Chapter 17
Chapter 17
"bari na kaimai. " Goggo ta kalleta tace " kinsan b'angarensa ne? " Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani. Nan Goggo ta bata. Fitowa tai tana ta kalle kalle, nan Allah ya had'ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace "Amra inane b'angaren Yaya? " Nan Amrah ta nuna mata, karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan. Knocking tai a hankali, Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace "in abinci ne ajiye zan d'auka." Nafi ta kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa. Shikam ya dade kafin ya taso ya bud'e kofar, mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace "lafiya? " Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi, kallan mamaki ya mata yace " kece? " Kai ta d'aga kawai, yace " D'auko abincin ki shigo. " D'auka tai sannan tabi bayansa, tana shiga ta tsaya a bakin kofar, ya karasa kan kujera yace " turamin kofar. " Rufe kofar tai sannan ta kalleshi, da hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning, nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta, ya kwanta ba tare da yace mata komai ba, itama shiru tai dan batasan me zatace ba. Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana, sun dade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi. Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa, a hankali ta d'an matso kad'an cikin in ina tace "dama d'azu ne.... " Sai kuma tai shiru, Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace "naji kace zan ma abu? " Nan ma shiru, lekashi tai kad'an, gani tai bacci yake, a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido, a ranta tace "na sashi yai bacci baici abinci ba. " Kallansa ta karayi, itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takesan taga tana kallanshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣4⃣ Sai yamma Little ta dawo, abinci kawai taci suka shiga bubud'a kaya nan Little ta ware mayafai da jaka suka had'a kayan da za'a kai d'inki. Nafi sai murna take a ranta zataga cikin gari. Driver d'in mumy ne ya d'aukesu, a hanya Nafi sai kalle kalle take can ta tuno tahowarsu a mota itada Ashraf murmushi ta saki wanda Little ta kula dashi. Little ta d'an harareta tace "Nafi na kula yau dai a farin ciki kikeyi." Murmushi ta sake sannan ta kalli Little tace "Little dan Allah tambaya. " Inaji kawai little tace sai dai ta maida hankalinta kan Nafi, Nafi tai kasa dakai cikin alamun kunya tace " in mutum yace yanaso kamai wani abu, me zai kasance? " Dariya sosai Little tai ta dade kafin ta tsagaita tace "Hala Ya Ashraf ne ya fad'a? " Nafi ta d'an turo baki kadan tace "shine to menene kike dariya ?" Little tai d'an karamin tsaki tace "in kikaji yaya ya fad'i haka wallahi aiki yakesan saki. " Nafi ta kalleta tace "aiki shine yanasan inmai wani abu? " Little ta girgiza kai tace "Tab bakisan mutumin nan ba, amma duk da haka nayi mamaki dan ni kad'ai yake sawa aiki ni kuma ba abinda na tsana a rayuwa irin inji yaya yace zan mai wani abu. " Nafi ta d'an jujuya kai sannan tace " Meye abin tsana? Nikam dadi zanji inya sani aiki ma. " Little ta mata wani kallo na yarinya da sauranki tace "Nafi bakisan waye Ya Ashraf ba, duk aikin da zakimai bazai tab'a burgeshi ba sannan bazai tab'a cemiki ko sannu ba. " Nafi ta d'an tabe baki tace " to mezai sa sai yayi miki sannu bayan ke kanwarsa ce? " Kallan mamaki Little take ma Nafi itakam Nafi ina ta sani cigaba tai da cewa " Sanna? N da alama ba a mai aikin yanda yake so ne. " Duka little ta kai mata,Nafi tai saurin sa hannu agun, Little ta rike hab'a tace "Lalai ashe kina magana haka? " Nafi tai murmushi batace komai ba, Little ta kalleta tace "Naji ni kanwarsa ce sannan naji d'in bana mai yanda yakeso, ke tunda kinanan sai ki mai yanda yakeso ki kuka tabbatar yacemiki sannu. " Nafi murmushi kawai tai batace komai ba, Little tace "Kinga da Ya Habib ne? Wayyo Allah na. " Da mamaki Nafi ta kalleta tace "Ya Habib? " Little ta saki wani fara'a yacigaba "D'an yayan mumy ne yanazuwa gida sosai ya dad'e yanzu ma na tabbata kila karshen satin nan ki ganshi. " Nafi ta maida kanta titi kawai, Hannu little tasa ta juyo da ita tace " Nafi kinsan me? " Kai Nafi ta girgiza alamar a'a, Little ta cigaba cikin zakuwa "Ya Habib ko Opposite d'in Ya Ashraf ne. " Nafi da mamaki tace "Oppo? " Little ta dafa goshi tace " Kinsan me? Kinga Ya Ashraf bai da san magana shi kuma ya Habib akwai surutu, sannan Ya Ashraf akwai zafin rai shikuma Ya Habib Saukin kai gareshi. " Nafi ta d'an bata fuska tace "Zafin rai? " Little tace " naji ba zafin rai ba, sannan kinga Ya Habib akwai san wasa da mutane, ga mutunci. " Nafi wanda ta rasa dalilin jin haushi Little datai tace "Little da wa kuka fi kusa? " Cikin rashin kulawa tace "Ya Ashraf. " Nafi tai shiru batace komai ba jitai Little tace "Amma Ya Habib zan aura. " Juyowa tai cikin tsananin mamaki ta kalleta, Little ta harari Nafi ta juya. Nafi kam ta kasa magana sai shiru tai. Tanaji Little ta d'aga waya suna hira da wata kawarta akan Lesson d'in da suke zuwa, saboda shirye shiryen Exam d'in Qualifying da zasuyi, ga makarantarsu anyi hutu kuma suna komawa za'a fara jarabawa. Nafi kam sai kallan sha'awa take mata, har suka isa gun d'inkin. An gwadata sannan suka bada kayan akai sai nan da sati d'aya za'a amshi wasu daga baya sai a zo a amshi sauran. _A gida_ Ashraf ya dad'e yana bacci kafin ya tashi, wanka yai sannan ya ci abinci, ya gama kenan Amra ta shigo tace Mumy na nemansa hakan yasa ya mike yai waje. Yana ganinsu Asim da kannensa a zaune d'auke kai yai kamar bai gansu ba yai gaba, yana wucewa kuwa sukaja tsakin takaici. Sun gaisa da Mumy sannan ya gaida Kawu, shiru ne ya biyo baya kafin kawu yace " Ashraf dama maganar auranka ne da Aneesa. " Kallan Kawu yai sai dai baice komai ba, Kawu ya cigaba "saura wata biyu a d'aura auren shine nakesan jin ra'ayinka akan abubuwa guda biyu." Ganin Ashraf bai da niyyar magana yasa yace " Da farko inda zaku zauna, anan kake so ko kuwa a d'aya daga cikin gidajen mahaifinka zaka duba d'aya? " Ashraf kam tambayar ta d'an b'atamai rai sai dai bai nuna ba kawai cewa yai "A tsarin mahaifina yafisan inzauna anan cikin 'yan uwana. " kawu yai murmushi yace " yauwa haka ake so dams banasan tauyema hakki ne, tambaya ta biyu maganar aiki fa? " Ashraf
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115