Chapter 37
Chapter 37
muyi? " Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina." Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya, amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba, kallansa tai idanunta suka ciciko, ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi. Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. " Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? " Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka." Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka." Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please." Bai kulata ba ya cigaba da tafiya, sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf. Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri. Kallan mamaki ta musu, Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? " Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? " Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? " Yace " ehen sai me? Abun haramun nai ko me? " Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana, Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? " Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu. Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki. Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya, sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? " "Kan jakar uba, abinda za ka tambayemu kenan? " Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. " A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? " Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce? Waccan yarinyar? " Umma ta kumbura kam, yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata." Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka? Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? " Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa da take kuka, matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. " Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? " Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi? Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan." Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi, tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito, kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? " Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa, zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi. Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. " Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake? Ita har takai in mata magana taki tahowa? " Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... " Cikin fada yace " amma me? Ba ki yadda dani ba ko me? " Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. " Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?" Tace " ba komai kawai dai dama. " Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to, in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. " Nan ya fara tafiya, Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri. Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba. Kan Nafi suka dawo a zuciye, gashi Habib ya tafi, duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi. Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan. Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me? Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi, Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. " Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. " Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka, jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take? Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? " Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa, Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. " Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy. A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya, ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. " Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. " Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai, sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi, fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol* { *31*} Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu. A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan." Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba." Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata. Little ta d'au waya ta kira Ashraf, sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga tace " Yaya." Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? " Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115