Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Zuciya Kowa Da Irin Tasa Book One Complete Hausa Novels 1,155 words 0 views Progress saved
Download Book

hannunta. D'aki ta shiga ga mamakinta Datti ta gani zaune akan tabirma wanda rabon da ko dakinta ya leka yaga a wani hali take ciki ita kanta ta manta. Shiga tai kanta a kasa, ta gaidashi sannan ta zauna kusa da Maman Hanne. Datti ya kallesu yace " To aure dai an daura sai dai an samu canji daga Ali zuwa wani Ashaf." Cikin tsananin mamaki Nafi ta d'ago ta kalli Baffa tace " Ashaf?" Datti ya jinjina kai yace " Kwarai nikaina nafisanshi akan Ali da alama yana da arziki sannan kuma shi saurayi ne." Maman Hanne ta kalleshi tace " nifa sam ban fahimci me ake nufi ba, banga ne daga Ali ba an koma Ashaf? Meye ma wani Ashaf? Ni bantaba jin sunan ba." Datti ya buga mata wani kallo yace " meye naki a ciki? ' yata ce ba 'yar uban kowa ba sannan in baki tabajin suna Ashaf ba yau ai kinji." Ya mike rai a bace sannan yace " ke kuma ki shirya yanzun nan dan yace ba agarin nan yake ba zaku wuce yanzu." Kallan mamaki kawai take ma babanta ta sani shi dabobinshi su kadai ne abinda ke gabansa kuma suka dameshi sai dai bata taba tunanin zai ma 'yarsa ta cikinsa haka ba, sai kace wata kaza? Ganin kallan datake mai yasa yace " in tunanin sadakinki kikeyi kima manta dan nima na dauki rabona na satar da uwarki tamin, yana kainan yai waje. Nafi kam kuka ma kasa zuwa mata yai jitai idanunta sun kafe kaf, sai dai rigar dake hannunta kawai ta shiga ninkewa jitake zuciyarya kamar zata tsage, Maman Hanne ta kalleta tace " Nafi ki taimaka ki fadamin abinda ke faruwa dan Allah." Nafi ta kalleta tace " Auntu ko na fada miki menene amfani? Tunda aikin gama ya riga ya gama? " Hanne ta mike cikin takaici tai waje. Nafi kam a zaune kawai take tana jiyo muryar Datti yana cewa suyi sauri. Ashraf kam yana tsaye a waje tunani sun taru sun mai yawa, ina zai sa kansa? Mai zai cewa masoyiyarsa kuma 'yar uwarsa wacce saura wata biyu a daura musu aure? Yasan ta sarai yanda take tsananin so da kishinsa lalai zata iya yin komai inhar taji abinda ya faru, kansa ya dafa wanda yakeji yana sara mai. Karar mashin ne yasa ya kalli hanya, Su D'an litti ya hango nan suka karaso D'an litti ya kalleshi yace " yama kace name d'inka?" "ASHRAF. " D'an litti yai murmushi yace " Gaskiya an cucen da aka samin D'an litti sunan ka yafimin dadi." Ashraf yai musrmushi sannan yace " D'an litti kenan." Datti ne ya fito ya tsaya kusa da Ashraf yace " Ashaf gatannan amma ya za'ayi in anaso aje gunta ina zance? " Ashraf ya kalleshi sannan yace " Kano anan garin nake, sannan ai kasan sunana."yai maganar cikin bacin rai. D'an litti ya tafa mai yace " Haba? Living Kano? I also came to kano." Ashraf ya furzar da iskar takaici yace " nikam D'an litti kadingamin hausa banasan turancin nan." Dariya Datti yai yace " gaskiya kam, yanzu kenan in wasu zasuje sai D'an litti ka rakasu ko?" D'an litti yai murmushi tare da sosa keya. Nafice ta fito sanye da lulub'i Hanne da mamanta na gefenta, Hanne ce ta kalli mazan gun su uku, tace waye mijin a ciki? Ta fada tana fatan Allah yasa ba wannan bane dan ya birgeta Allah yasa D'an litti ne." Gani tai D'an litti ya nuna wanda yai masifar burgeta da yatsa, dukda rigar kauye ce a jikinsa kana ganinshi kasan daban yake, tadan yi yake tace " to a rike mana 'yar uwarmu dakyau, amma bamu zamu kaita ba?" . Datti yace " bakiji me nace ba aciki ko kuma wani sabon kinibibi ne hakan? Ai nace su biyu zasu tafi ko?" Mamaki ne ya kama maman Hanne tace " su biyu? Dama abinda kake nufi kenan? Taya zamu bari 'yar mu ta tafi daga ita sai shi? " Datti yace " karki damu D'an litti yasan gidan." Tai shiru, Nafi kam hawaye ne ya fara zubo mata itakam tana ganin rayuwa? Wasa wasa kaza ma ta fita matsayi itakam. Jitai ance " Ina rigata? Ko kin barmin wannan?" D'agowa tai cikin tsananin mamaki, idanunsu ne suka hadu........gabanta ne ya shiga fad'uwa sai dai ta kasa dauke ido daga kansa, ya sakar mata wani sansanyan murmushi........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *WELCOME BACK ZEE FRESH,* *WE REALLY MISS YOU*😍😘.. 7⃣ Kallansa take cikin tsananin mamaki ya sake murmushi yace " Riga tafa? Ko kin barmin wannan d'in? " Kasa tai da kanta sannan a hankali tace "na d'auka ka tafi ai. " Datti yace " me kuke nufi kenan ka santa dama? Sani bana taimako ba? " Ashraf yad'an yi murmushi dama so yake ya kular da Datti yace " sani kuwa tunda ji jiya a d'akin ta na kwana. " Yai maganar yana kallan Nafi, gaba d'aya kowa ya kalleshi, Datti ya rike haba yace " Kwana? " Ashraf yai wani murmushin rainin hankali sannan ya ya d'aga kai yace " Uhm hum" Hannee da mamanta suka kalli Nafi cikin mamaki, Dan litti shima mamaki ne taf a ransa lalai wannan gayen ashe dan duniya ne? Nafi ce tayi baya da sauri tai cikin gida, kallan kofar data shiga sukai suna tunanin me kuma zatai. Nafi kam tana shiga da sauri tai d'aki tana tafe tana murmushi takasa gane dalilin murmushin nata, rigarsa data ninke d'azu ta dauka abin haushi ba tada turare hakan yasa ta fito, suna tsaye sai gata ta dawo. Datti yai tsaye yace "Gungumar Munafuka ina kika je? " Rigarsa ta mikamai fuskarta a sake tace " danaji bakai min magana ba sai na d'auka tafiyarka kayi. " Ashraf ya amsa yace" ina kuwa zan tafi? Bayan nasan kina cikin wani hali? " Salati Datti yasa yace " yau na shiga uku lalai yarinyarnan ke ba karamar 'yar iska bace, a haka kowa ya ganki sai ya d'auka ke ta Allah ce ba'asan tsantsar munafircin ki yafi na shaid'an ba, yanzu dan iskanci da so kikai ki auri Ali bayan kin gama lalata da wannan? " Cikin mamakin kalamansa Nafi ta dago ta kalleshi, lalata? Me kenan? Maman Hanne ma tace " Gaskiya Nafi kin ban mamaki ban taba tunanin zaki aikata haka ba. " Itakam Hanne harara kawai take makama Nafi. Ashraf ne ya kallesu yace " Gaskiya bakuda adalci, wato kai kana mahaifinta sanda nace ta taimakeni baka shi mata albarka ba ka yabe ta ba, sai yanzu dana fad'i na kwana a d'akin ta kaf cikinku ba wanda yai tunanin lalai kila ba abin banza akai ba. " Ya d'an furzar da iska sannan ya matsa daga inda suke, ta baya ya zaga ya cire rigar jikin sa yasa tashi, tunda ya juyo ya fara tahowa kowa ya kuramai ido, lalai wannan gayen bana karya bane, tafiya yake cikin isa Nafi itama ba'a barta a baya ba gun kallansa, Hanne kam kishi duk ya isheta. Ashraf har ya karaso basu daina kallanshi ba, D'an litti ya dafa yace " Babban gaye me kake tunani ne?

Table of Contents

Chapters

115 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115