Chapter 108
Chapter 108
da Ashraf?" Kanta ta girgiza alamar a'a tace " ni ai ko waya bamuyi ba tunda muka taho." Mamaki ya kama mumy tace " akan me?" Nafi tace " wlh bakomai, kawai dai nasan yanada al'amuran dake gabansa ne dayawa." Mumy tai shiru, jikinta yai sanyi ba shakka kam yanada su dayawa. Nafi ta kalleta tace " Mumy karmu fadamai harsai ya gama." Kai Mumy ta daga alamar amincewa. ************ Ashraf na zaune gidan Uncle Salim dashi dasu Auwal Max. Ashraf ya kalli Auwal yace " kayi hakuri kaga haryanzu bamu maidakai ba." Auwal ya girgiza kai yace " ba komai, acan din ma me nakeyi banda wahala, matata ta rabu dani ko ince tunda taga banida komai ta fitineni sai dana bata takardarta, 'ya'yan da muke dasu guda biyu ta kwashesu, ni ba sana'ar arziki ba sai dai inyi can inyi can." Ashraf ya kalleshi cikin tausayawa, Auwal yai murmushi yace " na sani alhakin Abbas ne ke bina, mai gida ya kula dani sosai amma naci amanarsa." Ashraf ya mike jin idanunsa na rawa ba shakka an zalunci mahaifinsa dayawa, shiyasa akullum in ya tuna akwai ranar hisabi sai yaji zuciyarsa tayi wani dadi. Sako ne yashigo wayarsa daga Little. Cikin mamaki ya bude _Yaya dan Allah kazo gidan gona na Mumy dake bayan gari akwai matsala._ Abinda aka rubuta kenan a sakon, shiru yai yana kara kallan sakon. Kb ya kalleshi yace " ya akai?" Ashraf ya mika masu wayar, sannan yace Auwal ya shiga ciki. Kb ya karanta yaba Salim shima ya karanta, Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje." Uncle salim ya kalleshi yace " anya Ashraf baka tunanin da matsala kuwa?" Ashraf yai murmushi ya kalli Dan Litti yace " Mutumin muje?" Dan Litti ya mike, Kb ne ya dafa Ashraf yace " Ashraf." Ashraf yai murmushi yace " karka damu, kawai dai nan da 20mins ka kira 'yan sanda kuzo gurin." Kb ya kalleshi cikin kulawa, Ashraf ya kalleshi sannan ya kalli Uncle yace " cikin abu biyu akwai d'aya, ko dai da gaske wani abun ne ya samu Little kaga kuwa in naki zuwa ko me ya sameta daga baya bazan iya yafema kaina ba, ko kuma trap ne Kawu ya shirya min." Salim yai shiru tabbas ya gamsu da bayanin Ashraf, ya mike yace to muje tare. Ashraf ya girgiza kai yace " A'a Uncle karka damu ba abinda zai faru." Sun fito dashi da Dan litti suka shiga mota sukai gaba. A hanya ya turama Little sako akan gashinan zuwa. Sun isa can waje gari inda gidan gonar Mumy yake, da sauri ya fito ya shiga ciki. Yana shiga cikin gun yaji daga baya ta waje an datseshi. Tsayawa yai cak ya kurama kofar kallo. Sannan ya kalli cikin gun, ba komai agun, kajin ma babu ga kajinan nan wayam. Dan Litti daya taho yazo yin kwana yaji an kwadamai wani katako. Nan ya fadi kasa a sume. Ashraf kam da sauri ya koma bakin kofar ya fara jijiga. Wayarsa ce tai kara, nan ya zarota. Ganin number Little yasa ya daga da sauri. Jiyai an sheke da dariya, da sauri ya danna record a jikin wayar sannan yace " Kawu ina Little?" Kawu ya sake dariya yace " kai da Little sai dai ranar tashin kiyama, dan kuwa kai daga nan sai kabarinka." Ashraf cikin mamaki yace " me kake shirin yi?" Kawu ya sake dariya yace " me? Are u scared?" Ashraf yai shiru. Kawu yace " Kasan dai Maryam 'ya tace, 'yata kuma wacce na haifa da Ruma, kana tunanin zan iya halakata ne? Na dauka u are smart ashe kaima kan baya jaaa." Ashraf cikin fada yace " me kake tunanin yi?" Kawu yasa dariya yace " kanada sako gun tsohuwarka ne?" Ji yai alamar kauri hakan yasa ya jujuya mai zai gani? Wuta ne ya fara ci ta waje. Kawu yace " ina jiranka." Ashraf yace " ka kashe mahaifina yanzu ni zaka kashe? Sannan kacigaba da zama da mahaifiyata?" Kawu yai murmushi yace " it's unfair ko? To amma ya zakai, wannan itace kaddararka Abbas na kasheshi ne saboda ya kwace komai da nakeso a rayuwa, kai kuma zan kasheka ne saboda kana neman rabani da abinda ya zama mallakina." Ashraf zai sake magana kawu yace " kaje kai lokacinka yayi mu ba yanzu ba." Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya ya karayi sannan ya fito daga bangarensa ya goge last call din dayai ya kaima little yace " Little wayar Nafin ma shiru, na kasa samunsu duka." Little tace " insun kira zan kawoma Abba." Yace "yauwa my Little sannan yai gaba." *********** Ashraf kam suna gama waya da kawo ya kalli wayarsa sannan yai wani murmushi tare da kiran Kb, yace "kuyi sauri." Nan kb ya amsa da to. Ashraf nan ya shiga tuno abinda ya faru. A safiyar yau ne ya samu Little da kansa har bangarensu. Ya kalleta yace " duk sanda Kawu yace ki bashi wayarki karkiyi musu ki mikamai sannan karki tambayeshi me zaiyi dashi." Ta amsa da to. Sannan ya fito ya tafi shida Dan litti sukai gidab Salim. A hanya ya kallu Dan Litti yace " mutumin nasan baka da tsoro sai dai abinda nake shirin yi har lafiyarmu zai taba." Dan Litti yace " karka damu yallabai ai komenene indai har bai sabawa shari'a ba to bazan taba yima musu bama bare inkiyi." Bayan sunga wannan sakon Ashraf ya mai murmushi kafin ya mikamai, dama Kb ya san komai. Murmushi ya sakeyi yace " abinda nakeso kayi ka taimaken kayi cikin gaggawa Alhaji Mansir, dama burina shine kayi nufin kasheni wanda hakan zai kaimu gun 'yan sanda daga nan kuma komai zai fara fitowa dala dala." Zafin wutar ne ya fara damunsa gashi har ya fara shigowa ciki. Tari ya shiga yi dan hayaki sai shigamai hanci yakeyi duk ya dameshi. Tari yake sosai wanda hakan ya kaishi ga suma. Dakyar su Kb suka iya b'alla kofa, nan suka ciroshi akai asibiti dashi. 'yan kwana kwana dama suka kira. Dan Litti kam ana samai ruwa a hanya ya farka, sai dai gefen kansa sai jini yake yi. Sun isa asibiti da sauri akai emergency dasu. Dan litti aka mai dinki shi kuma Ashraf har drip aka samai. Nan Kb ya kira shugabansu na gun aiki ya sanar dashi ga report nan ankawo musu anyi anyi attempting din kashe wani. Nan shugaban yace "yanzu zai turo Team dinsa su dau case din." *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *85* Bayan Ashraf ya farfado 'yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kanwarsa tamai ya kuma nuna musu sakon. Nan suka bukaci anuna musu kanwar. Ya sanar dasu tana gida. Kb ya jasu suka nufi gidan. ******** A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa 'yan sanda sunzo hankalinsa yai kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi. 'yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little. Ba'a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa 'yan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115