Chapter 95
Chapter 95
nayi nisa da fara tafiya, Isma'il ya turomin da hotunan ku gidana wanda Ruma ta kirani cikin gaggawa sai dai lokaci ya riga ya kuremin, ko ince dama can kwanana ya kare._ _Ban taba tunanin tsanar da kakemin zatakai ga hallakani ba, na maka komai na rayuwa, na kuma nemi 'yarka da ta zama matar d'ana, sai dai a wannan lokacin na janye zancen auren Anisa da Ashraf, banaso d'ana ya fiskanci kiyayya da wahalar danasha a gunku, ya rayuwarsa zata kasance inhar yaji Mahaifin matarsa shine yai sanadiyar nasa mahaifin?_ _Muktar nayi iya bakin kokarina wajen farantamaka da janka a jiki duk da nasan tsananin kiyayyar da kakemin akan Ruma da dukiyata sai dai ina rokonka kar wannan kiyayar ta koma kan d'ana, na yafe maka duk abinda kamin, amma bazan taba yafemaka ba in har ka cutar da Ashraf._ *Daga D'an uwanka Abbas* Da sauri Ashraf ya saki takardar yana girgiza kai cikin tsananin firgice, lalai Kawu mutum ne wanda dole aji tsoronsa, kasa ya sauka jikinsa sai rawa yake ya jingina da bango tare da hade kafafunsa yana girgiza kai kenan Kawu shine yasa aka kama kayan su Dady dan yasan halin Abbansa bazai taba taimakon su ba akan harkar miyagun aiyuka ba. Kansa ya cusa cikin cinyoyinsa a hankali hawaye ya fara zubo mai, wayarsa ce take ta kara sai dai sam ya kasa ko da mikewa, yanaji wayar har ta gaji ta katse. Ya dade a wannan yanayi kafin ya daure ya d'au wayarsa da taketa faman kara, Dan litti ne da kyar ya daga batare da yace komai ba. Dan litti yace " Oga Auwal Max ne a hoton nan." Kai ya daga kawai dama jikinsa ya gama bashi nan ya katse wayar tare da yin shiru, ya akai hotunan da aka ba mumy suka kare a hannun kawu? Da sauri ya mike ya zari makulli yai waje cikin tsananin rudani. Bangaren Mumy ya nufa zuciyarsa na masa wani irin radadi, banko kofa yai da karfin tsiya wanda ita kuma tana zaune rike da karamin hoto, tana jin yanda aka banko kofar ta mike da sauri hoton ya fadi kasa, kallan hoton yai ganin Abbansa ne a jiki. Wata irin dariyar takaici ya saki ya matso kusa da ita ya tsugunna ya dau hoton ya kalleta cikin tsananin takaici yace " me kikeyi da wannan?" Kallansa take cikin wani yanayi, ganin yanda ya rikid'e gaba daya, tace " Ashraf." Kallanta yai idanunsa sunyi jaa sosai yace " me kikeyi da hoton mahaifina? Bayan da ke aka hada baki akai komai?" Kallansa tai tace " Ashraf wai meke damunka ne kwanan nan da baka iya boye emotion din ka?" Ha ha ha ha! Yai tafi da hannunsa yace " Emotion? Kamar yanda kikeyi? Ku halaka min uba sannan ki wani dauki hotonsa kina kallo?" Idanu ta runtse cikin wani yanayi, wayarsa ya bud'e ya shiga nuna mata hotunan nan, yace " hoton nan ke Isma'il yaba shaidar shirin da Dady da kawu sukeyi na halaka mahaifina, tambaya ta anan shine tayaya akai hotunan nan suka isa gun Kawu?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana sai hawaye kawai takeyi, Ashraf yace " Good! Dama nasan bakida amsa, sai dai Mumy dukanku sai kun amshi laifinku a gaban hukuma an muku hukunci." Yana kai nan ya juya zai fita, haryaje bakin kofa yaji tace " Kana tunanin duk a san raina nake komai?" Tsayawa yai cak ba tare da ya juyo ba, tana kallan bayansa ga hawaye na zuba sosai a idanunta tace " me kake tunani? Banasan Mahaifinka? Ashraf na auri mahaifinka ne saboda soyayya ba dan komai ba." Juyowa yai yace " a'a kin aureshi ne saboda kudin sa." Cikin zafi tace"lokacin dana auri Abbas kana tunanin yanada kudi? Mahaifina shine ya neman masa aiki har ya zama abinda ya zama." Ashraf ya kalleta baice komai ba. Mumy ta zauna jabbas akan kujera ta share hawayenta tace " Zauna." Jikinsa a sanyaye ya zauna yana kallanta. Mumy ta kara share kwallarta sannan tace " Muktar bakasan wanene shi ba haryanzu, mutum ne wanda inyace yanasan kaza to fa sai ya sameshi ko da kuwa ta wani hali ne, bayan aurena da mahaifinka har Allah ya azirtashi ya gina wannan gidan baisan Muktar na sona ba, ni kaina sai bayan mun zauna tare sannan nai dana sani sosai dana amince da wannan hadin gidan. Muktar haka zai zo bangarena ya dade duk yanda naso ya tafi bazai tafi ba, anan zaici abinci ni kuma sai dai in shige d'aki. Danama Abbas magana sai yace kar in damu ba komai. Tsoro na ya fara yawa ne daga sanda Muktar ya shigomin d'aki ina bacci ya zauna kusa dani, idona a rufe na dauka Abbas ne inaji yana ta shafamin kai ina murmushi, sai dai daga sanda na bude ido na ganshi na mike da sauri na sa hijab na fara mai masifa. Abinda ya tsoratani shima cikin masifa ya matso ya turani jikin bango gaba daya idanunsa sun canza kamar bashi ba yace " Ruma kinsan tun yaushe nake dakon kaunarki? Banaji duk duniya akwai wanda ya isa ya rabani dake, wlh kinji na rantse miki sai na mallakeki ko ta wani hali ne." Ya sakeni yai waje a fusace. Tun daga wannan rana na fara rufe bangarena sai kuma awannan lokacin Abbas yasan komai sai dai bai taba kawowa Muktar zaiyi tunanin mun wani abuba." Mumy taja wani numfashi tacigaba, a sanda suka hada plan din halaka mahaifinka matar Dady taji komai, sanda aka kawomin hoto ina kokarin kiran Abbas matar ya hisham ta kirani nan ta sanar dani komai. Cikin rikicewa na kira Abbas na sanar dashi sai dai alokacin yana mota, bayan yayi hatsari ne ya sanar dani inyi a hankali da muktar lalai zai iya yimaka illa." Ashraf jin Mumy tayi shiru yasa yace " naji na kuma fahimta sai dai tambayata anan shine ta yaya hotunan nan suka je gun Kawu?" Tace "Dauka yai da ina asibiti." Ashraf yace " menene dalilin dayasa kafin Abba ya rasu ya bar zama dake kullum sai dai ya zauna dani?" Kallan Ashraf tai cikin wani yanayi tace " Ashraf wlh sharri akamin, Muktar ne ya d'aukoni daga gidan Ya hisham sai yace yanada abinda zai kai Tahir Guest palace shine muka shiga, ni a mota ma na tsaya ya shiga ya fito amma bansan ya akai ba wani ya dau hoto ya turama Abbas, tundaga lokacin naga ya daina shiga harkata sam nikuma ban kawo komai a raina ba, sai bayan yayi hatsari ya sanar dani dalili." Kallan rashin aminta Ashraf ya mata sannan ya mike tsaye yace " kinsan yana sanki akan me zaki yarda har ya daukoki? Sannan akan me zaki aureshi bayan kinsan shine ajalin mijinki?" Kuka Mumy tasa sosai tace " Ashraf bazaka taba fahimtata ba, Na auri Muktar ne dan na kareka, na auri Muktar ne dan na kare yayana na auri Muktar ne dan kare dukiyar da mahaifinka ya tara da guminsa." Ba tare da ya zauna ba ya mata kallan mamaki. Mumy kuka take sosai tace " Muktar shi yaba Ya hisham shawarar a halaka Abbas sai dai ya Hisham shine ya sanar da Driver din Abbas,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115