Chapter 25
Chapter 25
" D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu, gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........ *THE INNOCENT TEAM* [5/9, 09:58] Ayusher✍🏻: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Dedicated This Page to World of Hausa Novel 1* And *Taskar Lubie Mai Tafsir* 2⃣1⃣ A tsorace Nafi ta mike gabanta sai fad'uwa yake, shikam gogan ko mikewa baiyi ba sai cewa dayai "Little mikomin rigata a kan gado. " Nafi ta mikomai sannan ta fito daga d'akin da sauri tare da ja mai kofar, dan ta kula kamar bayasan asan bashida lafiya. Tana fita falo Asim ya karaso tare da jan hannunta da karfin tsiya, Nafi ta d'an turje sai hawaye da takeyi. Asim ya haska mata wani wawan mari yace " banza karuwa, a ido kamar bakauyiya ashe kinfi karuwai iya iskanci. " Nafi ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata. Kofa aka bud'e, mamaki ne ya kama Ashraf ganin Nafi, sai dai bai bari mamakin ya fito fili ba cikin isa ya karaso ya sa hannu ya rike hannun da Asim ya rike. Asim ne ya kalleshi cikin masifa yace " Me kenan? Kazo karema karuwarka ne? " Nafi kam kanta na kasa, kunyar Ashraf duk ta gama rufeta ta sani sarai bai san ita bace sai yanzu. Ashraf ya kalli Asim yace " Saketa ko? " Nafi kam hannunta sai zugi yake yi, Asim yace " bazan saketa ba sai munje gaban kawu ta sanar mai abinda kai da ita kuke aikatawa. " Ashraf yai wani murmushi ya kalli agogo karfe 6 na yamma, sannan ya kalli Asim yace " ai banaji sai ta bika wajen isar da sakon kai kad'ai ma ya wadatar kaje ka sanar. " Asim ya kara cika baki da takaici yace " Me kake nufi? " Ashraf ya kalli Asim ya mai alama da ya sakar mata hannu, cikin takaici Asim ya saketa, Ashraf ya kalleta yace " wuce ko? " Nafi ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla tanasan bashi hakuri sai dai bataga fuska ba, da kai ya mata alama ta wuce mana, jiki a sanyaye tai gaba tana yi tana waigensa. Tana fita Ashraf ya kalli Asim yace " D'an sako mai kake jira? " "d'an sako? Nine d'an sakon? " Ashraf yai wani murmushi yace " Au na d'auka danace kaje ka sanar ai zaka wuce da sauri ka gurfana agaban kawu ka sanar mai. " A zuciye Asim ya kama wuyan Ashraf cikin masifa yace " Ni kake fada ma haka? " Ashraf yad'an juya ido kad'an yace " inmu uku ne to dana ukun nake." Ya ja jikinsa ya koma d'aki dan yin alwala. Asim ya naushi iska cikin tsananin takaici yai waje jiyake kamar ya lumama Ashraf wuka hankalinsa ya kwanta. Ashraf kam alwala yai sannan ya fito waje. Nafi kam d'aki tai tana kuka, Little ta gani ta fito daga wanka, da sauri Little ta karaso tace " Nafi menene? Wani abin ya miki? Laifi kikama yayan? " Kai kawai Nafi take girgizawa, Little tace " to menene?" Nafi ta kalleta tace" me karuwa yake nufi dan Allah? " Little da mamaki ta kalleta tace " Yayan ne ya fada miki hakan? " Kai ta girgiza alamar a'a sannan tai hanyar ban d'aki da sauri, da alama kalmar bata da dad'i ganin yanda fuskar Little ta canza. Little ta bita da kallo, sannan ta d'au always d'in da Mumy ta kawo mata ta sa, zama tai jiki a sanyaye, waye yacema Nafi karuwa? Asim kam ana idar da sallah ya tari kawu acikin masallacin ma ya fad'amai, ran kawu yayi dubu gurin b'aci, ganin haka yasa Asim ya saki wani murmushin mugunta. Kawu ya fito cikin tsananin masifa nan yace Ashraf ya biyoshi, duk da kasan zuciyarsa yaji ba dadi sai dai bai nuna ba, nan Asim yabi bayan kawu. A falo Mumy, Umma, Asim da Ashraf ne a zaune sai kawu. Cikin fada kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf meke faruwa? Wani banzan labari nake ji haka? " Ashraf ya kallesu kaf sai dai kafin yai magana Aneesa ta shigo cikin tsananin kishi ta karaso kusa da Ashraf tace " Yaya me kenan? Ni zakaci amana? " Mumy wacce jikinta duk ya mutu dan ta taba ganinta ta fito daga d'akin, tai shiru yau kam batada halin kare Ashraf. Kawu ya daka mata tsawa yace " Aneesa bakida hankali ne? " Ta kalli kawu cikin tsananin takaici tace " Amma Abba..... " Hannu ya d'aga mata hakan yasa Umma ta zaunar da ita a kusa da ita. Ashraf wanda ke zaune sai dai duk masifar mutum bazai tab'a gane meke yawo a ransa ba, sam babu b'acin rai ko farin ciki a tattare dashi. Kawu yace " Asim fad'i me ka gani. " Hankalin Asim a kwance ya sanar da abinda ya gani har da karin cewa wai suna ganinshi suka tura kofar d'akin suka rufe, sai daya dade kafin su fito. Mumy ta runtse ido zuciyarta na wani irin zafi, Umma ta shiga tafa hannu tana salati, itakam Aneesa kafe Ashraf kawai tai da ido jitake kamar zata mutu dan tsananin kishi. Kawu ya kalli Ashraf rai a b'ace yace " Wani irin iskanci ne hakan Ashraf? " Ashraf ya mike daga zaunan da yake ya kallesu ga mamakinsu Murmushi sukaga ya saki, ya jinjina kai sannan yace" tunda maganar Asim itace gaskiya banaji inada abin cewa. " Yana kai nan ya nemi hanyar fita, Umma cikin kuluwa tace "lalai kuwa Alhaji yarinyar nan dole ne ta bar gidan nan, inshi ba'a isa dashi ba ai ita kam karya take. " Ashraf ya juyo ya kalleta sannan ya kalli Aneesa da ta ke zaune kamar gunki ya bud'e baki zaiyi magana yaji Mumy tace " Gaskiya nima Alhaji yarinyar nan bata kwanta min ba." Fuskar Ashraf ce ta canza, yanzu kam ransa ya b'aci sosai, bai damu inkowa ya mai abu ba amma ya tsani yaga mahaifiyarsa na goyon bayan masu mai abu. Kawu ya kalli Asim yace "Ai ba sai anja da tsauri ba, yanzu nan za'a kirata tabar gidan nan. " Ashraf ya had'iyi wani abu sannan ya d'auke idansa daga kan Mumy ya maidashi kan kawu, ya kalli Kawu yace " Kawu banasan abu yaji da zafi sai dai in aka kaini bango banajin kowa zaiji da dadi a gidan nan. " Yana kai nan yai waje, Mumy ta dafa kanta, tanaji Umma na cewa " Allah wadaran nakaa ya lalace, sam yaran nan yafi karfin kowa a gidan nan? " Kawu yai shiru shikansa ya kasa magana. Ashraf kam yana fita ya kira number Habib, bugu biyu Habib ya d'aga yace " Buddy yau kuma soyayyarce ta tashi? " Ashraf yai tsaki yace " Habib dan Allah makarantar Abbanka wace iri ce? " Da mamaki Habib yace "lalai Ashraf kana nufin bakama san me Abbana yake ba? " Ashraf yace " Malam dole ne sai na sani? Ba gashi ina tambayarka baa yanzu? " Habib wanda baiji dadin kalaman Ashraf ba yace " Primaryce da secondary." Ashraf yace " day ce ko boarding?" Day ce mana. Ashraf yad'an shafi kansa sannan yace "
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115