Chapter 43
Chapter 43
ciki zan shiga." Cikin rashin damuwa Asabe ta bata tare da kad'a kanta ta koma inda ta fito, Nafi kam da sauri ta nufi kofar Umma, gabanta kam sai dukan uku uku yake saboda tsoro sai dai ta rasa dalilin dayasa zuciyarta keta tunzurata akan lalai ta shiga. Murd'a kofar tai a hankali ta shiga da sallaha itama ciki ciki tayi ta. Batai mamaki ba dan dama batasa a ranta za ta gansu a falo ba, nan ta wuce cikin tsoro ta ajiye tiren akan dinning sannan ta kalli d'akunan dake falon guda biyu, a ina suke???abinda ta fad'a kenan a ranta. Lalab'awa tai ta karasa d'akin farko,tare da sa kanta a jikin kofar kamar munafuka, jin alamun rashin mutum yasa ta karasa d'ayan, zuciyarta sai kara tsananta take da fad'uwa wannan karan bata sa kanta a kofa ba tana zuwa jikin kofar d'akin taji cikin fad'a wanda yasa ta tsorata taji Muryar Asim yace " Umma nikam bakin ciki kasheni zai yi dan nikam indai har na cigaba da ganin Ashraf to fa lalai inaji ni zan bar gidan nan." Gaban Nafi ne ya yanke ya fad'i me kenan? Ta fad'a a ranta. Kafin ta nemo amsar tambayarta taji Umma tace " ni d'in ce maka akai farin ciki nake in na ganshi? To amma ya zakayi....???" Cikin fad'a Asim ya katse Umma da cewa " Yanzu sam 'yan gun aikinmu basa karramani magana ma ba yimin suke ba, sannan yanzun nan abokina na gun aiki ya sanar dani cewa shareholders na company d'in sun yi meeting akan a dawo da Ashraf matsayina inyaso ni sai a ragemin matsayi, nifa wlh in bakuyi wasa ba zanyi aika aika." Umma ta gyara zama tace "Asim kayi hakuri abi maaganar nan a hankali." Cikin zafin rai yace. " a hankalin me? Ni wlh har yan daba na kira kafin nazo nan na sanar dasu inya fito aiki anjima su tareshi su kawar mun da numfashinsa." Jikin Nafi kam rawa kawai yakeyi, har tsuma takeyi saboda tsananin tsoro da fargabar abinda yau kunenta yake jiye mata. A tsorace ta juya cikin tsananin tsoro da firgici tai waje har kafarta na hard'ewa ta fad'i kasa. A d'aki kam Umma ta kalli Asim tace " Asim yau lahadi naga ba aiki?" Asim yai wani murmushi yace " ai shi zai je saboda akwai wani project da sukeyi shi da 'yan team d'insa." Umma tai ajiyar zuciya sannan tace " baka ganin anyi gaggawa in aka mai illa tun yanzu? Asim yai tsaki yace " Illar me? Shima Abban ai yafi kowa san Ashraf ya mutu." Umma ta jinjina kai sannan tace " Aneesa fa?" Asim ya kara jan tsaki yace " kyale wannan in ya mutu taji ta cafki dukiyaa a hannu kina ganin zata damu?" Umma tai murmushi sannan tace " duk da Neesa na tsananin san Ashraf banaji tana sansa kamar yanda takesan kudinsa dan na tabbata da bashida komai duk sanda takemai bazata tab'a aurensa ba." Asim yai kwafa yace " Ni wlh na tsani ma na gansu tare, nifa inaji duk duniyarnan ba wanda na tsana kamar yaran nan." Umma ma tai tsaki tace " ai nima dashi da uwarsa sune mutanen dana tsana kaf duniyar nan." Nan suka zauna suka cigaba da sake sakensu. Nafi kam dakyar takai kanta falon b'angarensu, ta zauna akan kujera har yanzu jikinta rawa yake, sam kwakwalwarta ta kasa d'aukan abinda ta jiyoma kanta. Dif taji kwakwalwarta ta d'auke sam bata tunanin komai sai da wasu dakiku suka shud'e sannan taja wani dogon numfashi sannan ta mike a zabure tace " Ya Ashraf????" Jitai idanunta sun kawo kwalla ace d'an uwanka na jini???wannan wace irin rayuwace???? Sanar dashi zatai?? Zai yarda da abinda zata fad'a??ko Little zata fad'ama??kai ta girgiza tace"kar itama in tada mata hankali..." Wata zuciyar tace Mumy fa???kai ta girgiza da sauri tace " Mumy kuma da wani idan zata zauna dasu??" Kanta ta dafa dataji ya sara, can tace " Kawu fa???" Hucci ta saki cikin damuwa tace " shikuma matarsa ce da d'ansa." Kan kujera ta fad'a wasu hawayen suka sake zubo mata, Ya Ashraf me kai ake neman halakamin kai???ta fad'a cikin wata irin murya mai ban tausayi. Agoggon bango ta kalla karfe tara, karfa Ya Ashraf ya fita??? Da sauri ta mike kawai ta nufi b'angarensa, hankalinta bai tsaya ba sai da ta isa kofar b'angarensa, me zata cemai??? Shiru tai ta tsaya agun kamar abu mara motsi, dan batada amsar tambayar nan. Tana tsaye ba mafita har dakika goma suka shud'e, motsin bud'e kofa ne yasa ta dawo hayyacinta, idanunta ne suka firfito cikin tsoro, ta kalli kofar. Ashraf ne ya fito, jitai gabanta ya fad'i cikin mamaki ya kalleta, sai dai kafin yai magana sai ga Aneesa ta fito rike da jakarsa, fuskarnan tata a had'e da alama ranta a b'ace yake. Cikin mamaki itama ta kalli Nafi, "Malama wacce ce ke? Me kuma kike anan?" Nafi ta had'iye yawo cikin tsoro ta kalli Ashraf, shima kallan mamaki yake mata, Aneesa ta kara kallantaa yanzu kam kallan rashin mutunci ta mata. Tace " Ke malama wacece ke? A wani dalilin kikazo min kofar miji??" Nafi kam jira take Ashraf yai magana sai dai abin haushi gani tai ya d'auke kansa, tare da amsar Jakarsa zaiyi gaba, jitai idanunta sun fara cikowa ita gani take ai ya kamara Ashraf ya sanar da Aneesa, ganin ya fara tafiya ga tana so ta tsaidashi daga fita waje, sannan ga Aneesa ta tsareta da ido yasa duk ta rikice. Shikam Ashraf haushin abinda tai jiya da daddare ne yasa yaki kulata, Aneesa ta bud'e baki zatai magana kawai Nafi tai baya luuu jikake ta zube a kasa, wannan ita kadai ce mafita a gareta abinda ta fad'a kenan a ranta tare da runtse ido. Aneesa ta d'anyi kara tare dayin baya cikin tsoro, hakan yasa Ashraf ya juyo da sauri, cikin rud'ewa yasa ya karaso inda take, sannan ya d'agota tare da cewa " Nafeesa!!Nafeessa!!." Sai a lokacin Aneesa ta gane waccece, kallan Ashraf tai duk ya wani rud'e haushi da kishi suka kamata a zuciye ta matso tace " Aljanu ne da ita??" Ran Ashraf ya b'aci ganin yanda tai maganar cikin rashin kulawa, yace " bishiyar kuka ce a kanta..." Ya mike a zuciye ya d'agata ya nufi mota da ita, Nafi kam haryanzu gabanta bai bar fad'uwa ba tanaji ya bud'e bayan mota ya sata a ciki. Tanaji ya bud'e gaban mota ya shiga, ya tadata tad'anyi zafi sannan yaja motar suka fita, suna fita daga gate d'in gidan sai taji yace " Will u get up now?" Idanunta ta kara runtsewa a ranta tace " badai dani yake ba?" Ashraf ya kalleta ta madubi sannan yace " abinda kika koyo a makarantar kenan? Pretending??" Nafi kunya da takaici duk suka kamata ta kara danna kanta kujera, gefen titi ya gangara yai parking sannan ya juyo ya kalleta yace " Kin tashi ko sai na fitar dake waje da kaina?" Nafi ta mike zaune tare da zunburo baki gaba kanta na kasa, ya kura mata ido yace " me kike san fad'amin?" Kallan mamaki tamai, tace " ya akai kasan abu nake san fad'a?" Kallanta yai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115