Chapter 3
Chapter 3
ake cewa ba. Tana idarwa ta matso kusa da dan birni, kansa takai hannunta sai dai da sauri tadauke hannunta jin wani mugun zafi datai, Mikewa tai da sauri tace " Hande inboni!! Karfa kad'on nan ya mutumin adaki in shiga uku?" Dasuri tai waje ta shiga lelekawa, abin haushi a can gefe suke wanda inzakaje rigar kusa dasu sai kayi tafiya mai dan yawa, gashi tana tsoron mahaifinta kar ya dawo yaga ba tannan. Komawa tai ciki, ta nufi d'akin baffa nan ta shiga duba gayayyakin magani ko zataga na zazzabi, tai sa'a kuwa ta samu nan ta sato rigarsa ta fito daga dakin, wuf ta shige d'akin ta. Tofa nan ake yinta gani take jikaken kayan dake jikinsa ne ya jawo mai zazzabin nan, shiyasa ta dauko kayan baffa, to amma taya zata ciremai kayan dake jikinsa ta samai wannan? Tsayuwa tai akansa tai tsuru tsuru da ido tana tunani, maganin ta dauko ta jika a kofi sannan ta matso kusa dashi ta shiga bashi a hankali da cokali, wani yana shiga bakinsa wani kuma zubewa yake. Bayan ta gama ne ta kalleshi cikin kalaar tausayi tace ya zanyi dake? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 3⃣ Duk ta rud'e ta zauna kusa dashi tare da daura hannunta akan goshinsa, tsoro da fargaba ne suka cika mata zuciya jin yanda jikinshi yai zafi dauuu. Yawo ta had'iya sannan tace " bazamuyi ta zama a haka ba d'an birni kiyi hakuri bazan kalleki ba, zan cire miki riga idanuna a rufe, kinji?" Tana fadar haka ta ajiye rigar Baffa a kusa da ita ta matso kusa tare da rufe ido, irin rigarnan mai dogon hannu da kwala ce, sai botir dake jikin rigar daga sama har kasa, nan ta shiga b'allewa idanunta na rufe tana yi tana magana, "yanzu kaga bana kallanka, sannan namaki laifi guda biyu, na farko nasa bakina a naki sannan yanzu ina cire miki rifa, sai dai inaso karki manta wallahi ba asan raina duk nai hakan ba, banaso ne ki mutu kinji?" Tana kainan ta shiga kokarin zare rigar, jin ta kasa zarewa yasa ta manta ta bud'e idanunta kallansa ta shiga yi, sam ta manta, yauce rana ta farko data tab'a kallan jikin namiji dan kaninta tun daya tasa mahaifiyarsu ta raba musu d'aki, ita ba gurin wasan shad'i ake barinta taje ba, nan ne dai tasan maza basa sa riga sai wando, to ita inama take zuwa banda ta mika nono da madara cikin gari inda mahaifinta yake saidawa, dan rashin yadda irin na datti bai yadda ace wani yasai da mai abu sai dai shi dakanshi, nan shago ya bud'e yake saida madara da nonon shanu. Ganin yanda gabanta ke fad'uwa yasa tai saurin rufe idanunta sai dai wannan karan ta guntse bakinta gum, haka tasamai riga sannan ta fito waje da sauri. Sam bata kula da Baffa dake zaune akan tabirma ba, ta tsaya a waje tare da rik'e inda zuciyarta take, a tsaye take kamar gunki, jitai ance " Wato Nafi kin fara zarewa ko?" Dasauri ta kalli inda maganar ta fito, Baffa ta gani a zaune, hannunta ta zare cikin tsoro ta kalleshi tsoru tsuru tace " Baffa.." " Inajiyoki daga d'aki kina magana ke kadai wato zama ke kadai a gida yasa kin fara zarewa ko? " Tai kasa dakai cikin tsoro batace komai ba, baffa yai tsaki sannan ya juya kansa yace " damomin fura insha dare nayi." Cikin rawar murya tace " to Baffa yauma bazamuci abinci ba......" Katseta yai cikin masifa yace " Inkin gaji dashan fura da nono kiyi zuciya kiyi aure, nifa banga dalilin dazaisa yarinya kin kai aure incigaba da ciyar dake ba, sannan haka kawai inada shanaye dayawa bazanje insai abinci ba ah to." Nafi bata amsa ba ta juya dan shiga d'akin dasuke ajiye fura, nan ta debo, ta d'ebo nono a kwarya ta zauna ta dama, itakam yanzu warin nono ma yafara damunta, tunda uwarta tabar kasar nan kullum abincin da suke ci kenan, sam Baffa ya rufe ido ita kuma tasan inya fita shago yana siyan shinkafa yaci amma ita kullum abinda takesha kenan. Tana gamawa ta zubomai a langa ta rufe ta daura ludayi ta kawomai, sannan ta dauki nata tai d'aki, kallan mutumin dake kwance tai, tace " Nasan kaima yunwa kake ji ko?" Matsawa tai ta kara tab'a goshinsa, da zafi har yanzu, nan ta matsa kusa dashi ta dan dagoshi kadan tasa kafarta ta tareshi, ta dinga deban furar data dama tana bashi a hankali da cokali, wani yasha wani ya zube, ganin yadan sha dayawa yasa ta mik'e jiki a sanyaye ta zare zanen data shimfida na saman ta goge mai jikinsa sannan ta dauke numfashinta itama tasha, dan sam batasan sha. Waje ta fito da kwaryar sannan ta koma ciki tare da tura kofarta ta rufe, kusa da mara lafiyar ta koma ta zauna, ta hard'e cinyoyinta kallansa kawai takeyi, sai dai tunaninta nakan mahaifiyarta, a haka har bacci yai awun gaba da ita. Wajen gabanin asuba ya bud'e idanunsa a hankali, yarinya ya gani kwance kusa dashi ta dan dukunkune jiki tana baccinta, kallanta yai sannan ya shiga kallan dakin, mamaki yashiga yi a ina yake hakan? Yadauka ya mutu shikam, Nan ya shiga juye juye, tare da kallan d'akin dakyau "wannan kuma inane hakan?" Gashidai kamar d'aki sai dai gaba daya baisan dame akai rufin dakin ba, sannan ba komai a dakin banda ta birmar dayake kai sai gefe kuma bakko da 'yan samiru, kokarin mik'ewa ya fara sai kuma yaga kamar yarinyar tana neman tashi, dasauri ya maida idanunsa ya rufe. Nafi ta mik'e zaune tare da sa hannu akan goshinsa, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jin zazzabin yaragu sosai, ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace " Zazzabin ya ragu aradu, dan binni ya kamata ka farfado ko na samu in baka hakurin abinda nai maka." Tai kasa dakai tana murmushi tace " kaga sanda na sa bakina a naka a bakin ruwa wannan taimakon ka nai. " Shikam dake kwance jiyai kamar yasa ihu, bakinki? Yamaimaita a ransa, wayyo ni. Tacigaba " sanda kuma na cire maka kaya har tsautsayi yasa na kalleka wannan shine zan baka hakuri, bansan me yasa na kafeka da ido ba. " wayyo na shiga uku, kallon jikina? Ciremin kaya? Inalilahi, hannu wa na fada haka? Ba dai har wando tacire............? Jiyai ya kasa tunanin komai saboda tsoron abinda yake tunani. Nafi ta mike jin mostin baffa tasan yanzu zaice ta tashi tayi tatsar madara, ta mike hartaje kusa da kofa ta juyo tace " kema kina shan madara? " Sai ta juya tana murmushi. Tana fita ya mike zaune da sauri ya duba wandansa, ajiyar zuciya yai a sanda yaga wandansa nannan ya koma ya kwanta yana hakki kamar wanda yai gudu ba shakka ya tsorata kwarai, tunani ya shiga yi ya zaiyi yai alwala yai sallah? Muryar namiji ne ya katseshi yaji yana cewa " ke nafi? Ke Nafi. " Saurin amsawa tai daga garke tace "Baffa ganinan. " Ya kalli inda take yace " Dan gidan ku jiya bance ki karo wa dabobbi ruwa ba?? " Ta dan matso inda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115