Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,155 words 0 views Progress saved
Download Book

Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake, ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?" Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su, cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka? Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani bare. " Ran Asim ne ya kara dugunzuma, yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu, Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya? Gatannan sai ka tambayeta me baren nan ya mata. " Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba? Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai? Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......" Kasa karasawa yai saboda ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut! Dariya ma na baka? " Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? " Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?" Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri, tana kiranshi. Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? " Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa. Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje. Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna abinda likita yace mai. "Ashraf a ina ka bugu haka? " Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min." Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? " Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. " Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? " Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, sannan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. " Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. " Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. " Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira. Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo. Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. " Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo. Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. " Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? " Little tace " naji muryar yayan ma kamar......" Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan. Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne? Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. " Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita. Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama, jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki, baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi. A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri, a hankali tace "Yaya ga...... " Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. " Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... " "Little wuce mana" Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake, nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito, ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin, kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba, idanunta ne suka fara cicikowa, ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun, dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an. Kamar a jikinta takejin ciwo nan, intaga ya motsa sai ta runtse ido. Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule. Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki, me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai??????? Tofah! Babbar magana........ ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako, kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai. Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram..... ¤¤¤¤¤¤¤ Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi. D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. " Officer yace " Ashraf wa? A ina yake? Meye number wayarsa? " To fa! Da masifa D'an litti yace " nidai ba na fada muku ba? Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. " Officer yace " me kake nufi to? So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me?

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115