Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,131 words 0 views Progress saved
Download Book

zatai kuka sai kuma ta daure tace " a'a kaya zai sa. " Habib ya jinjina kai, zama tai a kan kujera shikuma ta mike yai waje, Aneesa ta dade a zaune tun tana irgaminti har ta dawo hour, ganin hour din Ashraf biyu a ciki gashi har bacci yana neman d'aukan ta yasa ta mike kamar ta kurma ihu. Abin haushi taje tana kwankwasa kofar Ashraf sai ga Habib ya shigo, yana ganinta baisan sanda dariya ta zo mai ba. Aneesa takalleshi cikin kuluwa tace " Abokin Ango meye hakan? " Habib ya had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri yace " Tuba nake Amarya amma naga kamar fada kukai da Angon." Aneesa wani takaici ya kara kamata ta kalli kofar Ashraf sannan ta kalli Habib dake juya kai yana d'an dariya haushi yakamata kawai ta tsugunna a gun tasa kukan shagwab'a. Kuka take sosai Habib ganin haka ya kara komawa waje. Ashraf kam wanda kukan duk ya dameshi ya mike jiki a sanyaye ya bud'e kofar, Aneesa tana jin ya bud'e ta kara sautin kuka. Ashraf ya tako a hankali, ya tsugunna shima tare da sa hannu akan kafad'arta, kamar jira take dama ya tab'a ta kawai ta kankameshi tana kuka, Ashraf ya shiga kokarin zare jikinsa amma ta kankameshi tamau sai kuka take. Ganin bata da niyyar sakinshi yasa ya mike da karfi, Aneesa ta d'ago fuskarta wacce duk ta b'aci kaca kaca sakamakon kwalliyar datasha, Ashraf ya dafata yace " Anie na fada miki ba sau d'aya ba kidaina kankameni haka." Ta turo baki tace " kai fa mijinane. " Ashraf yace " banzama ba tukunna, sai an d'aura mana tukunna, sau nawa ina sanar dake hakan? " Aneesa ta kara share hawaye tace " Yaya naji to zan daina amma d'an Allah kadaina wahalar da zuciyata. " Mikewa yai batare da ya amsa ba ya bud'e kofar d'akinsa yace " zo ki wanke fuskarki. " Ta turo baki tace " bakasan kwalliyar? " Kai ya girgiza alamar a'a yace " ki shiga kya gani " Ta mike zuciya ba dadi tai toilet. Tana shiga taga fuskarta a madubi kamar dodo, da sauri ta matso liquid soap ta shiga wanke wa tana yi tanajin haushin ganinta a haka da Ashraf yai. ¤¤¤¤¤¤ Da yamma bayan little ta dawo Mumy ta sasu a mota suka fita shopping, sunyi siyayyar kayan abincinta sannan aka sai uniforms, da house wear sannan suka wuce gun mai d'inki, nan suka bashi sannan suka amshi ragowar sababbin d'inkunenta, wannan kuma akan gobe za'a mata tunda uniform ne bawai style za ai ba. Nafi kam kana kallanta zakasan tana cikin farin ciki dan little ma sai tsokanarta takeyi. Sun gama komai kafin su nufi hanyar gida, Little ta kalli Nafi tace " Nafi kinsan Ice cream?" Kallan mumy tai wacce tai kamar batajinsu sannan ta kalli Little ta girgiza mata kai alamar a'a. Little ta zunguro kusa da Mumy tace " mumy asai mana Ice cream. " Murmushi Mumy tai tace " to. " Nan suka karkata suka gangara 212, Little ta kama hannun Nafi suka shiga ciki, Nafi kam sai sadda kai kasa take, dama Mumy bata bisu ba tana zaune cikin mota sai dai tabi Nafi da kallo wacce ta ke kula da nutsuwarta tunda suka fito. Tana jinta sanda suna siyayya tana tab'a Little akan wai duk kayan na makaranta ne? Ai sunyi yawa ina zata kaisu? Tanaji sai dai Little tai dariya tace "ke dai me ya dameki? " Mumy ta saki fuska tabi bayansu da kallo. Sukam suna shiga Little ta shiga zab'an abubuwan da zasu siya da yake duk sunayen da turanci take fada yasa Nafi kawai ta zura mata ido tanaji inama itama tasan ke ake cewa? Sunyi siyayya sosai kafin su fito, Nafi ta kalli Little tace " ku kam wani irin kud'i gareku? Na ga sam bakwajin wahalar kashesu. " Little ta d'an harareta tace " Ke dai in an miki abu kawai kiyi godiya ki daina cewa ya miki yawa. " Nafi bata amsa ba sai dai ta bita da kallo, nan suka koma mota. Mumy ta ja mota suka tafi, sun isa gida mumy tai parking zasu fito Nafi tace " Mumy angode Allah ubangiji ya kara bud'i." Murmushi Mumy tai sannan ta amsa da Amin. Zasu fita sai ga Habib da sauri ya karaso, shiya rike musu kofar motar, Little kam wani shaukin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta tace " Ya Habib? " Yakwantar da kansa a jikin kofar kad'an yace " My Little Princess i really miss u" Little wacce zuciyarta ta kara yin haske ta juya fuska cikin shagwab'a tace " bayan yaya ya daina damuwa dani? " Habib ya kalli Nafi ba tare daya ba Little amsa ba yace " Nafisa ba magana? " Ina wuni ta fad'a cikin sanyin muryarta, Ya amsa tare da kallan cikin motar yace " Mumy sannu. " Mumy ta fito tare da cilamai makulli tace " akwai kaya a boot ka tayasu kwasa zuwa b'angarensu. " Ya chafe tare da yi mata salute yace " yes maa. " Mumy tai gaba, Little ya kalla yace " Little Princess ba a huce bane? " Tace " Yaya Allah kuwa..... " Ya katseta tare da had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri, hakan yasa ta kasa karasawa, itakam Nafi dama tad'an matsa nesa da su kad'an, jitai Habib yace " To gimbiya sai ki matso mu kwashi kayanki ko? " Da mamaki ta juyo tace " Ba dai nice Gimbiyar ba ko? " Habib yai dariya yace " me? Bakyasan sunan? " Zatai magana Little tace " Ni Princess ita Gimbiya? Ya Habib to meye marabarsu? " Ya saki dariya yace " Princess ba dai tana kishi ba? " Da sauri tace " ni dai bance ba. " Nafi itakam ta karaso ta d'au ledoji manya manya ta nufi hanyar ciki, Habib da sauri ya sha gabanta yace " ta ina mace yarinya kamarki zata iya d'aukan kayan nan? " Nafi ta kalleshi tace " zan iya, kai dai kaba Maryam hakuri. " Ya kalli Little sannan ya juyo da niyyar yima Nafi magana sai dai can ya ganta tayi gaba, ya saki murmushi tare da shafar keyarsa sannan ya koma gun Little. A falo Nafi ta tadda Aneesa da kawarta a zaune suna hira, Nafi ta tsugunna ta gaidasu sannan ta nufi hanyar d'akinsu, Aneesa ganin manyan ledoji yasa tace " ke zo nan." Nafi ta juyo ta kalleta sai dai bata karasa ba, Aneesa tace " ke munafuka ba dake nake ba? " Nafi ta ajiye kayan a bakin kofa ta nufi gunta, cikin masifa Aneesa tace " da ke da kayan nakesan ganinki. " Nafi ta koma ta d'auko kayan ta karasa gunta, gyara zamanta tai sannan ta fizgi Ledar da karfinta ta shiga bincikewa, Nafi kam yau ta kulu, har ranta sai dataji haushin wannan abun, tana kallon Aneesa ta juye ledar ma gaba d'aya akan carpet dai dai nan Little ta shigo falon, mamaki ne ya kamata tace "me kenan? " Habib ya karaso shima ya kalli wannam cin mutuncin, ga Nafi a gefe ta tsugunna, Aneesa ta bugama Little harara idanta ya rufe ko Habib bata gani ba tace

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115