Chapter 87
Chapter 87
kuma? Sai ya tuna da Anisa, hakan yasa yai shiru. Kallanshi tai tace " ya kamata in daura mana abinci sai dai naga ba komai a gidan na girki." Yace " hmm kayan abinci ba matsala bane sai dai da alama kin warke, kar anjima azo acemin baza'a iya abincin ba bayan an siyo, a nemi sani a kitchen." Dariya tai sannan tace " ko na saka a kitchen din ai bana tunanin akwai abinda zaka iya dafawa." Yace " akwai abinda zan iya dafawa mana." Cikin zumudi tace " haba? Mene? Fadamin dan Allah." Dariya yai sannan yace " matso in rada miki." Da sauri ta kai kunnenta saitin bakinsa, ya jawo kunnen da hannun harsai da tadanji zafi sannan yace " kinasan ji?" Kai ta daga alamar eh, yace " ruwan zafi." Yana fada ya mike yana dariya. Leb'enta ta ciza tace " YaYa." Ta fada cikin fushi. Dariya yasa mata tare da yimata gwalo. Mikewa tai dasauri tana dingisawa ta bishi kafarta ya nuna yana mata dariya. Nan ta kara sauri dan kamoshi. Dariya sosai yake mata ya shige d'aki, itama ta bishi nan suka fara zagaye gado yana tsokanarta wai Nafisa Cogal, ganin ba yanda zatai ta kamashi gashi ta gama kuluwa yasa tace " wayyo kafata." Ta fada tare da durkusawa. Da sauri ya matso yace " Nafisa menene?" Cafkeshi tai tace " wacce Cogal din?" Dariya yai ya jata suka fada kan gadon, dariya suke sosai dukansu kafin daga bisani su tsagaita. Matsowa tai ta daura hannunta kan kirjinsa tana kallansa tace " yaya inaji farin ciki zaimin yawa, ina tsoro kar ya yankemin lokaci guda." Kallanta yai cikin kauna yace " Baby tun da nake, bandai san kafin Abba ya rasu ba sai dai a iya tarihin rayuwata yanzu ne nasan me ake nufi da farinciki, me ake nufi da dariya, me ake nufi da tsokana, me kuma ake nufi da so, Nafisa ban taba tunanin zan yi experiencing wad'annan emotions din ba, sai dai yanzu jina nake kamar yaro dan sha takwas, akanki gani nake zan iya komai." Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya harareta yace " karki soma min kuka please dan banasan kuka ko kadan balle daga wacce nake tsananin kauna." Batasan sanda hawaye ya zubo mata ba, ba shakka bata taba tunanin akwai ranar da zatazo wanda Ashraf zai sota haka ba, kallanta yai tare da kankance ido yace "na dauka nace banasan kukan nan?" Ta share hawayen da hannunta tace " yaya akwai hawayen da suke zubowa in har farinciki ya musu yawa, in har kaga nayi kuka to yanzu akan abu biyo ne, ko dai farin ciki yamin yawa ko kuma kai nakema kukan da zuciyarka ta kasa." Kallanta ya keyi cikin tsananin kauna, kanta ta kwantar akan kirjinsa tace " in har zuciyarka na maka radadi akan wasu al'amuran ni zan ma kukan da zai sanyayata, dan nasan kai bakasan kuka ko kadan." Idanu ya rufe batare da yace komai ba. Tai murmushi itama. Ya bud'e ido a hankali sakamakon wani idea data fado mai, kallanta yai yace " Nafisa duk abinda zan aikata a wadannan lokacin inaso ki kauda kanki, ki kuma yafemin a hankali zan sanar dake dalilin da yasa nai komai, sai dai inaso ki sa a ranki ni Muhammad Ashraf mai san Nafisa ne." D'agowa tai ta kalleshi ba tare da dogon nazarin kalamansa ba ta matso ta sumbaci goshinsa tace " nima inaso kasa a ranka ni Nafisa mai tsananin kaunar Ashraf ce a koda yaushe." Rungumeta yai wani sanyi na ratsa zugakan mutane biyun, sai dai Ashraf yana saka plan dinsa da zai fara gudanar wa. Nace hmmmmmm ************ A b'angaren Mumy kuwa tun bayan tafiyar Nafisa data shiga daki ta dade tana kuka kafin daga bisani ta kwanta. Juyi kawai takeyi san tunani sun taru sun mata yawa akanta. Tana nan a d'aki har yamma kawu ya shigo d'akin ganin bata falo. Kusa da ita ya karaso yana tsaye yace " Hajiya me ya sameki? Naga na dawo bakyanan sannan na shigo banga kin mun sannu da zuwa ba." Ba tare da ta kalleshi ba tace " kaina ke min ciwo." Cikin rud'ewa ya matso tare da cewa kinsha magani? Ko zamuje asibiti?" Kallansa kawai takeyi ba tare da tace komai ba, ya kalleta cikin mamaki yace " menene? Naga kin kuramin ido?" Idanunta ta dauke daga kansa tare da girgiza kai tace "ba komai." Ya karasa kan madubi ya d'auko magani sannan ya fita dan dauko ruwa. Kalli ta bishi dashi wanda ni kaina ban fahimci kallan me take mai ba. Bai dade ba sai gashi nan dauke da ruwa ya nemi d'agata nan tace zata iya tashi, ta mike ta amshi maganin tasha sannan ta kwanta. Yace " bari in fita naga kamar kinasan hutu." Kai ta daga kawai hakan yasa yai waje. Yana fita ta share wasu kwalla da ni kaina ban fahimci kwallar ta menene ba. *********** Datti kam sam ya kasa magana, banda Mairo Allah ya isa ba kalmar da take fitowa daga bakinsa, an kaishi gurin malamai harda yan duba sai dai haryanzu ba sa'a duk hayakin da akemai kuwa, abinci ma sam bayaci sai dai ai ta duramai kunu. Yana zaune kamar gunki sai kalmar Mairo Allah ya isa kawai dayake fada. 'yan gidan ba wanda ya damu dashi banda yayansa guda d'aya. Datti kam duniya ta juyamai baya.......... Mairo ko tana ina??? Abinda ya fado min kenan. *Juma'at karem* *#ASHRAFEENAH TEAM* *one love💞* 🤸🏻♀ *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Wannan shafin sadaukarwace ta musamman gareku 'yan Xahra Bukar Novel, nagode kwarai da gaske da kaunar da kukemin da littafaina.........ILYSM😍* *69* Da yamma Dan litti ya kawo mai mota, bai bari ma sun gaisa ba makullin kawai yaba mai gadi ya juya yai gaba. Suma wajen karfe 6 suka fito daga gidan, hannunsu rike da juna, tana dan dingisa kafa kadan kadan. Tuki yake zuciyarta nata sarka masa abubuwa kala kala, Nafi kam ganin haka yasa ta kwanta kawai batace komai ba. Sunje shiga gida ya zaro Atm daga wallet dinsa ya mika mata. Kallansa tai tace " Name nene?" Yace " nasan akwai abinda kike bukata sai kuje ke da Little, sannan ki barshi a gunki incase in akwai abinda zaki bukata nan gaba." Kallan mamaki tamai tace " nan gaba in zan nema ba sai na fadama ba?" Kansa yad'auke baice komai ba. A karamar purse dinta ta saka suka shiga gida. Sunje gun ajiye mota sukaga Anisa da su Umma a tsatsaye sai masifa akeyi, ga Asim nan ya rike kofar motar Anisa shima yana fada. Tunda suka kula da motar Ashraf sai duk suka zubama ma motar ido kowa fuskarnan a murtuke, Nafi kam yau ko a jikinta jitake yanzu bazata iya jurar wulakancin kowa ba. Ashraf na tsayar da motae ya bud'e da sauri tare da kallansu, kafin yai magana Anisa ta matso a harzuke ta cakumi wuyan rigar Ashraf kamar zata fashe saboda tsabar masifa tace " Wlh Yaya yau sai ka zaba ko ni ko wannan yar iskar, har ni zatacima mutunci d'azu? Sannan yanzu ka dauketa kun tafi yawan iskanci, wlh da so nai in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115