yace " Ashraf duk mun daga hankalinmu ganin jiya a rafin wudil muka wuni cur ana nemanka an rasaka tsoro yasa muka fara tunanin ko ka cika sai dai mahaifiyarka taki yarda sam tace lalai kana nan da rai. " Yad'an yi murmushi kadan sannan yace " Bari na shiga ciki, sannan dan Allah aba mai mota kud'i." Kai ya daga mai cikin farin ciki, Ashraf ya juya ya kalli Nafi dake tsaye yace " Mu shiga ko? " Kallanta kawu yai saidai baice komai ba, Nafi kam a hankali ta karasa inda yake, nan suka fara tafiya, hannu kawai ya dagama 'yan jarida suka nufo inda yake, bai jirasu ba ya nufi gate, ya shige ciki. Inalilahi abinda Nafi ta fada kenan a fili, wani tafkeken gida ta gani, ba wai haduwaa kad'ai ba gida ne kato flat flat dayawa, in ka gani zaka dauka ko gidan hayane na masu kud'i sai dai Ina gida ne na Marigayi Alhaji Saminu wato
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115